Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 38 of 41
Gida Mujahid ya nufa duk jiki amace, tunanin yake da amincewar ta tabar gidan tabi salim ko kuwa dai sacen ta yayi dagaske. Dafe kai yayi cike da tashin hankali kwata kwata yarasa ta yadda zai bullowa lamarin, wayarsa Da mubarak sunyi dashi cewa karya damu gobe zai baza yan sanda a gari neman duk inda take, for now ya ya bari ayi daurin auren ba tare da tashin hankali, dan kuwa muddin hajiya taji labarin abunda ake ciki saidai kuwa afasa auran. Da wannan shawarar Mujahid yadan samu nutsuwa kadan.
***
Washe gari Mom bata nunawa kowa abunda ake ciki ba, yaken dole kawai take ana buduri, ita duk atunanin ta ba bata Salma tayi ba aganinta su Hajiya suka dauketa dan su nuna mata iyakar ta, babu abunda tace da Daddy har aka daura auren su kowanne abisa sadaqi dubu hamsin, bayan Daddy ya dawo ne yace da ita tama su Hajiya waya yakamata ace Salma ta dawo, yafiso ya mikata gidan miji dakansa. Toh kawai Mom tace dashi saida taga yabar gurin tadau wayar Salma kiran nambar Mujahid.
Gidan Mubarak su Mujahid dasu Abdul suka nufa bayan an daura aure, ko wanne su sanye da tsadadsiyar shadda sunyi kyau barin ma Mujahid dayafi su kyau da kwarjini, da ganin fuskokin su babu walwala tattare da ita saidai ango duk yafi shiga kidima ganin tun safe samun inda Salma take yaci tura kasancewar yan sanda kusan ashiri da aka baza nemanta basu ganta ba.
Nisawa Mubarak yayi yace "Mjay kasan abunda zamuyi ?"
Kallonsa yayi ido yajir, Mubarak yacigaba "kawo namban ta muyi tracing Gps device din ta dan sanin exact location nata"
Tsaki Mujahid yaja yace "wannan idea din is of no use, wayarta na gida gurin momcy dinta, nifa am sure dan Iskan nan yasan inda take y not kayi kama shi kayi torturing dinshi tunda ni am out of the force"
Dariya Mubarak yayi.
"Taya zan kama Salim without concrete evidence, you're crazy sai kace nina aikeka ka kwafsa"
Abdul ne yace "anyi mai wuyan ai, auran"
Harara Mujahid yakai ma, aranshi yana fadin ina dadi babu matan.
Mubarak yace "kaga there is nothing i can do, addua zamuyi Allah ya bayyana ta, kuma dole su Hajiya susan abunda ke faruwa"
Magana Mujahid zaiyi wayarsa tahau ruri, dubawa yayi yaga namban salma, da azama ya dauka, Muryar Mom yaji tace "ina fatan dai ka fito da ita aduk inda kuka boyeta ?
Ruwan ne ya cinyesa, kasa magana yayi sai kuka daya fashe dashi, haushi ne ya kamata ta katse wayan.
Kallon yayi cike da tausayin kasan, Azabure kuma ya mike daga inda yake zaune ya kalli Mubarak yace "na tuna akwai agogona na office gurinta saidai bazan iya accessing gps din device dinba saboda password dinsa na office is blocked, i need your password da tab dinka"
Mamakine ya kama Mubarak, ya zaai yabata agogon shi na office wanda manyan maaikata kadai ke da acces dashi, kuma ma ai yakamata ace yayi submitting agogon tun randa Sir Ahmed ya bashi suspension, kodayake yanxu agogon zai iya amfani indai tana tare dashi, tsaki Mubarak yaja yace kai banza ne wlh, mikewa yayi yadauki tab dinsa dake kan table sannan ya mika mai yana kaimai harara, su Abdul kam dariya abun ya basu.
Lekowa haraban Gidan Salim yayi, saida ya tabbatar babu kowa sannan yaja akwatin sa ya fito waje, bakin mota ya tsaya ya karewa gidan kallon karshe, sannan ya bude boot yasa akwatin ya zagaya yazauna cikin motar, tagumi yayi yahau tuna yadda Daddy ya taimake sa lokacin da bashi da kowa yq dauko shi daga tsumma ya kawo sa gidan tun yana karami harya girma ya zama wani abun, Saidai soyayya Salma ta ruguzamai rayuwa kuma baiga zai iya hakura da ita ba. Hawayene ya zubo mai cike da tausayin kansa, atake yaji wani irin ciwon kai ya tsiga reshi, da sauri yasa hannu cikin aljihun rigarsa ya ciro wasu jajayan kwayoyi kusan kuda takwas ya afka abaki hade da hadiye su, wani irin buguwa yaji cikin kwakwalwaraa sannan kuma alokaci guda yaji sa ya dawo normal, Ajiyar zuciya ya sauke ya kunna motar ya fice daga gidan.
