Complete Hausa Novels

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 7 of 41

Da sauri Faiza tahau raba papers sannan kowa ya fara, hankalinta kwance Salma bata hall din.
Sai 5.30 Salma ta fito daga Auditorium, miss call din shehu tagani, bata damu ba ta karasa gaban hall, jin shuru gabanta ya fadi, tana shiga taga kowa yayi wiri wiri da ido, kafin ta ankara taji Faiza tace "Hey Get out"
Tsaye Salma tayi, tsoro yakamata ana test, Daddy kadai take tunawa zaici ubanta idan yaji labarin batai test ba.
"Kumin waje da ita" Faiza ta fadi ma securities din.
Dakewa Salma tayi hade da watsa mata harara sanan ta fita bakin Hall ta tsaya kaman xatayi kuka.
"Zakisan dawa kike" Faiza ta fadi a aranta hade da dailling numban Mjay, yana gida zaune gaban laptop yana dannawa saidai mintuna kadan yakan tuna haduwarsa da Salma.
Daukan wayan yayi, ta fito waje gaban Salma cikoin yauki da kwarkwasa tace
"Mjay ya jikin ka
"Am alright, ya skull ko kin dawo gida ?
"Ina skull dai, hope dai kasha magani... Ta fadi murya a shagwabe
Salma kam kallonta take aranta tana fadi "zaki gane kuran kine"
"Faiza miya faru .. Mujahid ya tambayeta cikin rashin fahimtar yadda cikin sakon daya ta canza salon maganarta a shagwab'e.
"Ba komai" tace
Katse wayan yayi, kunya ta kamata,
Mugun kallo tama salma sannan tace "okay, i love you tooo, bye" cike rangwada ta koma ajin.
Salma kaman ta hadiyi yawu ta mutu, tunowa tayi da worthless prostitute da Mujahid ya kirata dashi, shine ba kunya yake cewa tsohuwar nan i love you.
Haushi ne ya kuma kamata, afusace tabar gurin ta shiga motar ta taja.. Gurin wasu kawayanta area boys ta nufa, sun jima suna magana daga bisani tabar wajan zuxiyar ta fari tas.
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: *Zuma Sai Da Wuta*

~na~
©ҳaɾaɧ bųkar

21__23

Ana gama Test Faiza ta tattare script din gurin daya, zuciyarta fayau dauke da farin ciki, mota ta shiga ta ajiye su gefe sanna taja, ganin hadarin dake garin kuma magrib ta kusanto ya sanyata wucewa gida ba tare data koma office ba.

Wani Mugun Dariya Salma ta face dashi ayayinta take kokari kunna motar ta dake parke gefen titi, kunnawa tayi taja ta at 360 tanai bin motar Faiza abaya, can kuma tafara slowing down kafin daga bisani ta tsaya da motar tana dariya.

Parking Faiza tayi ta fito tanai kallon samari hudu rike da Adda dasuma kallon ta suke fuske babu annuri, da ganin su yan tasha ne.
"Lafiya ?
Ta fada cikin karfin hali nuna rashin tsoho.
Basu tanka taba saima dayan su dayace bude motar duk abunda kuka gani ku kwasa, kaman jira suke suka bude kofar test script din suka dauka hade da handbag dinta dake ciki, budewa sukai babu komai sai gayyar pen da kayan shafa.
Hankalinta ne yatashi tace "dan Allah kuyi hakuri, banda ko sisi takardun nan kuma ba nawa bane".
Dariya sukayi.
"ba matsala, wanan takardar ai kudi ci, muna bawa mai kosai zata siyosu naira hamsi"
Kaman tayi kuka take kallon su, test din da taci buri shine zasu saida hamsin, bata gama tsorata ba taga sun soka kusa a tire motar ta, dariya sosai suka kwashe dashi sannan suka hau mashi dinsu suka bar gurin.

