Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 39 of 41
Gidan Salim
Salma bata samu runtsawa ba sai bayan sallah Asubah wani mugun bacci ya sace ta, sai after 1 ta tashi da matsanan cin yunwa, ruwa kadai ta iya sha tayi alwala tayi salllah azahar sannan ta koma kan gadon ta kwanta, wani red light taga yana blinking jikin agogon hannuta bata damu ba ta share tahau Tunanin Abbanta da gidansu a Gombe da yadda tayi zaman kanta a gudin tun bayan da abba ya rabu da Amminta sanadin Aunty jamila daya aure ta mallakesa da sai yadda tace zaiyi karshe ma Abba dakanshi yace mata tabar masa gida taje ta nemi dangin uwarta, shine ma dalilin zuwan ta Abuja, bata san kowa agarin ba Allah ya hada ta da Daddy ya taimake ya riketa amatsayin yar cikin sa, Nisawa tayi tace "Allah ya kare ka Abba daga shairin Aunty, nasan bayin kanka bane" shuru tayi tana ayyana idan tasamu hanyan guduwa Gombe zata koma gurin Abbanta.
Around 3 taji motsin ana shigowa, mikewa tayi zaune adan tsorace, Salim ne ya shigo, farar fuskar sa jajir, da ganin sa ba cikin hankalin sa yake ba, cike da karaji yace "ke tashi mu tashi, flight din 5pm garemu"
Tausayin sane ya kamata ganin yana yinsa, tagane yayi high da yawa, cikin sanyi murya tace "yaya you need a doctor, na yadda zan bika amma kabari muje aduba ka, you're really sick"
Wani mugun kallo yakai mata da saida taja baya, Bindigarsa dake aljihun bayan rigarsa ya ciro afusace ya nunata dashi yana dariya yace, "i won't allow you take me for a fool, Get out out.." Atsawace ya karashe maganar.
Dan ihu tayi ganin dagaske zai iya pulling Tigger, tace "yaya zan bika Ghana, amma dole muje asibiti"
"Yarinyar nan wasa kike dani" ya fada, deawer ya bude ya ciro wasu drugs daban dake cikin wani white container ya ciro pills da dayawa ya apka abaki sannan ya kalle yace "Get out, before i pull d trigger.."
Haushi ne yakamata, dan kuwa tsoron ma ta daina ji, tace "babu idan zani, kuma nasan you wont try killig me kaida ko kwaro banga ka taba kashe wa ba".
Kecewa yayi da mugun dariya sannan yace "salma it all your fault you made me become a killer, saboda ke na kashe Babanayaro mistakely, dan haka you wll be stock with me foreva" hannu yasa ya fizgo ta batare daya damu da state of confusion data shiga ba, innalilahi kadai Salma ke ambata sai yanxu tagama gane ba sonta yake ba he is only obsessed with her.
Ihu tahau yi yana janya waje, gate din ya bude ya jata bakin mota taki shiga, kokarin turata ciki yayi ta gantsara mai cizo, wani mugun mari yakai mata saida ta fadi kasa hade da zakin razanannan ihu, hannusa yasa zai damko wuyanta ya lura da agogon hannunta dake blinking Red light.
Ware ido yayi in shocked, ya daga ta tsaye afusace yana fadin "gidan uban wa kika samu agogon nan?
Yawu ta fota mai a fuska, tace "you're insane" sannan tayi kokarin warce kanta ta ruga da gudu zuwa bakin gate din dake hangame, saita ta yayi da bindigar yace "dont you dare leave this house".
Stand still tayi gabanta na faduwa, takowa ya farayi gurinta suka ga motocin Yan Sanda ya diro gurin, motar dake biye dasu kuma Mubarak da Mujahid ke ciki, da sauri suka fito daga mota akidimi.
Salma na gani Mujahid ta rugu ta fada jikinsa tana kuka, shima rungemeta yayi yana kukan yana kara bata hakuri.
Salim kam is shocked, da abunda idansa yagani, ransa ne yabaci aganinsa Salma ta kara yaudaran sane ta hanya fada masu inda ya kawota, bai lura da jinin daya fara zubowa daka hancin saba ya kuma saita bindigar kansu.
Yan sanda dake gurin ne suka ce yayi surrender, ko kallan su baiyi ba balle yayi surrender.
Hankalin Salma ne ya tashi, tayi saurin saki Mujahid, kallon Salim tayi, hanci sa na bleading sosai tace "ya you need so help, plz stop acting crazing muje asibiti plz..." Kuka ta fashe da dashi tana rokansa, amma ina shikam bata kansan yake ba, so yake kawai ya harbe Mujahid dan kishi, takowa Salma zatayi garesa Mujahid yayi saurin rikota yace "he is crazy, dont move further.."
Kallan sa Salma tayi, murya kasa kasa tace "he is my brother, i dont wanna lose him"
Dariyar dayafi kuka ciwo sukaji Salim yayi yace "indai shi kika zaba na gwammace ki mutu kowa yayi asara" harba bindigar yayi saitin Salma ayayinda yaji karfin jikinsa ya kare ya fadi nan kasa, jini ta hanci da kunne, cikin zafin nama Mujahid ya tureta bullet din ya same shi, nan take ya fadi kasa wanwas babu rai ai jini dake ambaliya ta baki, Ihu Salma tayi, Mubarak yayo kansa gadangadan, sauran yan sanda kuma sukayi kan Salim.
