Complete Hausa Novels

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 31 of 41

Tsaye Salma tayi bakin stairs, har yanzu jikinta baibar rawa ba, she need to be strong karya raina ta much less yanzu da take ganin ya riga ya gano sonshi a kwayar idanta, tanason Mujahid saidai wata zuciyar taki aminta dashi, tsoro take ya yaudari zuciyar ta datayi mugun kamu da kaunar sa. Muryar Annah taji a fito palo tana fadin "ba kowa agidan ne" leke tahau yi ganin babu kowa gurin, Tsoro ne ya kama Salma lafewa tayi gurin ba tare data iya k'wak'waran motsi ba. Jafar da Junai ne suka shigo, sai wani narkemai take shi kuma yanai biye mata. Tsawan Annah sukaji akansu, afusace tace "wanan sabon salon fah, miye haka ?
Harara Junaina takai mata, Jafar yace "Miya faru ?
Nuna Junaina tayi da sandar hannuta tace "dan baki da kunya Mijin Yayar taki kike narkewa haka"
Ware idanu Salma da Junaina sukayi atare jin abunda tace, Junai tace "ban gane miji yayata ba?
Tsaki Annah taja tace "uwar taku bata fad'a muku ba, toh bari kiji dakyau ita Yayar taki data fiki nutsuwa itace matar Jafar, ke kuma da Mujahid da kuka raina ni tare zaku dauwama"
B'ata rai Junaina tayi, tahau gunguni hakan bazai yuyu ba, sandar Annah ta daga da niyyan kai mata tayi sauri fecewa hanyar dakinta da gudu.
Salma kam daskarewa gurin tayi, kallon ta Jafar yayi tayi sauri kawar da kai gefe kaman mai shirin yin kuka.
Duban jafar Annah tayi tace "muje daki, akwai abunda zan gayama" afusace ta juya yabita abaya yana mai cigaba da kallon Salma, jiki sanyaye Salma ta sauko ta wuce daki.

Adakin Annah kuwa abubuwa da dama tayi ta kimtsa wa Jafar akan lailai yaja Salma ajiki, shikam jinta kawai yake baice komai ba, bayan ta gama batun ta fita yayi daga dakin ya nufi gurin Salma.

Zama Salma tayi kan center carpet din dakin, kanta daure bisa gwiwar kafafunta, shigowa Jafar yayi ahankali ya zauna gefen ta, d'agowa tayi jin kamshin turararsa, kallon sa tayi yaga idanuwata mak'ale da hawayen dake kokarin zubowa, hannu yasa aljihu ya fiddo hanky ya mika mata, amsa tayi zatayi magana ya katse ta da cewa "shiiii...basai kince komai ba, i understand everything"
Shuru tayi tahau goge idanta sannan ta dubesa tace "Thank you"
Yace "you're most welcome, if you need anything, ko shawara game da brother na kina iya min magana, i'll alwayz be around to support you"
Cikin sanyi murya tace "yaya kana da kirki sosai, am sure kanwata zata ji dadin zama dakai"
Murmushi yayi, baice komai ba ya mike ya fice daka dakin. Ajiyar zuciya ta sauke ta shingid'e a gurin, tunani tahau yi daga bisani kuma ta mike ta fice Palo.

Junaina da Annah ta iske ana fadan kallon Tv, Annah hausa takeson kalla ita kuma Junai ta nace sai Disney channel, dariya draman yabata, sai kace babu Tv a dakunan su.
Ganinta Annah tayi tace yauwa diyar albarka zoki zauna nan" nuni tama Salma da tazo kusa da ita ta zauna.
Fuska ba yabo Salma takarasa ta zauna.
"ina kika baro jafar, aina dauka kuna tare". Annah ta fada tana washe hakori tamkar wanda akama albishir da abun arziki, Salma kuwa yaken dole tahau yi
Dogon Tsaki Junai taja tace "sai kace wani danta da zasu kasance tare, shifa yana study room yana wasu aiyukansa.." bata rufe baki ba taji sandar Annah abayan, mikewa tayi azabure.
"dan ubanki dake nake dazaki saki baki kina magana uwa an b'arka zani, hegiyakai tamulmule mai nono daya"
Turo baki Junai tahau yi, Annah taci gaba "niyau banma ga Mujahid ba, maza jeki kira min shi, dan tselan uwa wato bazai sauko gaida niba"
Junai kam ta gama kulewa, bakin stairs taje ta tsaya tana tunanin yadda zata doshi Mujahid.

