Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 35 of 41
Jin ihun Salma yasa Mujahid mikewa akidime ya fito waje, ganinta yayi zaune kasa tana rusa kukan daya jima yanason Ganin hawayanta. Da sauri ya karasa gareta yana fadin "Habibty yaushe kika zo ?
Wani sabon kuka tafashe dashi, jin sabon yaudarar dayake shirin yi mata, mikewa tayi tsaye tana kallon yadda duk ya gigice, rikota yayi cike da kulawa, wani irin feeling yaji ya ratsa jikinsa, ga kamshi jikinta sai ratsa mai gabobin jikinsa yake gabadaya.
Murya kasa kasa yace "sweetheart mi aka mike, plz stop crying, your tears are breaking my heart" janyota yayi zai rungumeta tasa hannu da karfi ta turesa baya.
Cikin kuka ta nuna shi da yatsa tace "dont you dare lay your filthy hands on my body, banza macuci, dan iskA, Allah ya isa tsakani na dakai, i hate you..", kuka sosai ya kufce mata, rike kanta tayi dake mugun sara mata lokaci gudu.
Hankalin Mujahid ne yatashi baiyi tunanin Salma zata dau komai da zafi ba ayadda takeson shi.
Matsowa yayi kusa da ita tayi saurin ja baya, kaman zaiyi kuka yace "plz forgive me, i was only joking, nasan kinji komai wlh ina sonki Salma"
Wani mugun tsanan shine taji ya diru azuciyan ta, she has never been humiliated like this in her life, kuka sosai take cike da tausayin kanta, tarasa miyasa Mutane biyu nan Abbanta da Mujahid datafiso arayuwan ta suka fi kowa kuntata mata. Innalilahi kawai take ambata aranta.
Kallon shi tayi tace "ko kana sona ko baka sona i dont give a fucking damm about it, cox ko kaine autan maza na hakura dakai, na gwamma ce na kashe kaina akan na aureka balle na zauna dakai" sautin kukan tane ya karu ta juya da gudu ta koma gurin motar ta, binta yayi shima da gudu yana kiranta, bata saurare sa tashige motar taja ta wuce ta gabansa wanda kiris ya rage bata kwashe saba, bai damu ba yabi motar da gudu amma tuni ta fice daga gate din.
Hannu Mujahid ya daura akai cike da tashin hankali yace "Am died...
Muryan Abdul yaji abayan shi yace "in life you rather learn leason the easy way or the hard way, da dukkan alamun i don't think she will ever accept you back".
Kuka Mujahid yahau yi cike da haushi abunda ya shirya dan rama abunda tamai, gashi komai ya fado kanshi.
[9/7, 12:38 AM] Xarah Bukar: ​​Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION {NWA}
Allahu akbar kulu'nafsi za'ikatu mauti, Allah yaji kanki da rahma Maman besty Yar ficika. May jannatul Firdausi be ur final destination.
63
Daran ranar Mujahid bai samu rintsawar arziki ba, ta b'angaran Salma kuwa bata san duniyar da take ciki ba, Salim kam yafi kowa farin ciki ranar, kodaya koma gida kwanciyar sa yayi yana hagon yadda rayuwarsa zata kasance tare da abun kaunar sa.
Washe gari babu wanda ya lura da Salma bata gidan, sai kuwan azahar da Kulchumi mai gyara mata jiki ta shiga dakinta yi mata wanka turare, wayam tagani babu alamun Salma tayi kwanan dakin, bandakin ta leka bata nan ta fice da azama ta fad'i ma Momy rashin ganinta. Ran Momy ne yabaci, shiga d'akin tayi dan tabbatar da zancen kulchumi, mamakine ya kamata gasgata zancen, da sauri tahau kiran nambar salma da wayar dake hannuta, ringing take bamu mai dauka.
Fitowa tayi waje ta hangi motar Salma a parke, mamakone ya kuma kamata toh ina salma ta shiga by this tym, karasawa tayi bakin motar hade da lekawa ciki ta hangi wayar Salma ajiye kan seat, bude motar tayi tadau wayar hade da duba dawa tayi waya last, sunan Mujahid tagani, ranta ne ya kuma b'acci, atunanin ta ko Salma na gidan su Mujahid, afusace ta koma cikin gida, batare da bata lokaci ba ta kira wasu yan'uwanta uku suka shiga mota zuwa gidan Hajiya.
