Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 33 of 41
Ahankali Salma ta tura k'ofar dakin ta shiga, can ta hango sa dunk'ule tsakiyar gadon kud'undine cikin bargo kansa kadai ke waje yana baccin sa hankalin kwance, ga wata sanyayyiyar kamshi dake tashi ta kowana lungu da tsakon d'akin. Karasawa tayi gefe gadon sannan ta kira Sunan sa ahankali, shuru bai amsa mata ba, tsoro ne yakamata kodai baya da lafia, rarrafawa tayi har tsakiyan gadon ta tsugunna daidai fuskar sa, hannu takai bisa goshinsa taji temperature dinsa is normal, ajiyar zuciya ta sauke ta zubawa kyakyawan fuskar sa idanu, murmushi tayi zata juya taji ya riko hannuta tafado jikinsa, cike da kid'ima ta kallesa, gani tayi idanuwan sa bude yana mai mata wani irin kallo mai fizgar zuciyar wanda ake ma, Saurin d'ago da jikinta tayi, suna kallon juna..
Ganin tayi ya mika hannunsa zai taba jikinta tayi saurin rintse idanu, murmushi marar sauti ya saki, yasa hannu ya gawar da gashin kanta gefe daya zubo ya rufe rabin fuskar ta.
"Kin dauka na mutu ne ?
Ya fada cikin salon da bata taba ji garesa ba.
Bude ido tayi ta dubesa, murya shagwabe tace "naga miss call dinka"
Marairace fuska yayi yace "sanyi nakeji, i need your body to warm me up" karashe maganar yayi ya kuma janyo ta jikinsa.
Mintsini takai mai, tace "are you crazy ? Cikin salon wasa ta fad'i.
Dariya yayi yace "am crazy about you"
Chakwulkuli yahau yi mata, tahau rokonsa ya bari, wani mugun dariya ke cinta, kasa jure wa tayi tadau karamin pilo tanai kaimai duka cikin salon kauna, tace "plz stop it..
Ganin ba bari xaiyi ba tahau kokarin sauka kan gadon da ya hargitse gaba daya, kowannan su dariya yake suka ji an bango kofar dakin da karfin gaske, atare sukayi surrender cike da tsoro.
Tsaye Annah tayi ranta na mugun tafasa da bacin rai, mugun kallon tama Salma tace "Miye hakan, nonuwa awaje, gashi a hargitse ?
Saurin karasa saukowa Salma tayi cike da kunya, adjusting hannun rigarta data zabulo kasa tahau yi.
Tsaki Mujahid yaja yace "waike Annah sa idon naki har dare ma kasuwa take ci"
Haushi ya kuma kamata, Salma kam tsuru tsuru tayi.
Annah tace "zakaci uwar kane, yarinyar mutane ka matse a daki, wayasan ma mikai mata, kaga yarinya shuru shuru".
Dariyar rainin wayo yayi yace "ki tambayeta idan nina ce tazo"
Kallon ta Annah tayi tana jiran amsa, Salma kam ihu yarage bata yiba dan kunya, kuma abun haushi ma ita takawo kanta....bata ankara ba taji saukar Sandar Annah a ajikinta, kara marar sauri ta saki zabar azaba, da sauri Mujahid ya sauko kan gado ya amshe Sandar yaja Salma gefe, yace "Allah kuwa kika kara dukanta awaje zaki kwana".
Tafi Annah tayi tace "ubanka ma yayi kadan" nuna Salma tayi da hannu tace "keda nake yabonki Sallah ashe ko alwalar ma baki iya ba, nasan maganin ku, kafin ku b'arko abun kunya kwara na aurar daku cikin satin nan yan banza yaran kawai" warce Sandar tayi hannusa ta juya tafita.
Adan kidime ya kalli Salma yace "hope bata ji maki ciwo ba.?
Kai ta girgiza alamun a'a, sai kuma tace "yaya sandar akwai zafi ashe" kaman tayi kuka ta fadi hakan.
Sosai yaji tausayinta, dan kuwa yasan zafin sandar, zaunar da ita yayi kan gadon yace "am sorry, duk laifi na ne"
Murmushi tayi batace komai ba, sai kallan juna da suke, Annah ce ta kuma dawowa tana fadin "kina fitowa ko saina zo na kara maki ?
Da sauri ta mike, tace "Ya good nyt"
Kaman karta tafi yaji, lumshe ido yayi yace "nyt dear, sleep tight"
Ficewa tayi da azama, yabi bayanta da kallo cike da tsatsan sonta, zuciyar sa sai kara tuna mai yake ya rama abunda tayimai kwanakin baya.
Labb'an sa nakasa ya ciza, sannan yace "i love you so much but dole nayi hurting dinki kema ki dandani azabar danasha" kwanciya yayi kan gandon yana tunanin hope he isn't making any mistake.
Saida Annah ta raka Salma har daki sannan takoma Palo tazauna tana huci, wayarta tadauka ta kira Hajiya, Hajiya kam duk ta tsorata ganin kira alokacin, tana dauka Annah tahau ta da Masifar akan lailai saita dawo gidan Gobe, dan kuwa cikin wani sati take so ayi aure tun kafin yaran Gidan su kasheta da bakin ciki.
Hajiya kam bata gane inda zance yado sa ba, saida Annah tayi mata bayanin abunda ya faru, Salati Hajiya tahau yi, tace bataga ta zama ba dawo wa gida yakamata.
[9/7, 12:38 AM] Xarah Bukar: ​Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION {NWA}
Allahu akbar kulu'nafsi za'ikatu mauti, Allah yaji kanki da rahma Maman besty Yar ficika. May jannatul Firdausi be ur final destination.
