Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 17 of 41
Shuru ne ya ratsa tsakanin su har taxi ya iso gidan su.
Kallon shi tayi, gabadaya baya cikin hankalinsa, tabosa tayi, adan firgice ya kalleta, murmushi tayi tace "kana da abun dariya, kodai dukan yafara tab'a kane.."
Murmushin k'asaita yayi, irin wanda yake fizgar zuciyar wanda aka yiwa.
Yace
"Kije ki huta, i'll call you later"
Okay, bye ta fada ta fice a mota.
Gobe Birthday na 👯👯👯👯👯👯💃ðŸ¿
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: : Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkar
41- 43
Gidan su fa'iza ya wuce amsan motarsa. Isketa ta yayi tsaye haraban gidan jingine bisa motar. Da ganin sa tahau cika da batsewa, cikin koya kula da yanayin ta yace tabashin mukullin. Kaman zatayi kuka tace "Mjay miyasa zaka min haka gaban yarinyar nan, shikenan ta gama raina ni yanzu gani zatayi daidai nake da ita tunda kana kulata"
Kallon takaici yayi mata.
"Keda ita ba d'aya bane, you're my friend ita kuma she is nothing.."
Cikin rashin gamsuwa da kalamansa ta tab'e.
"ban yadda ba saboda dazu kallon da kake mata baiyi kama da babu komai ba, kuma na tabbata ka fara sonta"
Murmushi gefen baki ya saki wanda shi kadau yasan manufarsa, yace "tabbas na kamu da sonta saidai son da nake mata baikai na kasance tare da ita ba, kin dauka zan barta taci bulus ne bayan tamin rashin mutunci "
Nisawa Faiza tayi, aranta batai na"am da koma mai yake niyyan yiba, tunda har ya furta yana sonta ba lailai ne ya rama abunda zaiyi ba
"What are you planning ?
Girziga kai yayi yace "i dont know yet, ina dai tunani gagarinmin abunda zanyi na koya mata hankali, so nake tayi kuka da idanta"
"Daganan kuma saika rabu da ita kenan ? Faiza ta fadi.
Tsaki yaja
"Kinga enough of your questions, you're just a friend banaso ki wuce limit dinki" ya fada, amshe mukulli hannuta yayi ya fada motar yaja ya barta nan tsaye baki sake cike da takaici.
Salma na shiga Gida daki ta wuce ta kwanta, zuciyar ta fal da farin ciki, tunanin Mujahid take tana tuna farkon haduwa su izuwa yau, kwata kwata takasa gane kanta, shin sonshi take komi, kullum dashi take kwana ta tashi, girgiza kai tayi, sam babu lissafi soyayya aranta, bata tab'a yi ba saidai na baya data gani sun wahalu daga karshe ma tsana ce ta biyo baya shiyasa take bala'in tsoron fadawa soyayyar wani. Tana son Mujahid amma bazata nuna mai komai ba ayanxu har saida tabbatar he won't break her heart.
****
Tun daga ranar lamari ya canza tsakanin su, soyayya da kulawa sosai Mujahid yake nunawa Salma saida bai fito yace yana sonta ba, har ilah yau bai kuma canza kudurin sa na koya mata hankali ba, ta bangaran Salma kuwa zuciya daya take zaune dashi takan yi mamaki sai kace ba kwanakin baya suke casa juna ba, aranta takanyi tunanin anya kuwa Mujahid baida wani mugun nufin akanta, saurin kawar da tunanin take saboda tsananin yadda yake damuwa da lamarinta.
Daddyn Salma ne tare da Ja'afar a office dinsa. ja'afar yana daya daga cikin lauyoyi da Alhaji Abbas ya aminta saboda tsananin rike gaskia da Tsoron Allah da yake azuciyarsa, sau tari yawan idan zaiyi harkar canji da dollars ko euro yafi yadda da damk'awa jaafar takardun shaidan komai dan yasan bazai cucu saba.
Zaune suka suna magana akan wani fili daya siya a Kaduna, copy na takardu shaida da komai ya mikewa Jaafar, karba yayi yana dubansu
Daddy yace "ka adana su da sauran"
Hade takardun jaafar yayi cikin briefcase nasa sannan ya mike da niyan yimai sallama, dakatar dashi Daddy yayi hade da cewa "ya maganar mu ta kwanaki, naji shuru baka kara waiwayar zancen ba.."
Zama jaafar yayi had'e da kirkiro murmushi dole, shikam yama manta da zancen, shuru yayi yana tunanin zancen da neman amsar bawa Daddy, bazai yaudari zuciyan saba dan kuwa yana son Junaina, saidai kuma ba damuwa tayi dashi ba ga kuma Daddy da yakeson ya hada shi da Diyar shi dako sanin ta bai yiba balle ma yasota, shi kuma auran bayama cikin lissafinsa yanzu kokarin Nemo Ummi kawai yake dan farin cikin hajiyarsu kuma baima isa ya tunkareta da sunan yana son aure ba, ana takai wa yake ta kaya.
