Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 36 of 41
Arabian nyt kam yayi shagali da maana, su Junaina da Jafar ansha kyau, jamaa sai tambayan Salma suke ba kunya Annah ke dankaro karya, hajiya kam ba wata walwala tattare da ita, sam bataji dadin Abunda Annah tayi ba, ganin Mujahid bai tunkareta da zancen ba yasa bata cemai komai ba, shikam gogan baisan da wata tafiyar Salma Kano ba.
****
Bayan Kwana Biu.
Tun Ranar da Salim yakai Salma Gidan bai kara komawa ba gudun kar a zargeshi, saidai yadda yaga anata cigaba da hidimar buki yasa shi mamaki, dabara yayi ya kira momy yace zai karbi mukulli mota a hannun Salma, ita kam bata kawo komai aranta ba tacemai Salma na Kano.
Dadi yaji yafara kiciniyar hada mata passport dan guduwa da ita Ghana.
Tsoron Allah ne yakama Annah bayan an gama shagalgulan Buki, daurin aure ne kadai ya rage daza ai gobe, kullum tambayar ta ake ya labarin salma saidai tace mai magani bai gama hada magani ba, Hajiya kam taso tagano Annah karya take saidai rashin damuwan mujahid yasa tayi tunanin bakin su daya, da Yamma Annah ta fita zuwa bangaran dasu Mujahid suke, gabanta sa faduwa yake tana tsoron rashin Mutuncin zai mata, ta window ta hango su zaune da abokai suna ta hirar su tare dashi kaman babu abunda yafaru, tace "kai Mujahid fito muyi magana"
Dafe kai yayi cike da takaicin mai matan nan takeso, fitowa yayi yanai aika mata mugun kallo.
Kamar munafuka ta sinne kai tace "dama batun Salma ne, baa ganta ba nace nina aiketa kano dan kar acinye min shagali, yanzu kuma naga buduri ya k'are yasa na gayama"
Agigice yake kallon ta dan kuwa bai gane inda zancen ta ya dosa ba, "wana kano taje, bata gida ne? Ya jaho mata tambayoyin.
Tsurewa tayi tace "bansani ba, kaje ka nemo ta"
Zare ido yayi in shock yace "Annah ina take ?.
Kara tsurewa tayi tace bansani ba, bata jira cewar saba ta rugu gida da gudun dani kaina bansan yar tsohuwa ta iya ba.
Innalillahi Mujahid ke ambata, bai koma palon ba ya rugu gurin motar sa yabude ya shiga, mukullin na jiki ya kunna yaja yabar gidan.
Salma bata farka ba sai washegarin daya kaita da daddare, juyi tayi taji ta tim tafado kasan, arazane ta bude ido, wani mugun ciwon kai ke dawainiya da ita, dakyar ta mike tsaye tana karewa dakin kallo, kasa gane dakin tayi ta dafe hannu jikin bango ta fito palon, tsoro ne yakamata bata gane komai na gidan ba, wani mugun jiri taji ta fadi kasa sai bacci.
Saida tayi kusan 4 hours a gurin sannan ta kuma farkawa, so take ta tuna wasu abu amma takasa, data fara kokarin tunanin saita yanki jiki ta fadi sai bacci.
The next day ne ta kuma farkawa, da sauri ta mike koma toilet din dakin, ruwa ta kunna tasha sannan ta kirkiro wa kanta amai, saida tayi amai sosai sannan ta dawo hayyacin ta abubuwa suka dawo mata, ya Salim ta fara ayyanawa aranta, wana mugun magani ne haka yabata daga ciwon kai, ita bataji saukin ciwo ba sai hallaka da magani yasoyi, tasan kuma shi kawo ta gidan, ranta ne ta baci ta mike wani jiri ya kuma dibarta, saurin dafe bango tayi, ga wata uwar yunwa nacinta, adaddafe ta fito kofar palo taji kofar a rufe kasa jure tsayuwa tayi ta rarrafa zuwa kitchen, komai na abinci akwai, tea na ruwan sanyi kadai ta iya hadawa tasha ta kuma rararfa zuwa dakin.
Sai sannan tahau neman wayarta ta tuna a mota ta barta, kwaciya tayi akasa tana tuna Betrayal din Mujahid bata sanda kuka ya kufce mata ba, agogon shi dake hannuta ta duba taga karfe biyar na yamma. Mikewa tayi ta koma toilet, dakyar ta iya watsa ruwa tayo alwala tamai da night wear din jikinta da hijab dinta tahau rama sallolin dabata yiba. Bayan ta ida ne kuma wani mugun baccin ya kuma sace ta.
