Complete Hausa Novels

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 21 of 41

*****
Washe Gari.

*Kaduna*..

Jaafar ne tsaye bakin motar sa bayan su kammala shari'a da sukai tayi kusan kwanakin da suka shud'e a Supreme court. Bude motar yayi ya ajiye tilan takardu dake hannunsa sannan ya shiga motar, yaja komawa Birnin tarayya (Abuja).

*Abuja*

Tun Safe Salma ta birkice kayanta gabayada tanai neman wanda ya dace tasa, karshe dai white jean da pink top ta ajiye gefe sannan tadau Hoton Mujahid wanda tuni ta wulla a trash can kwanakin baya saidai daga baya tacire ta adana shi, daukon hoton tayi tana kalla hade da lumshe ido, daga bisani ta bude pink cluth bag dinta ta ajiye frame din ciki, wanka tayi ta fito ta sannan ta zauna jiran karfe hudu ta cika.

K'asa Zaune Salim yayi a office, duk mintina kallon agogo yake, yana fitowa sallah azahar, joint dinsu na yan shaye shaye yaje, saida yayi tatul sannan yahau kuka yana tunanin yadda zai raba Salma da Mujahid, rasa mafita yayi daga karshe ya yanke shawaran zuwa Garden din Kidnapping dinta kafin su hadu da Mujahid.
Karfe uku da rabi nayi Motar sa ya shiga yaja yanai wani reckless driving har ya isa Garden din, black Face mask daya siya na musamman yadau ya sanyawa fuskar sa sannan ya shiga Garden din cikin sadaf ya boye cikin wata bishiya.
Katon Scissors ne Hannu Baba Nayaro, sai gyaran wasu flowers yake cikin sauri yana duba lokaci kar Salma ta iso ta iske bai gamaba, aiki yake sosai yaji alamun saukar Numfashi daga ina yake, dakatar da aikin yayi yafara takowa gurin yana fadin "waye anan...?
Tsoro ne ya kama Salim, da sauri ya fito yakama wuyan Baba nayaro, yace "sshh kamin shuru karka kuskara kayi ihu"
Kokarin kwace kansa Baba nayaro yahau yi, yakasa, iya karfinsa ya take kafar Salim, da sauri Salim ya sakarmai wuya, Guduwa Baba nayaro zaiyi Salim yayi saurin rikosa hade da kwashe tsoho da mari, nan take fada ya kicibe tsakanin su, sukahau dambe, duka sosai Salim yama baba nayaro, ganin yana kokarin guduwa yasa ya dauki scissors din zuciya daya ya caka mai atsakiya cikinsa, ihu Baba yayi ya fadi kasa bakinsa na ambato kalmar shahada, tsoro da firgice ne yakama Salim ganin yadda jinin Baba ke bulbula, hankali tashe ya cire mask din fuskarsa yahau yiwa Baba sannu, nunasa Baba yayi da yatsa yace dama kaina....,
Tsorata Salim ya kuma yi da sauri ya ruga da gudu yabar gurin cike da tsananin fargaba.

Fuska dauke da seriousness Mubarak ya iske Mujahid, yace "Mjay tashi muje na nunama wani abu"
Dubasan Mujahid yayi kaman bazai kulasaba ganin yadda yaci serious first tym in his life yasa shi cewa "miya faru ?
Mubarak yace "it urgent, plz tashi muje banaso ka cikani da tambaya"
Kaman bazai tashi ba, daga baya kuma ya mike bayan Mubarak ya fice a office, "this is not good" Mujahid yafada aransa, atunanin sa ko batun wani crime ne Mubarak yakeso suje sugani, drawer na table din ya janyo yadau bindigar sa da Handcuffs yasa a ajihunun sannan ya fita, gurin mota ya iske Mubarak, shiga sukayi Mubarak yaja motar.

Hudu na cika Salma ta kammale shirin ta, jakarta da hoton ke ciki ta dauka sannan ta fita palo, dakin Mom ta nufa da sauri tai mata sallama akan zataje shopping sannan ta fito, bata dau motar taba acewarta kar Mujahid yagani bakin garden din yafasa karaso wa ciki, Fita waje tayi ta Tari Taxi ya kaita Garden din.

Tana shiga Garden din wani irin fresh air taji da farin ciki, fatan ta Allah yasa Mujahid yace yana sonta da sai tafi ko wace farin ciki.
Taku daya biyu zuwa uku tayi tafara ganin d'ison jini, bin jini tayi har inda Baba nayaro ke kwance, cike da tashin hankali ta tsugunna gaban sa takiran sunansa, jini sosai ke zuba saman cikinsa, hannu ta tasa ta tari jinin tana ambatan innalillahi wa inna'ilaihi rajun, jijji gashi tahau yi ko motsi baya yi, tuni hannuta da farin wandonta suka kwashi jini, ihu take tana kiran sunan baba.

