Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 26 of 41
55
Daddy na shiga d'akin yayi farin cikin ganin Salma ta warware, nan ya basu albishiri din yadda komai ta kasance. Mom kam tafi farin cikin rashin aikin mujahid sai d'ura mai zagin Allah tsine take. Hajiya kuwa murmushin dole kawai take, tana mamakin karfin hali irin na Mom, kodayake Salma diyar tace duk abunda tace daidai ne. Salma kam tagama gano komai da Reaction din Hajiya sai fama yiwa Mom ido take akan tayi shuru bata sanma tana yiba. Aunty Bilki ma tazo dubata, sun dade asibiti kafin daga bisa suka koma gida.
Kwana su Salma biyu a asibiti Likita ya sallame su. Gidan Mom suka wuce wanda ba hakan Hajiya taso ba. Bayan kwana biyu kuwa Daddy dakan sa yacema Salma ta shirya Jafar ya kaita gurin Hajiya tayi mata kwana biu, dadi sosai taji dama ta jima dason tambayarsa zataje sai Allah yasa ya furta mata hakan.
Ranar da zasu Jafar na waje parking lot yana jiranta, ita kuma tana tare da Mom a palo suna Sallama, mik'e mata wayarta Mom tayi tace
"Saura idan kinje ki manta dani"
"Haba Mom taya zamanta dake, kece fah uwa ta" ashagwabe tayi magana.
Kunnan ta Mom tajA, cikin zolaya tace "banda rashin ji, kinga Allah ya kawo maki mijin mai kirki karna kuskura naji kinma Jafar rashin Mutuncin, nasan halin ki"
Dan k'ara Salma tayi hade da cizge ruk'on da Mom tayi mata, dariya tayi sannan tace "kai Mom ina laifin wanda ya taimake ka cikin tsaka mai wuya"
Dariya sukayi atare sannan sukayi sallama, har bakin Motar Mom tarakata tanai kara mata fada, motar zata shiga ta hangi Salim bakin window dakinsa yana kallonta, dauke kai tayi tana mamaki yadda yake acting crazy kwana biyun nan. Saida Mom taga sunja sannan ta koma ciki.
Shuru sukayi kowa da abunda yake sak'awa aransa, satan kallon ta Jaafar yayi yaga tana juya wayar dake hannunta, da alamun kuma tunanin take ganin bata cikin hayyacin ta. Cikin cool voice yace "tunanin mi kenan, ko har yanzu jikin ne ?
Sai sannan ta dawo daga duniyar tunanin inda jakar ta da hoton Mujahid suke, tasan dai tare suke da wayarta cikin jakar amma Wayar kadai Mom ta bata ba jakar.
Murmushin ta saki hade da dubansa, tace "everytime i close my eye kai nake gani, kana da kirki sosai"
"Uhmm are you sure, ba wani can daban kike gani ba.." Cikin zolaya ya karashe zancen.
Dariya tayi bata ce komai ba, banda murmusawa da take.
Gabadaya duniyar tama Mujahid zafi, ba aikin fari balle na baki duk zaman kadai ce ya ishe ba, tun ranar dama bai kuma bi takan Salma ba, mugun haushi da tsanarta yake ji duk asanadin ta ya rasa komai, one thing dayafi damunsa shine yadda ya kasa yakaceta aransa, wani mugun Tsaki yaja hade da kaiwa hannusa daya haushi, gidan dayake zaune ma bakin kirin yake ganin sa tsbar takaici, mikewa tsaye yayi daga kan kujerar palon da yake zaune, kai komo yahau yi yanai nemawa kansa mafita, karshe dai ya yankewa kansa komawa Gida tunda dama ba koransa akayi ba shiya kori kasan, duban agogo yayi yaga biyar na yamma ta gota fasa tafiya yayi ya bari zuwa gobe.
Suna isowa Gidan, Salma ta jinjina kyan da girman gidan, fitowa tayi daga motan tanai karewa ko ina kallon, kallon Jafar tayi, tsaye yake bakin boot yana ciro trolleys dinta.