Ihu Salma take tana kuka tana jijiga Mujahid, amma ina bai ma san tana yiba, halinkali tashe Mubarak ya ba yan sandan oda aka dauke su biyu cikin Mota, Salma sai kuka take tana rokon mujahid Gafara, duk itace sanadin komai, kuka sosai take har suka isa asibiti aka wuce dasu Emergency.
Salma kam kuka jikinta ya gama gayamata Mujahid dinta bazai farfado ba, dakyar Mubarak yahau Lallaba ta rage kuka, wayar Mujahid dake motarsa yadauka ya kira su Hajiya ya shaida masu suna asibiti, sannan ya karbi namban mom gurin Salma suma ya sanar dasu abunda ke faruwa.
Baa fi minti 30 ba kowa family ya hallara agurin, tsabar Kidima Salma bata ma lura da Abbanta dake tare da Junaina ba, Jikin Momy ta fada tana kuka mai tsuma Zuciya, Kowa kallan ta yake cike da tausayi, Annah sai ihu take tana fadin shikenan Jikana ya mutu tun banga tattaba kunne ba, haushi ne yakama Hajiya tahau rokonta tayi shuru saboda asubiti ne kuma ana iya koronta.
Doctor ne ya fito cike da tashin Hankali, da sauri Jafar da Mubarak suka karasa gurinsa, hankalin sauran kuma ya koma kansu.
Zufa Doctor ya share yace "Allah yayi dayan su rasuwa tun kafin ma su iso asibiti.."
Salati ko wanne su dauka cike da firgici.
Dakyar Salma ta iya sakin Mom, bakin na rawa tace "Doctor waya rasu cikin su ?
Dogon Ajiyar zuciya Doctor yayi sannan ya kalli Mubarak yace "Suwaye Family din wanda aka Harba ?
"Gasu nan" Mubarak ya nuna su Momy da sukayi wiki wiki da ido, tuni jikin Salma yahau rawa.
Girgiza kai Doctor yayi yace "Am sorry....
Bai karasa maganar Salma ta saki wani irin ihu tayi tangal tangal zata fadi Abbanta yayi saurin taro ta hade da kwalla kiran sunanta da "Ummi"
Hade ido sukayi, zatayi magana ta fadi jikinsa sumammiya.
Happy Sallah in AdvanceðŸ˜Â
Last page ya rage mana, Insha Allah.
[9/7, 12:38 AM] Xarah Bukar: ​​​Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION {NWA}
Wannan littafin Gabad'aya na Sadaukar dashi ga kawar arziki *Aynarh Dimples* Allah ya barmu tare, LYSMðŸ˜Â
Ana Bahebak â¤â¤
Allahu akbar kulu'nafsi za'ikatu mauti, Allah yaji kanki da rahma Maman besty Yar ficika. May jannatul Firdausi be ur final destination.
Last page
65
Hankalin kowannan su kara tashi yayi, akidime su Hajiya sukayi kanta tare da Salati, saurin dakatar dasu Doctor yayi ganin suna neman maida gurin kasuwa, Nurses biyu ya kira suka shiga da Salma wani daki dan samun nutsuwa da dawo wa hayyaci, Annah kam kuka take rusawa tana ihun jikanta ya mutu. Takaici goma da ashiri ne ya kama Doctor yace dasu Jafar da Mubarak su iske sa office dinsa, da azama suka mara mai baya suka shiga suka zauna cikin kaguwa dason sani abunda zaice. Duban su Doctor yayi cikin nutsuwa da hankalta, yace "Alhamdulilah dan'uwanku yayi surviving gunshot din, thanks to Allah komai yazo da sauki mun samu mun cire bullet din, but he is still unconscious"
Ajiyar zuciya na relief su Jafar suka sauke, Mubarak yace "Salim fah, miye condition nasa ?
Nisawa Doctor yayi yace "am sorry we lost him tun kafin ku karaso asibiti saboda drugs dayay using, he died of a heroin overdose,"
Mubarak kam baiyi mamaki ba dan kuwa yasan Salim baya rabuwa da harka miyagun kwayoyi, Jafar kam jikinsa ne yayi sanyi yadda komai ya faru acikin kankanin lokaci,
Doctor yace "yanzu dare yayi, sai zuwa gobe zamu saki jikinsa"
jiki sabule suka koma gurin su Hajiya dake tsayuwan Jimami, nan suka zayyane masu yadda Doctor yace, duk da bawani sanin Salim sukayi ba mutuwar tai mugun girgiza su (sabon Kabari mai karasa tsoron Allah), Mom kam kuka tahauyi abun gwanin tausayi, su Daddy da hajiya suka hau bata baki. Haka suka bar asibitin jikin sanyaye banda Hajiya da junaina da suka zauna jiran fardadowan Salman da mujahid. Washe gari aka mika Salim gidan gaskia. Da yamma Salma ta farka cikin matsanan ci tashin hankali, dakyar Hajiya ta kwantar mata da Hankali dacewa mujahid nanan kalau, saidai fadi mata rasuwar Salim yasa ta kuka matika, sosai Junaina taji tausayinta sai yanxu tagane tanason yayarta haushi abunda tayi mata yasa take nuna mata kiyayya, Suna cikin haka Abban su ya shigo, mikewa Hajiya tayi ta fice dan basu guri, kuka shima Abban ya fashe dashi yana neman gafarar su, atake suka ce sun yafe dan kuwa hannuka bai rubewa ka jefar, cikin shesheka Salma ta tambaya shi ina aunty Jamila, yace da ita ya jima da rabuwa da ita tunda yagano asiri take bashi cikin abinci. Sosai yaran sukaji tausayin abbansu, dan family reunion sukayi a dakin cike da farin ciki.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.