****
Wani dattijo mai kimanin shekaru hamsi da hudu ne zaune cikin motar sa dake fake bakin gate din gidan Hajiya, yafi minti talatin zaune yana saka da warwaran yadda zai shiga gidan, idan bai manta ba last haduwan su da Hajiya kusan shekaru goma da suka wuce, rannar da suko gidanshi a gombe ya masu rashin mutunci akan karsu kara zuwan mai gida yanzu kuwa gashi ya dawo cikin hayyacin sa yaran kawai yake son gani ya nemi gafarar su, musamman Salma daya yayi mugun bakan ta mata. Kukan nadama ne ya kufce masa, saida yayi mai isar sa sannan ya fito ya tunkari gate din gidan, gaisawa sukayi da Mai gadi sannan yace mai yamai iso gurin Hajiya, maigadi kam ganin mutumin yamai yanayi da yaran gidan yasa shi cemai ya shigo ciki bara yaje ya kira mai Hajiya.
Hajiya kuwa sai hidima take da bakin da suka zo daurin aure, su Aunty Bilki na daki tare da Junaina da wasu yan uwa suna ta zolayar ta, ita kuwa sai wani kuka da langwabewar shagwaba take, Annah ce ta leko dakin jiki ba laka, ganin Hajiya bata ciki yasa ta komo palo ne manta, jamaa sai janta suke ta hira batako kalle su ba,
Bata ganta ba, daga can kitchen ta jiyo muryar ta, da azama ta shiga kitchen taja ta suka fito waje inda babu jama'a.
"Annah lafiya kuwa ? Hajiya ta fadi tanai mata kallon tababbiya, ta lura jiya zuwa yau Annah bata cikin wani walwala.
Kuka Annah ta fashe dashi tana fadi mata karyan aikan Salma da tayi da kuma sanarwa mujajid gaskia da tayi, Salati Hajiya tayi cike da tashin hankali, right under her nose abubuwa sun faru bata da labari, wayarta da hannuta tahau kiran Mujahid dashi, shuru no amsa. Hakalinta ne ya kuma tashi, bata sanda tahau Annah da masifa ba tsabar takaici, Annah kam kuka take tana fadin "wlh duk laifi nane, kila ma yan yanke suka kamata, ashaa tama mutu kila"
Ran hajiya ne ya kuma bashi, magana zatayi taga mai gadi ya kusanta gurun su, da sauri ta karasa garesa tana tambayar sa ko yaga Mujahid, shikam bai amsa tambayar taba yace "Hajiya kinyi bako, wai Alhaji babangida daga Gombe ?
Ras gabanta ya fadi, Annah ta gane waye hakan, kallon Hajiya tayi baki wangale.
Daskarewa sukayi gurin ba tare dasun san ya karaso gurin ba, sai jin muryar sukayi cikin Sallama, atsorace suka kai dubansa garesa nan take annurin fuskan Hajiya ya dauke.
"Babangida ina fatan dai ba daurin aure kazo ba, dan tuni madaurin auren uban yaranka ya daura"
Jikin sane yayi sanyi, baiyi mamaki ba tunda yasan yammatan sunkai aure, kuka ne yazo mai ya tsuguna baiwa Hajiya hakuri, bata sauraresa ba ta juya zata koma suka ji muryar Junaina ta fito da gudu tana kiran Hajiya, da gudu ta karasa gurin cikin haki tana fadin "hajiya kinji su Aunty biliki wai dole sai anmin kitso kanana nikuma bana so" karshe maganar tayi tanai bin ko wannen su da kallo ganin bama fahimtar abunda take fadi sukayi ba.
"Yar auta ta haka kika girma" babangida ya fada yana kallonta, kallon shi tayi kaman taso gane shi a hoto, Annah ce ta katse mata kallon da cewa "ke Abban kune"
"Abban mu" junai ta fada cike da murna, ita kan burinta bai wuce taga Abban taba, da sauri taje ta rungume shi cike da farin ciki, kuka sosai Abban su yafashi dashi, Shuru Hajiya tayi tana kallon su idonta cike da hawaye tunanin ina Salma ta shiga take aranta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.