Complete Hausa Novels

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 8 of 41

Baa jima ba ta shigo Cikin takun kwas kwas, dagowa yayi ya dubeta cike da mamaki, aranshi yace "alamu yarinyar nan bata da niyyan barin rayuwata, i have to act fast"
Murmushi ya sakar mata yace "ashe kece"
Yap" ta fada, cire abaya tayi ta ajiye gefe sannan ta zauna kujerar dake fuskan tar shi.
Jinjina Too much of confidence dinta yayi aranshi
Tace "hop am save wannan murimshin naka bangane ba"
B'ata rai yayi
"Miya kawo ki office dina..
Karewa hadadan office din kallo tayi sannan ta dube shi tace "i was expecting naga crying baby mama dinka anan"
Mugun kallon yayi yama yace "saboda ke she has fallen sick, what were you tinking da zaki tura mata yan daba"
Tabe baki tayi.
"Am sure kukan banza da tayi yasata zazzabi, koni karama banga abunda zai sani kuka ba, infact banga wanda ya isa na zubdamai precious Hawaye na ba"
Shikam kallon ta yake yana mamaki over confidence dinta, yace "iskanci da kike a titi bai ishe kiba sai kin zomin office tsabar jaraba irin taki"
Murmushin daya fi kuka ciwo tayi sannan ta mike tsaye, idanuwansa akanta tabi gefe table din ta dawo gabansa ta zauna kan table din shikuma a kujera suna fuskan ta juna.
Murya kasa kasa tace "iskancin bai isheni ba, ka taba ganin worthless prositute na iskanci dan kudi ko aji, kaga am all yours kayi abunda kaga dama dani"
Unfasten din shirt dinta tafara, Yarage white vest dake jikinta.
Bai hana taba saima zubawa jikinta ido da yayi
"Hey, look at mee" tace hannu tasa ta tallafo fuskansa, ganin hankalin sa gabadaya baya tattare da ita, yasata duban direction da idanuwa sa suke, wani birthmark mai shape din triangle dake saman boobs dinta yake kalla..
Lumshe ido yayi, yace
"Miye wanan ?
"I dunno nima haka nagani"
Tashi yayi fusace, adan tsorace ta kalli sa, yace tashi ki fice min a office"
Harara shi tayi tace "baka min abunda nakeso ba"
Finciko hannuta yayi da karfin gaske ta fada jikinsa, kansu yana garuwa da juna, nace ki fice min kafin nasaki kuka yanxu nan.."
Magana xatayi aka turo kofar aka shigo, Salim ne ya shigo rike da wasu takardu hannusa, ransa ne ya baci ya tsaya kallon su, daure fuska Mujahid yayi yana huci, Salma kam dariya tayi ta ajiye mai Id dinsa tadau jallabiyar ta tayi waje batare data dubi salim ba.
Mugun kallo Mujahid yamai yace "baka iya knocking kofa ba ?
Daure wa yayi yace "sorry sir, banyi tunanin kana da company ba" ajiye Files din yayi ya fice zuciyarsa na zafi.
Dukan table din Mujahid yayi cike da takaici yadda ta zubar mai da mutunci, "dan iskan yaron nan raina ni xaiyi, ya dauka son budurwarsa nake" azuci yayi magana.

Salma na kokarin kunna mota Salim ya bude ta afusace, fuska ba walwala yace "miya kawo ki nan, make tsakanin ki da dan iskan nan ?
Tsaki taja, "ina ruwan ka" cigaba da kokarin kunna motar tayi, haushi yasashi finciko ta waje.
"Salma sonshi kike kenan Cikin masifa tace "Allah ya sauwake naso shi, dan Allah ka kyaleni karka batamin rai.
"Toh miye kukeyi dana ganku, are you trying to seduce him or what?
Tsaki taja ta harara shi hade da fincike hannuta, "i don't own you any explanation duk abunda kake tunani hakane" shiga tayi zata rufo kofar ya kuma riketa, Salma am sorry, kawai bansan ganinku tare, dat man is full of himself koda kin soshi zaki wahala ne, plz stay away from him"
Tausayin sa taji batace komai ba, sakin murfin kofar yayi, taja motar jikin ta sanyaye, harga Allah bason Mujahid take ba aslima kure shi tasoyi yadda yake dauka kanshi wani abu da Insulting
mutane yadda yadda yaga dama.
Sai yanxu ma taji haushin abunda tayi, saidai bazata kuma shiga tsabgar saba.
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai da Wuta☄

~na~

©ҳaɾaɧ bųkaɾ
®NWA

24___26

Tun ranar Salma da Mujahid basu kara crossing path ba, haka yamai dadi matik'a saboda shigan mai rayuwa da take ba karamin treat bane agareshi. Ta b'anganan Salma ma kusan hakan ne tuni ta bawa banza ajiyar sa, harkokin gabanta da zuwa skull tasa agaba, tsakanin ta da Faiza kowa tasa ta fisheshi bamai shiga tsabgan wani, duk da faiza na rik'e da ita a zuciyan akan cin kashi datai mata saidai kama girmanta shi yafiye mata.