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhaji wani hazari ba gudu ba, maizai hana mu hadu da diyar taka, idan ta amicin dani saina yadda karya zamana ko tana da wanda takeso"
Farin ciki sosai ya lulube Daddy, kasancewar ta bangaran Salma ba matsala koda batason Jaafar yasan zata mai biyayyah, kuma ma baiyi tunanin Salma nada wani da takeso ba.
yace "ba matsala, gobe kazo gidana mu kara tattaunawa saika ganta
Yake jaafar yayi aranshi yace "Allah yasa karta aminci, afili yace "saidai yau nazo, saboda gobe da safe ina da aiki a Kaduna"
"ba damuwa, Allah ya kaimu zuwa dare" acewar Daddy.
Godiya yama Daddy sannan sukai sallama ya fice azama.
Tun ranar da Hajiya ta kira Mujahid tace yazo gida bai samu daman zuwa ba sai rana ta yau acewarsa aiki yamai yawa bacin kuma da gangan yaki zuwa.
Fuska ba yabo ba fallasa Hajiya ta tarbeshi, nan tahau mai fadan barin sa gida akan abunda baikai ya kawo ba, Mujahid kam shuru yayi yana sauraran ta dan ya kagara ta gama ya wuce aikinsa, tace "Bani hotunan Ummi dana baka kwanakin baya"
Sosa keya yayi alamun marar gaskia yace "mi zaai dasu, an ganta ne ?
Hajiya tace " baa ganta ba, kawai hoton zaka bani tunda ba nemo ta zakayi ba, tuni Jaafar ya dukufa da nemo ta kuma am sure zai samota aduk inda take"
Ware ido Mujahid yayi adan kidime yace "jaafar zaki bawa hoton ?
Mugun kallo takai mai, tace "ko babu hoto Jaafar yasan fuskan ta, kaida ba saninta kayiba yasa na baka hoton"
Gabansa ne ya fadi, fatan shi Allah yasa kar Jaafar ya hadu da Salma, nisawa yayi yace "Hajiya basai jaafar ya nemo taba, nida kaina zan kawota gidan nan very soon."
"Ka ganta ne" Acewar ta.
Kai ya girgiza alamun a'a, aranshi yace "ki bani time very soon zaki ganta amma saina koya mata hankali yadda idan ta shigo gidannan bazata yadda ki had'ata aure da niba".
Tashi yayi ya mata sallman zai wuce office ya fice waje, nan suka hadu da Junaina ta dawo daga gidan wata kawarta dan tuni sun gama Neco.
"Yaya kyan tafiya dawowa" ta fada tana dariya.
Tabe baki yayi yace, "ce maki akayi nadawo"
"Oh Allah, he will never change, ni ina can ina missing dinshi amma koya kula dani" aranta tayi maganar, Afili tace "yaya akwai abunda nakeso kasani, sumtin is going on in this house"
Kallon gefe yayi babu mai dubansu sannan ya jata gefe danjin wana abu ke faruwa, sau tari dama ita ke kaima rohoton abubuwan dake faruwa agidan dan ba zama yake ba.
Murya kasa kasa tace "bansan full story dinba, naji dai Hajiya na Waya da Aunty Bilkisu akan wani abu, i dunno ko kudi ne ko gida ko kuma ince sumtin is missing i dont really know, naji Hajiya tace tunda kai kaki nemo wa idan ya jaafar ya nemo shi zata
bawa ta fasa baka"
Hankalin sane ya tashi danya gane inda Zancen ya dosa, saidai bazai bari Jaafar yaga Salma ba much less ya yadda da auran suba.
Dakewa yayi yace "little sis kinsan mi zakimin"
Kur tayi tana kallon shi, yace "inaso ki sawa Jaafar ido, idan kinji yana waya akan wata mace ko bincike ki bani feedback kinji"
Kai ta girgiza alamun toh, murmushi ya sakar mata. "yauwa my beautiful sister, you know i like you alot"
Dariya tayi tace "nidai yaya kadawo gida plz, wlh i missed you alot".
"Karki damu nakusa dawowa"
Dadi sosai taji, sun jima yana biyeta sai shagwaba take zuba mai daga bisani ya lallab'a ta ta tafi ya koma motarsa yaja yabar gidan.
Tuki yake yana neman mafitan yadda Jaafar bazai hadu da Salma ba, idan yayi sake kuwa yanaji yana gani zaiga Salma a gidansu, dabara ce ta fadowa mai yadau waya hade da dailing no din Salma.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.