Tace "wow yaya this house is beautiful.."
Magana zaiyi sukaga an bude gate motar kirar avensis ta shigo, dauke kai Jafar yayi, salma kam kallon motar take har tayi parking idan suke tsaye, Junaina ce ta fito amotan hade dakaiwa Salma wani mugun kallo aranta tana fadin "i cnt believe this devil is my sister" wani mugun tsanan Salam takaraji tun ranar da Hajiya ta fadi mata ita kanwar tace, dan haushi ma ko asibiti kasa zuwa dubo ta tayi.
"Ya jafs ina wuni" tafada batare data kalle saba, tayi wucewarta
Bai amsa ba, sai kallon Salma dayayi yaga duk jikinta yayi sanyi, murya maraice tace "i dont think she will forgive me..
Yace "she is very angry but trust me she will hose down"
"I pray so" Salma ta fada hade da sauke ajiyar heart, ciki suka karasa, Hajiya na zaune palo tana kallon aljazeera, ladabce Salma ta gaidata, farin ciki mara misaltuwa ne lullube Hajiya, kasa zaune tayi ta mike tahau nannan da Salma, babban dakin mai kyau anan kasa Hajiya ta nuna mata amatsayin nata, Salma kam kin zama tayi ta nace lailai ita a dakin Hajiya zata sauka, hajiya kam taji dadi hakan, ranar kam Salma taga gata gurin Hajiya da Jaafar, sai wani narke masu take suna biyeta, Junaina kam sai binta da harara da tsaki take, zama tayi dakin tahau trying namban Mujahid dan kai masa rahota, taji wayarsa kashe.
****
Washe gari Mujahid yayi shirin sa tsaf cikin kananun kaya dayayi matukar fiddo azahirin kansa, kulle gidan yayi ya fada motarsa yaja yabar Gidan.
Bayan sun kare breakfast, wajen gidan Salma da Jaafar suka fito yanai nuna mata ko ina da garden dun gidan. Kaman masoyan juna gwanin shaawa suke tafe suna darawa abunsu ba tare da matsala tattare dasu ba, zayawo sukayi suka tsaya bakin motar sa, da alamun fita zaiyi.
Marairace murya tayi tace "yaya yaushe zaka dawo ?
Folding hands dinsa yayi a kirji hade dakai mata wani killer smile, yace "tun baje gate ba harkin fara missing dina"
Dariya tayi, sai kuma ta tsayar da dariyan tace
"Yaya you're very special,
Shuru sukayi suna duban juna for some seconds sannan tace "plz karka dade.."
Agogon hanusa ya kalla yace "i promise..
Okay bye" ta fada..
Kashe mata ido yayi, sukai smiling atare sannan ya shiga motar yaja.
Palo ta komo hade da sauke dogon ajiyar zuciya, sai sannan ta tsaya karewa ko ina na palon kallo kasancewar babu kowa..
Palon ya hadu, idanuwan ta suka sauka kan Katunan frames mai step guda biyar manne jikin bangon palan, wata farar kyakyawan Tsoyuwar mai glass ce a babban frame din, "ko wace ce wannan" ta fada.
Mai bi masa ta kalla Hajiya da late Abban su Jaafar wanda sanye yake da kayan Sojoji, sai saura kuma hoton jaafar, junaina da Mujahid, sun mata kyau sosai, kallon na Mujahid tayi ta buga uban tsaki aranta tace "to hell with you".
Afusace ta juya zata bar gurin tagan shi Tsaye bakin kofar shigowa, kusan minti daya yayi tsaye ganin ta tsaye gaban Hotonsa, baisan wace ce ba, yadai tsaya jiran ta juyo.
Harga Allah ta tsorata da ganinsa, ihu yarage batayi ba ta maze ta tsayaa mayar mai da mugun kallon dayake wurgo mata.
Magana zai yi Hajiya ta fito daga daki tanai kiran Ummi, "naam Hajiya" Salma ta amsa aladabce, ganin Mujahid yasata daure fuska tace "kai kuma daga ina ?