Parking Mubarak yayi, kallan sa Mujahid yayi yace "wai miye zan gani anan ne, nifa ban ciki da wasan ka na banza.."
"Fito muje" Mubarak ya fadi, fito wa sukayi suka shiga Garden din, suna tafiya Mujahid yaji ihu, kallon Mubarak yayi yace "whats going on ?
Kafin Mubarak yayi magana sukaji wani ihu, atake maza suka rafta da gudu inda ihu ke tasowa.

"Na shiga Uku" Salma ta fada, tanai kokarin cire Scissors din dake makale jikin cikin Baba, kasawa tayi ta mike hade dasa duka hannunta biyu akan scissors din da niyyan cirewa.
"Mi kikeyi anan ?
Muryan Mujahid taji agabanta, sam bata lura da tahowar su da gudu ba, adan tsorace tayi Baya ganin mugun kallon dayake mata, "ba komaii" ta fada cikin inda inda.
Tsayawa gefe Mubarak yayi, Mujahid ya karasa hade da Taba wuyan Baba, babu alamun rai tattare dashi, kallon Salma yayi, cikin karaji da zare ido yace "Uban mi kika yimai ?
Kaman zatayi kuka tahau fadin "nima haka naganshi.."
Mujahid ya gama kulewa, ko daya bai yadda da abunda tace ba, yace "ni zaki rainawa wayo, munafuka, yar daba, karuwa yar iskaaa..."
Katse shi Mubarak yayi da cewa "mjay stop it mana, baka da hankaline kake tunanin karamar yarinya da kashe tsohon mutum haka..".
Kallon banza yama Mubarak sannan ya dube Salma hade da ciro bindigar da handcuffs, nunata yayi da bundigar, fuskar ba annuri yace "you're under arrest ..."
Katse shi tayi da cewa "yaya dan Allah kayi hakuri, wlh bani bace, believe me.."
Tsawa ya bugu mata dasaida yan hanjin ta suka kada yace "shut up, you have the right to remain silent, anything u say can and will be used against you in a court of law..."
Iya kuluwa Mubarak yakai, ganin Mujahid da gaske yake arresting salma zaiyi yasahi, riko hannusa "Mjay, calm down mana, kar kayi using personal issues dinka da aikin ki, we both know ba ita ta kashe shiba".
"Karya kake, am sure itace tayi kisan kuma abunda yasa ka kawo ni nan kenan danna gani da idona"
Kallon Salam Mubarak yayi yamata sign din ta gudu, tagane da sauri ta juya zata gudu, mujahid yace "don't you dare walk out on mee"
Tsayawa tayi chak, kuka takeson yi dan taji dadi takasa, kwata kwata ba mujahid din data sani ne wanan ba saidai she isn't stupid dazata tsaya yayi arresting dinta abanza.
Tana jin yafara taku daya biyu a bayanta tayi sauri afkawa da gudu, Tsayawa Mujahid yayi yana kwalla kiran sunanta, ganin bata da niyyan tsaya wa yasanya shi pulling trigger, daidai kafardar hannuta Bullet din yabi ya karce ta, ihu tayi sosai, wani mugun jiri yafara daukar ta, bazata iya tsayawa ba ta cigaba da gudu hade da rike gurin wanda tuni jini yafara zuba.

Ko ajikin Mujahid saima kokarin kara kai mata harbe da yake, wani Mugun Mari Mubarak ya tsakar mai, suka haure da Dambe...

Hankali tashe Salma ta fice a garden din, kan titi tayo da gudu tana neman madafa, kasancewar titi high way ce yasanya motoci daidaiku ke wucewa aguje batare da sun lura da ita ba, titin ta kalla da idanuwan da sukayi dishishi, kallon bayanta tayi taji tsoron kar Mujahid ya kamata, da sauri ta ruga tsakiyar titin, kafin takai ga gangarawa kasa wata BmW ta kunno kai, kiris ya rage bai kwashe taba yayi saurin taka burgi, itakam stars tafara gani nan take jira ya kwasheta kasa...
"Subhanallahi" Jaafar ya fada ganin yadda ta zube kasa, ga jini ta ko ina ajikinta, fitowa yayi da sauri ya karasa gurinta, kallonta yayi gabansa ya fadi, "Ummi.."
Ya kira sunanta a akideme, daukarta yayi yana jijjiga, yana kiran sunanta, ahankali ta bude ido ta kalle shi, "Help me..' Ta iya fada, kanta ya fado bisa Kirjinsa alamun babu rai tattare da ita...

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.