Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 5 of 41
Tuk'i Mujahid yayi yana tunanin yadda xai rama wulakanci da Salma tamai, danya lura ma kallon banxa Salim yamai daxu duk akan rainin da salma tamai agabansa.
Sallah ishai da yaji ake kira yasa yayi parking a gefe hanya ya shiga masallacin dake gurin, bayan ya fito ne ya tuna da Junaina, wayarsa ya fiddo ya kirata, alokacin kuwa tanai zaune tare da Hajiya a Palo suna hira taji kirar sa.
Dauka tayi ta mike hade da matsawa can gefe da ita
"Yaya kana ina, daxu naji Hajiya da Aunty Bilkisu suna waya, kuma kaman zancen kane, hajiya nata fada.
Dafe kai yayi, yace "kin dawo gida ne "
Haushi ne yakamata, sai yanxu ya tuna da ita, tace "eh nadawo".
Katse call din yayi ba tare dayace komai ba, kallon wayar tayi kaman tayi ihu, jiki sabule ta koma ta zauna.
Tsaki yaja hade da kallon agogon sa, takwas da rabi na dare, muddin yaje gida yanxu xai hadu da Hajiyarsa, shawara ya yanke na zuwa Officers Club kafin sha daya ya koma gida, yasan by dat tym tuni Hajiya tayi Bacci.
Nima xarah nace na tayi yin wanka kafin mu hadu Officers ClubðŸÂŠðŸÂ¿ðŸÂŠâ€Â♀ðŸÂŠâ€Â♀ðŸÂŠâ€Â♀
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: *Zuma Sai Da Wuta*
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
Fatan Alheri gare ku Nagartattu.
Benaxir Omar
Lubie maitafsir
M jabo
Futha lurv
Biebee Isa
Queen miemee
Jeedah Aliyu
Fiddausi Sodangi
Miemee bee
Mom Fatee
Khadeeja Candy
Pharty BB
Mr umar
Mamu
Deeja Abdul
Asee B Aliyu
4 Stars
Raz
Safha
Da duka wanda ban ambata ba.
*Jinjina Ga kawata Zuwairat (Umm Maryam) Allah ya kara basira da kaifin Ido*.
*Ayusher*
*Sumayya Salees Sadeeq*
*Billyn Abdul*
*#Ana tare*🙌ðŸÂ¿
*Wannan Shafin naki ne Shuwah Darling, ilysm* â¤â¤
15 - 20
Tafi mintuna ashiri da shiryawa cikin fitinannan matsatsan english wears riga da wando da sukayi mutukar fiddo da azahirin shape din jikinta, kai komo take a tsakar dakin tanai saka da warwaran neman hanya fecewa. Lek'awa tayi ta k'ofa ta hange Daddy da mom zaune parlour suna hira, susucewa tayi ta koma ta zauna hade da latsar nambar Salim.
Yana tsaye bakin mota yanai jiranta ganin call dinta yasashi azaman dauka.
"Kayan da kika shanya sun bushe" Ya fad'a cike da takaici zaman jiranta da yake.
"Ya salim am sorry kaban tym kadan, narasa yadd zan fito, su Daddy sun babbake apalo"
"Minti biyar nabaki idan baki fitowa zan koma daki na kwanta"
Tsaki tayi ta kashe wayan.
"harshi zai bata minti biyar waye shi" Aranta ta fad'i.
Wardrope ta bude tadau dogon hijab dinta mai hannu ta sanya sannan tadau wipes to goge red lipstick dake shafe bisa sexy lips dinta. Math textbook dinta ta dauka da biro sannan ta fita zuwa palon, kusa da Mom ta zauna tana dubu textbook din sannan ta kalli Daddy fuska shagwabe tace "Daddy nayi misplacing calculator dina gashi kuma ina da assignment dazanyi"
Murmushi Daddy yayi jin diyar shi taci serious da karatu, yace
"ki duba dakina cikin drawer bazaa rasa ba"
Mikewa tayi da azama, cikin sauri tace "yauwa Daddy, nagode, Mom gud nyt" ta karasa maganar hade da sauri fad'awa dakin Daddy.
Dariya Mom tayi suka cigaba da hirar su.
Kaman munafuka tadau calculator din ta fito, sad'af ta wuce hanyar kitchen ba tare da iyayan sun lura ba, cabinet ta bude ta ajiye textbook da cal din da hijab din jikinta sannan ta bude k'ofar ahankali ta fice waje bayan ta rufe da mukulli.
Salim dake tsaye yana kallon tahowar ta susucewa yayi, gabadaya ta rikitamai tunani wani abu yaji yana tsikaran shi da azalzalan zuciyan shi.
Bai ankara ba yaji ta gabansa yana shakar kamshi dake tashi jikinta.
Harara takai mai tace "wannan kallon fah, kasan dai i hate it, ka kama kanka"
Sose keya yayi baice komai ba ya bude mata motar ta shiga sannan shima yaja.
Officers Club...
Sun iso yayi parking, tura kofar Salma tayi ta jita gam...
Bata rai tayi ta dubeshi
"Miye haka".