Sosa keya yayi ya gaidata, tabe baki tayi
Da sauri Salma ta risina tace "yaya ina wuni, sannu da zuwa" fuskar ta daure da fara'a..
Kallon mamaki yabita dashi..
Hajiya tace "bada kai take ba, mugun banxa, Allah yasa dai zuciyarta a tsarkake take shiyasa bata nufeka da shairi ba upon all abun dakai mata, idan baka sani ba toh yar'uwarka ce"
Ware ido yayi in shock.
Hajiya tacigaba "iskancin banxa au dama baka sani ba ?
"Bansanta ba, yama sunanta ? In serious tone yayi maganar
Kallon Banxa Hajiya tamai sannan ta kalli Salma tace "kiyi hakuri da abunda ya maki, Mujahid sunan sa, daga shi sai jaafar a haife.."
Shuru Salma tayi, ta mugun kuluwa da denying dinta da yayi, sai yanxu ta kara tabbata wa dagangan yaki nuna cewa yasanta tun farkon haduwan su..
Dakyar tace "ba komai hajiya ya wuce" wuce wa tayi daki, hajiya tabita abaya..
Tsaye Mujahid yayi gun hade da daura hannu akai, "yaushe tazo gidan nan ? Ya tambayi kansa..
Tifowa Salma tayi rike da Plate a hannu, ko kallan shi batayi ba ta wuce ta gabansa, fizgo hannuta yayi da karfi, ihu tasoyi yayi sauri rufe mata baki da hannusa yaja ta suka shiga kitchen, can karshe bango ya turata hade da matse ta da jikinsa har suna juwo numfashin Juna, tsuro tayi da ido, fuska ba annuri yace "What are you doing here, evil tramp from hell..
Alamun tamai da bakinta is close, cire hannu yayi daga bakinta, harara takai mai tace "the evil tramp is you, you kept me away from knowing my family and the worst part of the story you try putting me behind bars, why, do you hate me that much ?"
Cikin rashin damuwa da abunda tace yace "datx your story not mine, i need to know uban miya kawo ki gidan nan ? Cikin zare ido yayi maganar.
Dariyar takaici tayi tace "the only reason y am here, its because of your brother, he is such an Angel, so sweet, i cnt wait to be in his arms..".
Murde hannuta yayi, yanai mata mugun kallo da idanuwa sa da suka sauya launi zuwa ja, ko ajikinta saima kokarin gyara gashin kanta daya bazu gefe, hannu ya nunata dashi, "badai karuwan ci ya kawoki cikin gidan nanba, we shall cee about that.."
Tsaki taja ta kalli hannuta dayake rike dashi tace "M.u ka saki hannu karuwa mana, ko ka fara shiga tarko ne.." Cikin salon rainin wayo tayi maganar.
Haushi biyu ne ya kamashi, "wai M.u, amma yarinyar nan ta raina ni, kodan Yaya bamu" aransa yayi magana.
Rai bace yayi wurgi da Hannuta sannan ya juwa zai fita sukayi kicibis da Junaina zata shigo, "yaya yaushe ka dawo" ta fada da murnan ta, ko kallanta baiyi ba yayi gaba abunsa.
Tabe baki tayi, ganin Salma Mak'ale gurin kaman mai shirin kuka, karasawa gurinta tayi tanai kai mata kallon banxa sann tace "bawai kinzo gidan nan ba, better stay away from my boyfriend, Mujahid nawane nikadai, kodayake y am i wasting tym talking to you, very soon zaiyi kicking dinki out of this house cox he hate you so much Big sister" tsaki taja ta juya ta bude fridge tadau drink sannan ta fita tabar Salma daskare tanai kallon ta.
"Oh ma God, little sis you're too good ki falling wa M. U, na shiga uku" ta fada hade da zamewa kasa ta zauna.
Kanta ta daura kan kafafunta tahau yin kuka dani bansan dalili ba.
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.