61
Har wayewar garin Allah Annah bata bar jinini ba, ganin babu wanda ya tashi bacci a mutanan gidan yasa ta tusa Salma agaba akan lailai saita koma gidan su kafin ta janyo mata abun magana, ita kam dariya ma batun ya bata, had'a kayanta tayi cikin akwati ta fito, har waje bakin mota Annah ta tisa keyarta gaba tana kumfan baki, Salma kam ko ajikinta tafad'a mota Driver yaja maida ta gidansu. Ajiyar zuciya Annah ta sauke ta koma ciki tana magagganun ita d'aya kamar tab'abb'iya..
Salma na isa gida Momy taji dadin ganinta, dan kuwa ta jima da son dawowarta alkunya yasa kawai batai mata batun dawowa ba dan har Daddy taima zancen yace da ita karta manta Salma gidan yan'uwanta taje ba wani gurin ba.
Ta b'angaran Mujahid kuwa koda ya sauko kasa around 12 baiji duriyar Salma ba, sharewa yayi atunaninsa abunda ya faru jiya yahanata fitowa. Around 4 bayan ya dawo Masjid ne ya lura something is not right ganin yadda Annah kemai mugun kallon tana cika tanai batsewa, baibi takan taba ya leka dakin Hajiya, wayam yagani babu salma balle alamunta, ransa ne yabaci, atake ya ciro wayarsa daga aljihu ya kira Salma, dariya tayi dataga call din though she was expecting ya kira ta tun dazu, tana dauka yace kina ina ? Atakaice yayi maganar.
"Gidan mu" ta fada tanai cigaba da dariya, shikam haushi ma tabasa ya katse call din ya fito palo gurin Annah, fuska ba annuri yace "Annah miyasa Salma tabar gudan nan ba tare da izini nabaa ?
Harara ta watsa mai sannan ta d'auke kai tana fadin "Zancen kake so, wai ance da gwauro ya iyali"
Iya k'uluwa Mujahid yakai baima san mai kalamanta suke nufi ba, yace "bar ganin kin koreta kamar kinci galaba akanmu, ni yanzu gidan su zan nufa ganin ta, sai inga abunda kika isa yi" cike da karaji yayi maganar.
Dogon Tsaki Annah taja ta tab'e baki had'e da ware hannuwanta biyu, tace "Abu mai sau'ki, shan koko da matsami, kuje can ku karata badai agidan nan ba, idan kaga kuma ta dawo toh an shafa fatiha ne, jarababbun yaran kawai"
K'wafa Mujahid yayi ya fice waje afusace.
Salma tare da Momy a d'aki suna hirar su cike da annushuwa, Salma tace "Momy nikam ina ya Salim tunda na tafi bai kira niba ??
Tab'e baki Mony tayi tace "these dayx bansan maike damun saba, he is always indoors, dukya rame ba yadda banyi muje yaga Doctor ba yaki acewar sa kalau yake"
Jikin Salma ne yayi sanyi, sosai taji tausayinsa, ada bata da wani aboki sai Salim tanson shi sosai, halinsa kadai yasa take maintaining distance.
Wayarta ce tayi karar shigowar text, dubawa tayi tare da murmusa, kallon Momy tayi tace "sweetheart dina ya iso"
Dundu Momy takai mata tana fadin "marar kunya kawai" dariyar sukayi atare ta mike da azama taje dakin ta tadau veil tayafa akan doguwar rigarta sannan ta fita haraban gidan inda yake tsaye bakin motar sa, fuska murtuke.
Da fara'a ta karasa garesa, gaidasa tayi ya kuma tamke fuska ya dauke kai.
Rud'ewa Salma tayi, sam batason ganin one love dinta ahaka, kaman zatayi kuka ta shagwab'e murya da cewa, "yaya am sorry, wlh Annah ta tisa ni gaba shiyasa banma Sallama ba"
Sai sannan yakalle ta, cike da haushi yace "atleast you could have holla me on phone before leaving, bakiga yadda hankalina ya tashi da rashin ganin kiba"
Hakuri Salma tahau bashi shikam sai wani cin magani yake, dakyar tasamu ta lallaba shi haryayi dariya, hirar su mai cike da so da kauna suka hauyi daga bisani yaduba agogon hannu sa ganin lokaci, duban agogon Salma tayi hade da dariya tace "ya agogon nan yan nan ?
Murmushi yayi ya kalle ta yace "babu inda zaije tunda baki sace shiba"
Dariya ta kumayi tuna haduwar su ta biyu a club data zaremai agogon yabiyo ta ya kwace.
"Wlh i was only looking for your trouble ranar, amma yaya do you still smoke ?
Gyara tsayuwar sa yayi yanai kaimata wani shumin kallo sannan yace "har yanxu kina zuwa Club ?
Harara takai mai cikin salon wasa, bata bashi amsa ba tace "yaya inason agogon nan, ban taba ganin irin saba"
Kallan sliver agogon yayi yace "ba normal agogo bane, but i cnt tell you kona miye"
Ashagwabe tace "yaya kabani plz, inason agogon"
Dariya tabashi da yadda tayi maganar, zai iya bata amma yana tsoron karta batar mai dashi. Cire ogogon yayi ya rike hannuta yace "promise baza kibari asace ba"
Kada kai tayi cike dajin dadi, yace "aro nabaki fa"
Kai ta kuma d'agawa cike dajin dadin, sakala mata yayi a hannu tana shakar kamshin sa dake fita daga agogon, sosai tajita cikin farin ciki sun kara jimawa agurin daga bisani sukayi sallama yabar gidan.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.