Complete Hausa Novels

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 32 of 41

Fuskar Mujahid daure babu annuri, tuki kawai yake har suka karaso babban titin, tsayar da motan yayi sannan ya kalli Junaina da tayi kicin kicin da fuska yace "zaki sauka ko saina bakin wawan mari "
Bude motar tayi ta fito tace "aiko baka fad'aba bazan bika ba, mugu kawai" rufe murfin kofar tayi da karfin gaske ayayinda shi kuma yake dariya, ba karamin dariya taba shi ba.

Motar Jafar nabiye dashi abaya, ganin ya tsaya shima ya tsaya, kallon Salma yayi yace "i guess ke yake jira"
Murmushi tayi, tana shirin bude kofar Junaina tabude afusace tace "malama saiki sauko mai guri tazo, sannan kuma awa biyu nabaki kidawo muyi exchange, kinsan Annah ba wasa, ban yadda tamin duka abanza"
Salma batace komai ba ta sauka, shiga motar Junaina tayi tana jan tsaki, bata rai Jafar yayi yace "idan kika sake tsaki zan ajiyeki nan nakoma gida kuma learn to respect your sister"
Okay, am sorry" Junai tafadi amaraice.

Motar Mujahid Salma ta shiga ta zauna, gani tayi sai fama murmusa wa yake, itama murmushin tayi cikin sanyi voice tace "yaya whatx d good news?
Wani sexy look yakai mata, murya kasa kasa yace "muje miyu shopping daga nan sai muje mu gaishe da Aunty dinki, kwana biyu tana missing dina"
Kallon rashin fahimta tamai sannan tace "wace haka... ?
Bai kalleta ba yaja motar yace "Malamar ki mana, Faiza.."
Gabanta ne ya fada, murmushin da take dauke dashi ya koma bacin rai, "faiza" ta fadi aranta
"Faiza dai, ko kin manta ta ? Ya fada jin ta kira sunan afili batare data sani ba.
Shuru tayi bata iya cemai kala ba, tunani tahau yi anya batayi kuskuren fadawa tarkon Mujahid ba, shida baya da lafiya ina ruwanshi da wata Faiza, kila ma shopping din ita zaai wa...surutai barkatai tahauyi azuciyanta.....
[9/7, 12:38 AM] Xarah Bukar: ​Zuma Sai Da Wuta

~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Allahu akbar kulu'nafsi za'ikatu mauti, Allah yaji kanki da rahma Maman besty Yar ficika. May jannatul Firdausi be ur final destination.

*Wannan shafin naki ne ke daya Princess Sakhna (yar Gatan xarah bukar) thanx so much 4 ur love & support, Allah ya barmu tare, ILYSM*❤❤❤

ZSDW fans😘

60

Murmushin dole Salma tahau k'irk'iri kar ya gano wani abun dake zuciyar ta. Haka suka isa Sahad stores, abubuwan amfani masu kyau da tsada ya loda cikin lodoji sannan suka fito, ita dai Salma bata cemai k'ala ba suka zo shiga mota ta mak'e abakin kofar batare da niyyan shiga ba, alama yayi mata data shigo su tafi ta make kafada had'e da shagwab'e fuska, dariya ta bashi, ya zago gurinta had'e da bud'e mata k'ofar, k'in shiga tayi tace "nifa gida zan koma, bazan rakaka gurin taba" murya raunane tayi maganar.
Hannu ta ya riko, muryar kasa kasa yace "haba habibty malamar kice fah, ina laifin wanda ya karantar ka"
Turo baki tayi.
"ni ba abunda ta koyamin, mostly korata take a class, dan haka bazan je gidansu ta wulakantani ba"
"Toh ya kike so ayi yanzu, already na kirata awaya ina tafe.
Dadi ne yakama Salma jin sai yadda tace, daure fuska tayi tamau tace "muje gidan amma a bakin gate zaku gaisa mu wuce"
Dariya yayi, ta shiga motar sannan ya zagaya ya shiga yaja zuwa gidan su Faiza. Awaya ya k'irata, ta fito ta iske shi waje, daganin Salma ta had'e rai, dukda ma Mujahid ya fad'imata Salma yar'uwa sa ce bai hanata jin haushin taba balle inta tuna yan daba dana aiko mata, ko kallon juna basu yiba ta k'arasa gefen da Mujahid ke zaune, sai wani yauki take mai tana mitar kwana biyu ya shareta, shikam lallaba ta yahau yi harta d'an hak'ura suka fara yar wasa da dariya, Iya k'uluwa Salma takai, wayarta sai ringing take takasa dauka tsabar takaici, sakon ne ya shigo nacewa "muna jiranku abakin gate" nanta gane Junaina ce, Gyaran Murya tayi had'e da kawar dakai gefe.
Kallon ta Mujahid yayi sannan ya maida dubansa ga Faiza yace "frndy ya samari, ko kuma dai nace ya bazawarai ?.
Annuri fuskar tace ta sauya, tahau wasa da yatsun hannuta, tace "tukun nadai"
Murmushi yayi ya d'auki ledar shopping din ya mika mata, yana fadin "gashi ama mai rabo kwalliya" cikin zolaya yayi maganar.
Harara tamai cikin wasa sannan ta amsa tace "niba wanda zanma kwalliya"
Magana zaiyi, Salma ta katse shi dacewa "yaya muje kunnena na ciwo"
Wani mugun kallo Faiza ta jefe ta dashi ganin yadda yayi saurin bata attention, ciki ciki tayi godiya ta wuce batare data jira abunda zaice ba. Idanuwan sa nakan Salma yanai mata sannu dukda ma dai yasan karya take, juyawan dazai yi yaga bata gurin, kallon tuhuma yama Salma sannan yaja motar sukayi gida.
Bakin gate suka had'e dasu Junaina nan sukayi canze, Jafar da Salma suka shige agidan atare, shi dariya ma abun ke bashi, Mujahid kam ko ajikinsa kota kan Junai bai biba suka shige gida, daganin su Annah tahau washe baki, aganinta sun daidaita kansu tunda taga sun jima da fita, albarka tahau shi masu tanai jinjina nutsuwa da hankalin Salma ganin yadda komai tace ayi Salma na mata biyyayya.