Parking Salim yayi a haraban gidan ya fito rike da ledan abinci daya kawo mata, ahankali yasa mukulli ya bude kofar sannan ya shiga, kasa ya ganta kwance a dakin ta kudundune cikin Hijab, Murmushi yayi aranshi yace wato tayi kokarin yaki da maganin.
Sunan ta ya kira ta bude ido ahankali ta kallesa, bakin magana kawai take dashi amma babu wani karfi Tattare da ita.
"my love kin tashi" ya fada yana shafan fuskar ta, murya sanyaye tace "yaya why, miyasa zaka kawonin nan ?
Murmushi yayi ya dagota zaune suna fuskan tar juna, yace "Salma ina matuka sonki, bazan iya hakura ki auri mujahid ba, cox nafishi sonki"
Dakyar ta iya sakar mai harara, tace "miyasa kace ka fini sonshi
"Salma biliv me, akwai certain time danayi confronting mujahid akan ki nace mai kin zubar da cikina, inda yana sonki dagaske bazai nemi wulakanta ki ba harya yayi kokarin daura miki kisan daba ke kika aikata ba"
Kallon mamaki Salma tamai dajin shairin da yayi mata, amma toh yaushe akayi hakan Mujahid bai taba gayamata ba, wata zuciyar tace ba sonki yake ba tayaya zai gayamaki, Ajiyar zuciya ta sauke, tana son Mujahid bazata bari Salim ya nemi aibata saba.
Bata rai tayi tace "wanda kema son gaskia baya binka da shairi, no matter how bad Ya Mujahid yayi treating dina i still love him, kaga tashi ni kamaida ni gida"
Daura fuska Salim yayi yace "keda gida har abada, you're mine, Ghana zamu tafi gobe"
Mugun kallo tamai sannan ta mike tsaye da kyar tace "you're crazy, no wonder kayi drugging dina dan ka gudu dani, toh wlh baka isa ba" afusace tayi maganar, wucewa zatayi gefensa ya fizgo ta tafada cikinsa, matse ta yayi gam yana shakar kamshi jikinta, batasan sanda wani karfi yazo mata tasa hannu ta turesa hade da kai masa kyakyawan mari.
Kallon mamaki yayi mata sai kuma ya kwashe da dariya uwa tababbe, hannu yasa cikin aljihun sa yadauki wasu kwayoyi gudu biyar ya watsa a bakin sannan ta kalleta
"Ni kika mara ?
Harara takai mai.
"Dont you dare touch me, banza marar hankali"
Murmushi yayi hade da lasar labb'an bakin sa, ya karasa daf da ita ya shako wuyanta tare da hijab dinta, zare idanuwa tayi da already sun canza launi, magana take sonyi takasa tsananin yadda taga ya koma mata uwa zaki, harshen sa yakai kan fuskar ta yana lasa, da sauri tasa k'afarta ta ture sa hade da matsawa, yawu ta hada abakin sannan ta tofa mai a fuska tace,
"wanna ba so bane, rashin hankali ne" akufule yace ni kika tofawa yawu ?" Ba tsoro tace "eh kai din, niba kare bace da zaka na lasar min fuska."
Haushi da takaici ya cika sa, ya tako gabanta tare da bata k'akk'aywan mari guda biyu a fuska, ihu ta sakani dan azaba, bakinta ya fashe yana zubda jini, yace "zan nuna miki kare ya fiki daraja"
Daukar ta yayi tsam ya wurga ta kan gado.
Ihu take tana kiciniyar kwace kanta, shikam ko kallon baiyi ya yage wuyan hijab din ya cire, danne mata hannuwa yayi yahau kai mata kisses ta ko ina ajikinta, kuka tasoma tana rokansa, bai saurareta ba yahau kiciniyar cire mata riga, ringing din wayarsa a aljihu ne ya katse mai hanzari dubawa yayi yaga Mom ce, gabansa ne ya fadi yayi saurin dagawa daga jikinta, itakam Salma kuka take, kallon ta yayi duk ta firgice, yace "zanje na dawo inci gaba daga inda na tsaya"
Sauka yayi kan gadon tayi saurin rikosa "yaya kayi hakuri, na yadda zan auraka, dan Allah karka cuci rayuwata, ka kaini gida plz"
Yace "saboda kin raina ni ko, na maida ki gida dan ki auri wacen banza ko ?
Kai ta girgiza, tsaki yaja ya tureta da karfin gaske har tana bugewa da gadon, yayi gaba ya fice yabarta nan dafe da kanta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.