Salma kam baki har kunne dan dariya, kallon Faiza take yadda gaba daya ta susuce, next plan dinta tayi shirin yi, tayar da motan zatayi ta lura faiza na waya bayan ta gaba kuma ta shiga motar ta zauna hade da tagumi.
"Bari muka wa take jira" Salma ta fada, gyara zama tayi hade da saka earpiece akunne saurara waka.
Mujahid ta kira awayan, baafi 20 minit ba ya karaso gurin, fitowa yayi ya doshi motar ta, tana ganin shi ta fashe da kuka hade da fitowa daga motan.
"Hoo dama shi takira" acewar Salam daga inda take masu eye service, wani irin haushi ne ya mamayeta, kunne motar tayi ta kara gaba daidai inda Mujahid yayi parking sannan ta fito hade da daure fuska.
Faiza kam kokari fadimai abunda ya faru take sukaga Salma gaban su.
"Malama lafiya kike kuka da girman ki"
Dakatar da kukan Faiza tayi ta nunata da yatsa,
"I knew it, kece kikai planing duk abunda ya faru"
Kallon rashin fahimta Salma tayi.
"mai kuma nayi, miya faru ?
Tambaya ta kike, Faiza ta fada hannu dakai hannu zata kwashe ta da mari, Sauri rike hannunta gam tayi, tace "karki kuskara hannuki ya tabani, kuma ki daina accusing dina da abunda ban yiba"
Fize hannuta faiza tayi ta juya yima Mujahid bayanin abunda ya faru tun a makaranta, shikam mujahid bai gane komai ba banda area boys da Salma ta turo, mamaki sosai yake banda bakin halin Salma ashe har yan daba ma harka take dasu.
Suna cikin haka aka fara ruwa, lallaba faiza yayi bayan ya ciro mukulin motarsa ya bata ta yace taje gida zai biyo mata da nata, bataso hakan ba, ba yadda ta iya ta shiga motar cikin rawar darin ruwan daya bugeta, Salma kam tun lokacin da Mujahid ya ciro mukullin motansa ID card dinsa ya fadi ba tare daya lura ba, hannu Salma tasa ta dauka sannan ta arce cikin motar ta, ko kara kallon su batai ba taja motarta tayi gaba.
Mechanic ya kira ya gyara motan sannan ya shiga yaja xuwa gidan su faiza maida motar, nan ya iske zazzabi mai karfin gaske ya diran mata, saida ya siyo mata magani tasha sannan ya dauki tasa motar, Umma sai godiya take tanai shimai albarka.

*****

Washe gari da Mujahid yayi shirin fita aiki, ba inda bai bincika neman Id dinsa ba, atunanin sa a office ya bari, yana zuwa bai gani ba, zama yayi ya fara aikin gabansa.
Karfe sha d'aya na safe Salma ta tashi daga baccin data koma tun bayan da sukayi karin kumallon, wanka tayi tasa blue jean da white long sleve shirt sanna ta zauna latsar wayarta, bata da niyyah fita kasancewar basu da lec aranar, ID din Mujahid ne ya fadowa mata arai, da azama ta mike tadau jarkarta ta zazzage abunda ke ciki tasa hannu tadau ID din, murmushi tayi ta zauna karanta abubuwa dake rubuce akai,, nambar wayarsa dake jiki ta cofe a wayarta sannan tayi Dailing.
Shikam ya dukufa sosai da aiki gabansa, yana jin ruri wayarsa ya danna hade da sata a speaker yaci gaba da aikinsa,
Dariya tayi tace
"Mujahid Abdulsalam Right ?
Wani iri yaji yadda ta ambaci full name nasa, bai d'ago murya ba saidai zaiso sanin wace ishashiya ce.
"Who are you ? Ya tambayeta.
Tace
"don't worry yanzu zaka ganni, ina da Address din wia you work"
Tsaki yaja had'e da kashe wayan sa, atunanin sa Yahoo girls ne dakeson cin kudinsa, cigaba yayi da aiki gabansa.
Dariya Salma tayi tanai kallon inda marital status dinsa ya nuna single, tabe baki tayi tace ashe ma faizar ba matar sa bace take ta rawan kai akanshi"
Mikewa tayi ta zura Bakar abaya tayi rolling kanta da veil sannan tayi light makeup ta fito, dakin Mom ta nufa ta mata karya zuwa skull sanan ta fito da sauri ta fada motar ta.
Aikinsa kawai yake yama mance da kiranta, yaga ta turo mai text
"Kazo ka shigar dani kafin securities dinnan su gama tattab'ani"
Dariya ma ta bashi, bari dai yaga ikon Allah, wani police ya kira yace yaje ya shigo da ita.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.