Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 6 of 41
Mikewa tsaye yayi ya kai ido kan hannusa dan duba tym saidai wayam yagani ba agogo, k'asan gurin yahau dubawa saidai wayan, mamaki yayi dan daxu ma ya duba agogon,
"Kodai.. Ya fadi aransa, ba tantama itace amma how cms, can ya tuna daxu hannusa da nata sun hade.
"Yarinyan nan wasa take dani" ya fada, fitowa yayi waje, kicibis sukayi xata shiga yayi saurin finciko ta hade da manne ta jikin bango, hannusa daya shake bisa wuyanta.
Zare ido tayi tanai kallon yadda ya koma mata kamar zagi, murya sheke tace "sake min wuya...
Kara shaketa yayi, ya matse ta tsam har suna shakan numfashin juna, cikin zare ido "dan ubanki, idan kina karuwancin ki, sata da rashin kunyar ki, ki tsayar can gurin k'ananan k'wari da kika saba yi suna kyale ki, dont you dare ki kusanto gareni, am not one of those useless men da kike toying around dasu, Understand?
Harara takai mai ta kuma cewa "kasakeni ?
Sakinta yayi, yana kara kallon shegen kayan jikinta, sannan yace "ina agogona ?
"Ka bani ajiye ne"
Kara daure fuska yayi
"Tunda kinyi shaye shayan da kika saba ai dole kice haka" kara matseta
Yayi, jikinsu na gogan juna ya kuma tambayanta.
Wani irin yanayi taji da tunda taxo duniya bata taba jinsa ba, d'an matsar da jikinta daga nashi tayi ya kara matseta, daurewa tayi ta kallesa cikin dakewa gudin karya gano komai tace "bansani ba" hade da daure fuska, jikinta yahau dubawa baiga komai ba, can idanuwasa sukayi caraf akan boobs dinta, kallon su yahau yi, xaikai hannu tayi sauri sa hannunta ta tokare shi, bige hannu yayi yanai mata mugun kallo yace "Worthless prostitute kin dauka dason raina jikina ke goguwa da naki, banxa marar tabiyya" bai jira cewarta ba ya tumbula hannu cikin yar top din jikinta yafara laluban agogon shi, sai gashi ya dauko.
"Banxa barauniya" ya fada hade da tureta gefe.
Ranta ya gama bacci, saidai bazata bari yaci galaba akan taba, dariya tayi tace "ai ban cika barauniya ba tunda baka da guts din arresting dina, dan iska kawai"
Murmushin da shika d'ai yasan manufarshi yayi yace,
"We will see about that, useless girl, bani da lokacin ki" tafiyarsa yayi yabarta nan tsaye.
"Salma karki ma banxan nan kuka, you're strong" ta fada aranta, jiki sabule ta juya ciki takira maza biyu sukasa Salim a mota taja su sukayi gida zuciyar ta dauke da tunani iri irin. Tana isa gida dakyar tasamu ta rike Salim zuwa part dinsa danta lura sam baya cikin hankalinshi sannan tabi ta kitchen ta shiga part dinsu cikin sand'a ta gudun cikin dakinta.
Hankali kwace yasa mukulli ya bude palon gidan ya shiga, jin shuru yasa shi sauke ajiyar zuciya tare da kokarin haurawa sama.
"Mujahid.... "
Yaji kiran sunan sa tamkar saukar aradu, gabansa ne ya fadi ya juyo, Hajiya yagani sanye fuska babu annuri.
"Daga ina kake, wato ni mahaifiyar kake wasan buya da ita, ko kuwa dai ni saar kace ??
Cikin fusata ta jeromai tambayan tare da karasa wa gabansa suna facing juna.
D'aure fuska yayi yace "aiyuka sukamin yawa"
"Aiyukan banxa da haryau ka kasayin simple aiki dana saka"..
Kallan mamaki yay mata, "wai simple aiki, nemo mutum daya bata for 7 years ne simple, kuma ma just 3 month back aka san she is missing"
Afili yace "hajiya sorry to say, ya kamata ki manta da so called yarinyan nan, cox nayi iya kokarina ban ganta ba.."
Wani mugun mari Hajiya ta watsa mai kafin ya ida magana, cikin huci tace "diyar kanwar tawace so called, Mujahid ni kake gayawa maganan nan, yarinya da uwarta taci kashinka da fitsari kake kira da so called, atleast idan baka nemo ta dan niba ko adan yadda uwarta ta raineka ai ka nemo ta"
Idon shi sosai ya canxa launi, yace "shikenan Hajiya zan ajiye aikin, sai anemi wanda xai nemota amma bani ba, tunda duk kokarin da nake baa gani, narasa miyasa bakya kaunata acikin gidan nan, kowa zaiyi abunda yake so amma banda ni kuma tunba yauba kike treating dina haka" kaman xaiyi kuka yayi maganar, wuce warsa yayi ba tare daya jira cewar taba.