Mujahid kam duk ya figi dare daya, tun yana jiran Salma tadau kiran wayarsa harya saduda ya zubawa wayarsa ido karshe yanke zuwa gidan su yayi Abdul ya hanashi da cewa ba lailai ne ta saurare shi balle yanzu da gidan ke cike ana hidimar buki, kumai ai Salma bata fasa auran saba tunda har yanzu basu ji bayanin komai daga bakin hajiya ba. Da wannan kalaman Mujahid yadan ji sanyi aranshi.
Annah baki har kunne, Jallabiyo yi ne matsu tsada gabanta tana zaban nasawa yau adaran Arabian nights, dakin makil yake da wasu yan jikokonta da yan'uwan ta, sai zolayar ta suke tana masu tsiya, Hajiya ce ta shigo dakin adan birkice taja Annah suka fito haraban gida kasancewar ciki makil yake da bak'i yan buki.
Cike da kidima Momy tace "Annah kinga Salma gidan nan ?
Tsaki Annah taja tace "dalilin katsamin jin dadi kenan.
Mom tace "yanzu momyta ta kirani ta tambaye ni, nace mata bata nan, da alamun kuma ba lafiya ba"
Gaban Annah na yafadi, aranta fadi take "sabon tuggu kuma yaran nan suka kulla dan karna rakashe abukin nan, toh wlh baku isa ba"
Magana zatayi sukaga an bude gate motar su Momy ya shiga da gudu, parking tayi duk suka sauko fuskar su dauke da kunci.
Babu ko gaisuwa Momy ta dubi Hajiya tace "kun mamaki wlh, a tunanin na Salma bata da wata uwa data wuce ni shine zaku rabani da ita sannan kuma kice min ke baki ganta ba, kuma ni nasan tana gidan nan"
Tashin hankali ne ya mamaye Hajiya, nanta hau kokarin fahimtar Momy da kwatakwata ta kasa gamsu wa da kalaman ta, Annah kam binsu tayi da ido tana tunanin indai dagaske Salma guduwa tayi ko sace ta akayi ba lailane ayi buki budiri ba, itakam bazan lamunci a bata mata bojet ba ayadda ta shirya juya mazauni wanga bukin. Kamar an tsikareta ta fashe da kuka hade da daura Hannu akai, duban ta su Momy sukayi adan tsorace.
Cikin kuka Annah tace "Kuyi hakuri duk laifi na na, nice na tura Salma Kano amso min may an in ciwon idona, batayi niyyan zuwa ba saida nace idan bata jeba zan hanata auran Mujahid, ba shiri ta kama hanya batare da bata lokaci ba" kuka sosai Annah ta kara fashewa dashi.
Ran Momy ya gama bacci, kasa magana tayi ta juya tace da yan'uwanta su tafi, yaukam taga matsayin ta gurin Salma da danginta.
Kirata Hajiya tayi ko kallan ta batai ba suka shiga mota yaja. Takaici ne yakamata Hajiya ta dubi Annah da har yanzu kuka take, kasa ce mata uffan tayi ta koma cikin gidan. Dariya Annah tayi tare da debo rawan shoki tana fadin "yo ina dalili kura da daukan kayan kare dashan bugu, ai baima yuyuwa ne dan ita baa ganta ba nasan halin hajiya sarai sai afasa bukin".
Da bacin rai su Momy suka komo Gida, gurin Daddy ta nufa ta tsara mai abunda ke faruwa, shikam baidau komai da zafi ba yace ba komai karta damu aci gabata kudanar da buki, inayaso ranar da Salman ta dawo shi yasan yadda zai nuna mata rashin kyautawar sanar dasu da batayi ba.
Jiki sabule Momy ta amince da hakan, ba yadda ta ita tunda shi daya kawo Salman ma baiji haushi ba.
****
Da daddare aka fara shirin Arabian night, su Mujahid kam suna zaune tare dasu Abdul harda Mubarak ba yazo, hirar su suke basu da damuwa banda Mujahid dayayi sukuku dashi, yasan ko karan hauka ne ya cize Salma bazata fito arabian nights ba, wayarta ya kuma latsawa kira tana ringing ba'a dauka ba, babban matsalan shi ma yarasa wa zai tunkara da maganar dan yasan duk wanda yaji maganar a iyayen saidai kuwa afasa auran..wata zuciyar tace miye zaka damu tunda kaji shuru kila ta hakura ayi auran, murmushi yayi zuciyar sa nagasgata masa hakan.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.