Yau sunday, bayan sunyi karin safe Salma ke jib'e a palo tana kallon ball, ko wanka batai ba jikinta sanye da nyt wear riga da wando, Mom ce ta fito palo cikin shigar alfarma tahau ta da fadan hanata zama da kayan bacci balle yau data kasance weekend lokacin ziyarar Baki, shagwabe fuska salma tayi kaman xatayi kuka ta mike ta shiga dakinta, Hoton sa dake kan console ta fara tozali dashi, muguwar harara ta tafka wa hoton had'e da jan doguwar tsaki ta shiga toilet freshen up. (Ni xarah nace baima san kina yi ba).

*****
Cikin kananun kaya yayi shirin sa tsaf daya matukar fiddo azahirin kyaun kyakyawan sifanshi, zuciyar sa fes ya tsuri mukullin motar sa ya sauko kasa, Junaina kadai ya iske zaune palo tana kallon Jennifer dairy, baibi takan taba ya zauna yana fadin "Ummi dauko min ruwa na sha".
Kaman jira take ya mata magana ta mike tsulum tana mai duban mamaki..
"Yaya Yaushe kuma na zama Adda Ummi ?
Gabansa ne ya fadi, baima san Ummi ya ambata ba, kallon ta yayi gabadaya ta rikede mai kaman Salma saurin maido da hankalin sa waje daya yayi, yace...
"Ummi kuma, wace ce haka ?
Kaman zatayi kuka tace "yayata mana".
Tsaki ya yaja ya mike hade da rab'awa gefenta ya wuce kitchen, Junaina kam ba wuya kukan, share hawaye daya zubo tahauyi sannan ta arce da gudu dakin Hajiya.
Hajiya da Jafar ke zaune kan gado, wanda tuni ya dawo daga tafiyar da yayi, Hirarsu sukeyi cikin nishadi, shi dama jafar ma'abocin raha ne, indai yana Gida toh Hajiya bata da kewa..
Fashewa tayi da kuka ta karasa ciki hade da fadawa kan cinyar Hajiyar, hankali tashi tahau tambayan ta ba'isin, Jaafar kam dauke kai yayi ya koma duban wayansa sanin kukan ta baida nasaba da yayanshi..
Cikin muryan kuka tace "Hajiya sai yaushe zanga Ummi ? Yaushe zata dawo zama damu ?.
Cikin bazata tambayar tazoma Hajiya, murmushin dole ta kirkiro tace "junaina banason kukan banza, indai Ummi ce very soon zaki ganta, Abbanku dakanshi yace xai kawota...
Mik'ewa Jaafar yayi ya fice daga dakin, zuciyar sa namai zafin, baya kaunar ganin kukan junaina koda wasa.
Bata rai Junaina tayi jin an ambaci Abbanta tace "hajiya banason Abba ba ruwana shi dani, tunda nadawo hannuki baizo gurina ba, ni banma sanshi ba, yayata kawai nakeson gani dukda itama ban santa ba bata sani ba, amma zanji dadin kasancewa da ita"
Murmushi Hajiya tayi tahau shafa bayanta tana cewa "very soon zaki ganta, kinji autar hajiya"
Kad'a kai Junaina tayi batace komai ba banda sauke ajiyar zuciya da take.

Fitowan Jafar palon sukayi kicibis da Mujahid rike da bottle water yanai shirin fita waje
"Hankalinka ya kwanta ka sata kuka ko ? Jaafar ya fada yanai kallon shi, fuska babu walwala.
Kallon am not your mate Mujahid yamai sannan yace "miye amfanin ka, kaje ka lallabata tunda sonta kake..
Yak'e Jaafar yayi.
"Ai ita kai takeso, bai kamata kuma kana hurting feelings dinta ba, ko baka sonta she deserve some respect"
Mugun kallo Mujahid yamai yace "fada kazo min kenan"
Ba fada bane am just saying the fact, ya ake ciki da neman Ummi.. ?"
Dariyan rainin wayo Mujahid yayi sanna ya tamke fuska
"Am done searching for bitches" bai jira abunda Jaafar xai ce ba ya ficewar sa waje.
Jaafar kam mamaki ne yakama shi, girgiza kai yayi ya zauna hade da tunanin yadda xai fara nemo Ummi kodan sanya Hajiyarsu farin ciki.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.