Jikin hajiya sosai yayi sanyi, tasan Majahid da taurin kai, tunda ya furta bazai nemo taba toh kuwa bazai ba, tsoro ne ya kamata kar ya ajiye aikin.
Zancen Abban su Mujahid ta tuna.
"Salamatu ki rage daukan zafi akan Mujahid, shi yaro idan yayi laifi baa mai duka ko zagi dan kuwa zai iya zama tsegararre, hakan da kikeyi yasa yazama mai mugun taurin kai acikin yan'uwan sa" abunda mijinta ke yawan fada mata kenan aduk randa Mujahid yayi mata laifi, Ajiyar zuciya ta sauke tana kara tuno wasu abubuwan da Abban yaranta ya fadi mata kafin rasuwar sa.
Cikin kunci ya karasa dakinsa, ya jima yana saka da warwaran neman mafita dan kuwa bazai yadda kudurin Hajiya ya tabbata akan shi na auramai ummi ba, ga kuma wata can Salma tanai daura mai zafi, tunowa yayi sanda ya matseta jikin sa dawani yanayi daya shiga, saidai abun daya lura ita ko ajikinta da alamun shi kadai ya shiga yanayin, tsaki yaja yace "ta saba da maza no wonder she wont feel anything...
Dogon Ajiyar Zuciya ya sauke, aranshi sunan Ummi Salma ke yawo a kwakwalwan kanshi.
***
Bayan kwana biu...
Mujahid bai kuma fita office ba, kullum yana makale a daki, ko kiran shi akai a office saidai ya dauka yace baya da lapia, hankali Hajiya yayi matuka tashi sosai, saida taje dakanta ta lallabashi bayan tace mai ta hakura da neman Ummi harsai randa Allah ya bayyanata sannan ya saki ranshi.
Ta bangaran Salim ma kusan hakane, mugun Haushi salma yakeji saidai sonta na nan daram aranshi.
Kasancewar yau suke da lectures masu yawa, tun 10 Salma ta shiga skull. Karfe hudu bayan an fito sallah, sukaje faculty ita da abokanta Shehu da Habib submitting wani assignment da aka basu kwanaki baya kowa yayi submitting banda ita.
Zama sukayi kan dakali suna hira da musun Ball, dan kuwa Salma akwai son Ball, Suna cikin yi Malama Faiza taxo da motar ta kirar Civic tayi parking gurin ta fito rike da takardu hannuta, dawowar ta kenan daga lecture data dauki yan level 2.
Dariya Salma tayi ta kalli Habibu tace ka kalli wani film the sugar Mummy.
Shikam Habib ya dauka da gaske take, yace "miya faru, halan film din ya hadu...
"Ina fa ya hadu, wata tsohuwar matace ta auri Yaro koma ince sa'an ta, kaga couple din, ko dacewa basuyi ba, i dunno y old hags dinnan basa respecting kansu su nemi daidai dasu".
Dariya Habib da shehu suka kwashe dashi, tsaf Faiza ta gane da ita Salma take, dakewa tayi ta tsaya duban takardun hannunta duk dan taji karshe cin fuska da Salma ke mata.
Habib yace "indai akwai love ai shikenan"
Tsaki salma taja, "love my foot, kaga kamin submitting din nizan shiga Auditorium nasha Ac, kasan ban saba da zafi ba"
Shehu yace "Salma akwai fa Math 101 yanxu, kodayake Mutumin bai shigowa da wuri"
Yatsine fuska tayi tace "nikam sai 5.30 xan shigo hall, nasan Shirgegen gardin nan ba zuwa xai ba" juyawa tayi ta kara gaba.
Sai sannan su habib suka lura da Faiza dake kallon su, cikin rawar jiki suka gaidata hade barin gurin.
Ran Faiza ya gama baci, tana shiga office dinta tahau tunanin yadda zataci uban Salma.
Salam dai akwai kwakwala balle tabata F a course dinta, tunanin take can dabara ta fado mata, timetable tadau ta duban sunan wanda ke masu Math 102, Malam Dauda ne kuma suna gaisawa, mikewa tayi ta iske shi office zaune baya da shirin fita lectures, rokosan tayi akan ya bata aran space din, ba masu yabata dan kuwa bashi da niyya zuwa.
Office ta koma da azama tadau Test Question papers daya kamata ta masu test next week ta fita dashi.
Securities shida ta kira suka rakata Hall din, dalibai kam tsorata sukai ganin test zaai tuni wasu suka tsure, shehu kam kokarin kiran Salma yahau bata dauka ba, gashi kuma itace mai kokarin, nata suke kwashe idan zaai test.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.