Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 13 of 41
Zaune Mujahid yake a office tare da abonkinsa Mubarak, sun dan tattauna issues daya shafin aikin su sannan Mubarak ya gangaro mai da cewa, "wai ya ake cikin da diyar Alhaji Abbas ?
Mujahid kam kaman jiran tambayan yake, ya jima yana son mai zancen Salma amma ya share,
Dariya yayi Yace "yarinyar nan bomb ce, nan ya tsarawa Mubarak duk yadda ake ciki tun farkon haduwan su sannan ya kara da cewa "d worst part of the story itace same Ummi da Hajiya take nema ruwa ajallo"
Ware ido Mubarak yayi in shocked yace "abokina mai kake jira, ai albishir zaka ma Hajiya, komai yazo cikin sauki"
Mugun harara Mujahid ya sakar mai yace "yadda na tsanin yarinyar nan bana fatan ganinta gidanmu, what am curious about shine ya akai ta koma diyar Alhaji Abbas sannan kuma why is she alway acting bitchy, deep down nasan akwai something good about her"
Nisawa Mubarak yayi
"Toh ai ita zaka tambaya bani ba.
Muhajid yace "She isn't stupid da zan tunkareta da tambayoyi ta amsa min"
"Ai dama ba zuwa xakayi kafara jero tambaya ba, make friends with her, you can pretend loving her, kasan mata da rauni daganan saika tatso information da kake son sani"
Dariya sosai Mujahid yayi sannan yace "ajiye love aside, yadda na tsane ta i can't even pretend, abu daya zan iya shine mu zama friends, when am done with her sai nayi destroying dinta for good kaga na rama abunda tamin"
Kallon shi Mubarak yayi aranshi yace "this is serious, i cnt wait naga karshen Drama dinga" Afili yace "Allah ya bada saa, if you need my help kamin magana"
"Bani address din gidansu". Mujahid ya fada.
Ba musu Mubarak ya bashi dan kuwa Gidan Alhaji abbas sanan nene.
Salma ta warware, cikin walwala take, duk wani abun da zai b'ata mata rai kawar dashi tayi, basu da lec sai gobe, kitchen ta wuni tana taya mai aikin su abincin dare, bayan sun gama, ta jere komai a dining sannan ta shiga ta kara wanka ta sanyawa jikinta doguwar rigan kanti, bayan sallah ishai ta nufi Dakin Mom, sun jima suna hira, mai aikinsu Lami ta shigo tace maigadi na magana wai wani na kiran Salma awaje, tsaki Salam tayi tace kice mai bana fitan dare, ba masu Lami ta juwa,
Mom tace "kinma isa, ai tashi zaki kije kiga waye, dama tuni na fara jin kamshin yan jikokina"
Dariya Salma tayi bata da niyyah tashi, ganin mom ta bata rai yasa ta mike, daki ta shiga tasa Hijabi sannan ta fito zuwa waje.
Jingine yake cikin motarsa, agogon hannusa ya duba yaga 8.30 tsaki yayi, maigadi ya fito yace mai Salma bata fitan dare, bai damu ba yasa aranshi gobe zai isketa a school, shiga mota zaiyi yaga wata mota ta danno gurin gate din, tsayawa yayi, Daddy ne a motan tare da Driver, Wining glass yayi yace "yaro aida ka karaso ciki, halan wa kake nema...
Kafin Mujahid yayi magana salma ta fito, gaida Daddy tayi aladabce, tana ganin Mujahid ta juya zata koma ciki, Daddy yace "salma jeki mana, ba gurin ki yazo ba"
Yaken dole tayi ta amsa da toh ta karasa gurin Mujahid shi kuma Daddy ya shiga gidan.
Dan nesa dashi ta tsaye hade da kawar dakai gefe, kallon yayi aransa yana jinjina yadda ta bawa Daddy respect, dan matso wa yayi kusa da ita, murya ciki ciki yace "baza ki gaishe da bakon ki ba"
Yadda takeji tsanan shi bazata iya tanka shi ba, juyawa tayi a fusace xata wuce,
Yace "Ummi".