Kallon ta yayi, gabadaya idanunsa sun sauya launi, hannu yasa ya fizgo ta jikinsa sannan yace "ki bani chance Salma, ina mutuwar sonki"
Kallonsa tayi cikin ido ba tare da tayi yunkurin dagowa daga jikinsa ba saima murmushi ta sakar mai hade da kai fuskan ta daidai fuskar shi suna jin numfashin junan su, kallon ta yake yanai tunanin kota amsa mar soyayyar ganin yadda ta sakar mai jiki, da kuma bakin junan su dake daf da hadewa, kallon lips din yayi, yana gaf da daura nasa yaji ta bugu uban tsaki hade dakai hannuta bisa lock tayi unlocking motar, janye jikinta tayi ta bude kofar ta fito ta zagaya bangaran sa ta window tace "kasan dai halin Daddy, karma ka fara" wuce wa tayi ba tare data jira cewar saba.
Numfashi ya sauke mai dauke da tari wahala da shaawa data motsomai, kallon joystick dinsa yayi ya ganta tsaye k'ekam, saidai ba yadda ya iya mafitar sa daya yasa hannu karkashin sit yadau kwalba mai dauke da barasa (giya) ya fara tuttulawa bakinsa.
Cikin takun isa da takama ta shiga gurin mai dauke da disco light, hadaddan gurine na watayawa, kowa da abinda ya shafe shi, ba ruwan wani da wani, wasu mazan na gefe suna rawa da yammata wasu kuma zaune suke gurin wine bar, wasu kuma makale da yammata su suna shan minti, wasu kuwa chess game sukeyi.
Fara taku tayi gurin Wine bar taji wani a bayanta,
"Yammata..
Juyawa tayi
Yace "kin hadu fah, da irinku yadace aje Dubai hutawa.
Yak'e tayi hade da fari da Ido, aranta tace da uwarka zakaje Dubai hutawa badai dani ba, shege mai kan kwakwa.
Afili tace
"Dagaske" cikin nuna farin ciki, wayarsa ce tayi ringing yadauka hade da jan hannuta suka karasa gurin hade da zama kan long backless chairs dake gurin...
Daga can Gefe yake zaune, yana kallon abunda ke gudana agurin, agogon hannusa ya duba yaga goma ta cika, guntun tsaki yaja hade da gyara zama, ya dubi bartender dake guri..
"Bani sigari guda daya".
"Yes sir" bar tender ya fadi hade da mai lightening sannan ya mika mar.
"Sir do you need wine or beer ?
Kallon banxa da Mujahid ya wulla mai yasashi tsuke baki.
Cikin kwarewa ya fara zugarta juyawan da zaiyi ya hangota tanai kokari saka hannu cikin aljihun wanda suke zaune tare, ware ido yayi yana tuna abunda fa'iza tace mai akan yarinyar barauniya ce.
Shikam ya shagala da waya, Salma ta ciro wallet dinsa dake ajiye, budewa tayi taciro dari biyar biu dake wallet din.
Mugun tsananta Mujahid yaji hade da saurin dauke kai gareta.
Tsaki taja tana fadin "matsiyaci ko kudin kirki baya shi" maida kudin tayi cikin wallet din sanan ta maida mai abarsa ta mike tsaye, saurin riko hannuta yayi yanai mata nuni da karta tafi, harara takaima sannan ta fizge hannun tayi gaba.
Cike tsananin bacin rai Mujahid ya gama yiwa sigarin zukan Allah tsine uwar hegu, sannan ya mika hannu gurin bartender yana fadin karomin daya"
Mikomai bartender yayi, hannusa yasa zai amsa yaji hannu wata bisa nashi tanai shirin amsan sigarin saidai kafin yakai ga amsa ta rigashi amshewa.
Saurin Duban ta yayi dan ganin wace yar iskan ce da karfin halin shiga tsabgarsa.
"Kallamu ka gama kallo..." Ta fada cikin salo rainin wayo, kallon ta yayi saidai mamakin ganin tasa sigarin abakinta yasa shi sank'amewa gurin...
Dariya tayi ta cire sigari daga bakin ta
tace "i never knew the decent and useful policemen smoke, much less a indoors inda babu wanda zai gansu"
Shikam ya gama kulewa da ita, tashi yayi ya canza guri dan bazai iya tanka taba yadda yake mugun jin tsananta da haushinta.
Matsawa tayi inda ya canxa tanai kuma darawa, tace "karka damu your secret is save with me, am sure irinku ke claming goods guys a gida"
Tsaki yaja aranshi yace "shameless bitch"
Karaf a kunnan ta baisan ma ya fada fili ba.
Ranta yadan sosu, sai yanxu ta gane kallon dayake mata, murmushin dole tayi tabar gurin. Fita tayi ta wurgar da sigarin sannan tahau goge bakinta, abunda bata tama yiba asalima taimakon shi tajeyi, saidai inya san wata bai san wata ba, hannuta dake dunkele ta bude kallon agogonsa data zare ba tare da sanin saba, murmushi tayi ta cusa a bra dinta sannan tahau nema Salim su koma gida. Can lungu daga baya taganshi da azama ta karasa gareshi ganin baya cikin hayyacin shi banda barasa dayake ta kokarin sha, idon ji jajir.
"Na shiga uku, yaya miye haka" ta fada cikin tsoro, rikoshi tayi da niyya dagoshi suka fadi kasa tare ayayinda yake ta suburbuda surututai game da yadda yake sonta.
Tsaki taja, duk ya shafa mata giya ajiki, barin gurin tayi neman temako.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.