*****
Kwanaki sun ja, Soyyaya sosai Mujahid da Salma keyi babu wani ruwanshi da sa Idon Annah dukda ma dai Salma na kokarin kare kanta gurinta na nuna cewa ba ruwanta dashi, hakan kuwa ba karamin Dadi yama Annah ba aganinta dagaske Salma take, sau tarin yawa tafi bawa Junaina laifi akan bata kula Mujahid, ba kunya Junai kece mata ba sonshi take ba, dukda hakan Annah taki hakura ita adole zabinta kowa zaibi dan ta lura ma Jafar baya bi takan Salma, indai yana gida ta tare zata ganshi da Junaina, hakan na mugun b'ata mata rai.
Hajiya ma shuru bata dawo ba, akullum Annah saita kira tai mata albishirin yara sun daidaita kansu, da kuma yaushe zata dawo afara shirin buki, Hajiya dai jinta take tasan ba hakan bane, iya kaci tace mata ta kusa zuwa bada jimawa ba.

****
Gidan shuru kowa kwance dakinsa kasancewar ruwan da ake tafkawa tun bayan Magrib. Sanyi ne kadai ke ratsa ko ina, lamo Salma tayi cikin bargo tana lumshe idanu, hannu takai karkashin pilo tadauki wayarta ta duba lokaci, karfe goma da kwata na dare tagani . Murmushi tayi ta yunkuro zaune hade da dialing nambar Mom, sau biyu tayi ringing Mom ta dauka, idanta biyu, alokaci tana shirin shiga dakin Daddy, tana ganin call din Salma tasan bai wuce zancen Mujahid ba wanda akullum sukayi waya saita mata zancen sa, ta rasa wana irin so Salma kema mugun yaron nan.
Gaisawa sukayi cike da fara'a, sannan Salma ta gangaro mata dacewa "Mom kin sanar da Daddy kuwa ?
Dariya Mom tayi.
"Yar gatan daddy kinsan duk abunda kikeso hakan zaai, amma are you sure he is the right man for you, nifah i dont like him"
Nisawa Salma tayi, kaman mai shirin kuka tace "haba Mom, wlh ya Mujahid nasona, bashi da matsala, trust me"
Mom tace "okay dear, dama Daddy yace na tambayeki tunda kinyi insisting sai shi, babu damuwa, your happiness is ours"
Farin ciki ne sosai yakamata Salma, sun jima suna hira daga bisani sukayi Sallama, sai sannan taga Miss call din Mujahid hudu ya kirata kusan mintin arba'in da suka wuce.
Da azama tayi dialing no dinsa ta jita akashe, mikewa tayi da sauri tana tunanin kilan wani abun yakeso takaimai ko kuma wani mugun abune yasame shi, cike da Fargaba ta fito daga dakin, jikinta sanye da sliky night wear riga da dogon wando ko dankwali babu kanta tayi saurin haurawa stairs, bata ma lura da Annah dake tsaye bakin kofar dakin Junaina ba. Mamakin ganin haurawan ta sama Annah tayi, kullum dare takan fito dan tabbatar da Yammatan kowanne na dakinta sabod tsaro da kuma tarbiyan su, basu kadai ne agidan ba, shiyasa duk inda kake da yaran mata da baligi namiji a gida yazama dole kasanyan idanu saboda gudun shairin sheden dazai afko.
K'wafa Annah tayi ta juya dakinta dauko sandar ta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.