Wani irin shocked taji, gabanta ne ya fadi, she can't recall wen last data ji Ummi abakin wani. Ganin yadda ta daskare agurin yasa Mujahid shan jinin jikinsa, sam baisan ya furta sunan Ummi ba, wayancewa yayi dacewa "Miemie, momy, ummita kinsan bansan sunan ki ba, dole yasa nahau guessing..."
Ajiyar zuciya ta sauke, saidai taji dadi yadda ya kirata da Ummi, juyowa tayi tace "Sunana Salma"
Yace "nice name" kalan ta yayi tamai kyau sosai.
Hararar sa tayi tace "kaga Malam miye ke tafe dakai, indai 500k dinka kazo amsa toh babu na zubar a titi"
Murmushi yayi.
"Karki damu nina yafe maki, nazo ne muyi sorting difference dinmu"
Shuru Salma tayi tanai mai kallon banxa.
Yacigaba "can we be friends ?
Mugun Dariya rainin wayo Salma ta face dashi, sannan ta daure fuska tace "you're not serious" juyawa tayi ta koma cikin gida, tana gudun dumamai zagi a zuciyanta.
Shima dariya yayi ya koma mota yaja yabar gurin.
Kicibis Salma tayi da Salim bakin gate, da alamun lekan su yake, hannuta ya riko
Fuskar daure yace "Salam ki gayamin gaskia, mike tsakanin ki dashi, jiya da yau sam bangane mai kuke nufi ba"
Fizge hannuta tayi, cikin daga murya tace "mind your business and stop acting like a fool" afusace tayi gaba ta barshi da sakin bakin Fool data kira shi dashi, kwafa yayi ya wuce part dinsa zuciyarsa na kuna...
****
Washe gari, 12 to 2 su Salma ke da lecture din Faiza, da wuri ta shiga skull, mutane sai mata congrats din face of gwagwalada suke, ko kallan su batai ba ta karasa Hall ta zauna, baa jima ba Faiza ta shigo Tafara masu lec, bayan ta gama ne ta sanar dasu test datai masu is cancelled, ihu sosai yan aji suka fara dan kuwa sunsa basu tabuka abun arxiki ba, Salma kam baki ta Tabe ko ajikinta.
Faiza na shirin fita hall din ta kalli Salma tace "ki sameni a office".
Bayan kaman 10 mins Salma ta taka zuwa Department, office din Faiza ta shiga ta iske ta zaune, da alamun zaman jiran Salman take.
Zama Salma tayi kan kujera dake gurin ba tare data jira permission dinta ba.
K'wafa Faiza tayi tace "zan baki A a course dina kuma zan biyaki idan kikayi min alkawarin fita harkan Mujahid"
Mugun Kallo Salma takai mata aranta tace "what an insult, aiko banyi karatu ba ina iya cin B, kudi kuma ai baki dasu"
Afili tace "I assume kin kirani muyi magana woman to woman not lecturer to Student ?
Kad'a kai Faiza tayi tace "duk yadda kike tunani hakane".
Mikewa tsaye Salma tayi tace "y not kibiyani na tursasashi ya soki, tunda naga har yanxu bakya gaban shi kuma shekarun ku na tafiya"
Hannu Faiza ta nuna mata alamun gargadi tace "karki kuskura ki zageni, cox am not your mate"
Dariya Salma tayi.
"Yes ma, amma abunda baki sani ba shine if you keep following him around like a fool, obeying is orders bazai tab'a sonki ba"
Afusace Faiza ta mike tsaye tace "enough, kawai ki fadi abunda kikeso"
"Ni banaso komai, ki rike kudin ki, grade dinki da Mujahid all for youself cox i dont give a fucking dammm about dem" juyawa Salma tayi, Faiza tace karya ne i know you love him".
Salma kam tagama kulewa, kallon ta tayi tace "love huh !!! Ki kalleni dakyau banda lokacin soyayyar shirme, infact the word love doesn't exist in my Dictionary"
Afusace Salma tabar office din hade da banging door.
Rai bace faiza ta zauna tana nazarin abunda Salma tace, kai ta gigirza tace "so take nadaina binsa na nadai obeying abunda yace kenan" tsaki tayi ta kuma cewa "karyan banxa sodai take nafita harka Mujahid danta samu shiga, toh yarinya kinyi kadan" kamar Tababbiya Faiza tahau surutu ita daya a office.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.