Kallon Salma Annah tayi tace "ke kuma dauko min ruwa insha" mikewa Salma tayi ta nufi kitchen, da sauri Junai tabi ta abaya. Daukar ruwan Salma tayi ta juyo sukayi kicibis da ita tsaye gabanta tanai makamata harara.
Salma tace "lafiya ?
Tsaki Junaina taja tace "i dunno why kike claming kaman wata saint, kodayake ba wannan ya kawo niba, so nake kiyi using halinki nayan daba ko ma ince yar tasha, kisan yadda kikayi Annah ta sauya zancen ta na kokari lak'amin Mujahid da lak'amiki Jaafar"
Murmushi Salma tayi, sai kace ba rannan kadai Junai ke threatened dinta ta rabu da Mujahid ba, yau kuma table yayi turning kan Jafar.
Tace "abu mai sauki why not kicewa Annah bakya son ya Mujahid"
Ware ido junai tayi tace "so kike nasha duka kenan, muguwa kawai"
Salma tace "toh ya kikeso ayi, kinga ni am not complaining".
Mugun kallo Junai tai mata. "Ai dole kice haka, saboda jafar aka lak'amaki toh wlh baki isaba, yadda kike yar tasha da ya Mujahid kika dace, two devils"
Insult din yafara bawa Salma haushi, dakewa tayi tace "we have to work together idan kinaso musamu solution"
"Kaman ya kenan ?
Mika mata ruwan Salma tayi tace "ki kaiwa Annah ruwan, bara naje sama na kira Mujahid, ke idan kinje kice mata yana zuwa"
Amsan ruwan Junai tayi tace "idan ta tambayi ne kefa ?
"Datx your problem not mine" juyawa Salma tayi ta wuce tabar Junai tsaye gurin baki sake, dakyar ta tsaitseta kanta ta wuce gurin Annah, mika mata ruwan tayi tace gashi, harara Annah takai mata tace "akarambana waya aike ki, ina mujahid ?
Kaman marar gaskia tace "yana Zuwa, Ummi kuma ruwa ta zubar akitchen shine take gogewa tace nakawo maki ruwan".
Amsa ruwan tayi tanace mata "ja'ira harda kwantar da murya kamar gaske".

Da sauri Salma ta haura sama, tana shiga palon yana fitowa, yar gware sukayi kowa yayi saurin matsawa baya, dafe gurin tayi tana kallon yadda yayi kyau sai zuba kamshi yake, kananun kaya jean da top ke sanye jikinsa. Gyara murya yayi yace "yau kuma kinzo fasamin kai ne ?
Bata gane inda zancensa ya dosa ba, murya shagwabe tace
"Kai yaya kodan sannu babu ?
Murmusawa yayi ya janyota wajan palon yana cewa "waya biyoki kike zabga uban gudu ?
Alamun yayi shuru tamai, murya kasa kasa tace "Annah na downstairs tana jiran ka"
Tabe baki yayi "muje ki rakani Shopping" hannuta ya riko suka karasa stair, da sauri ta zame hannuta tayi saurin rigashi sauka tana dariya kasa kasa.

Yana sauka ko kallan Annah bai yiba yace da ita sannu da zama, tagane da ita yake amman ta share. Duban Salma yayi da tuni ta zauna kan kujera yace "5min nabaki kisame ni waje bakin mota.."
Mikewa tayi kaman munafuka Annah tace "koma ki zauna, ke Junaina tashi ki sameshi awaje"
Galala Mujahid yabita da ido sannan yace "niba ita nace ba, ita wace na kira kasuwa zamuje da ita"..
"Aikuwa wace kakeso bazata bika ba.... Ke Ummi shiga ki kira Jafar yazo saiya kaiki kasuwan" nuna Junai tayi tace "dauko mayafi ki bisa" kaman bazata ba ganin Salma tai mata ido yasata dauko mayafin, takaici ne yakama Mujahid ya fice daga palon Junai ta bisa abaya kaman munafuka.

Fitowa Jafar yayi cike da taikaicin katse mai aiki da Annah tayi, jarabar ta yafara isanshi, so yake sati ya kama yabar masu gidan, fitowa waje sukayi su ukun, Annah sai washe baki take, saida taga ko wana couple sun shiga mota sunja sannan ta sauke ajiyar zuciya, tace "aifa dole kowanne taso hadin nan nawa, shegun yara kawai, Sannu-sannu ba ta hana zuwa, sai dai a dad'e ba a je ba" wani mahaukacin dariya ta saki tana cewa "muje zuwa, mahaukaci yahau kura".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.