Complete Hausa Novels

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 2 of 41

****
Reckless driving da take bisa titin ya sanya mutane da dama da suka san ciwon kansu matsawa gefe sunai bata guri. Gudu take shantakawa iya san ranta hade da kyalkyale dariya ganin yadda kowa ya bata sarari, daidai data karaso traffic light ya nuna red, dogon tsaki taja tayi gaba ba tare data tsayar da motar ba. Bata ankara ba kiris ya rage ta bugi motar data danno, cikin kota kula da abunda ya faru ta fizgi motar at 360. Gudu take sosai can ta lura da motar data kusan bigewa na biye da ita, tsoro ne ya kamata kasancewar last week kadai Daddy ya gargadeta da reckless driving, bata daddara ba kuma takeyi, fatan ta Allah yasa ba yan road safety bane, dan dakyar daddy ya amso mata motar ta da sukayi seizing kwanakin baya.

Yadda take sharara gudu haka yake binta a baya, baisan waye acikin motar ba amma yayi alwashi koyawa koma waye lesson, dama ranshi a bace yake yasamu scape goat dazai huce haushi akanshi. Ringing din wayarsa ce ta katse mai hanzari, murmushi ya saki ganin wacce take kira, dauka yayi hade da sakawa a speaker.
"Fa'iza am driving, zan kira ki later.
Tace "Mjay karka manta by 2pm zaka zo dauka na".
Bata rai yayi yace "you know am not your driving, kuma am not a jobless man, bazan iya zuwa ba ki shiga cab" katse call din yayi but deep down yasan dole yaje yayi picking dinta bayason tana shiga motar haya. Kaman kiftawar ido yaga wayam babu motar dayake bi, dukan sitiring yayi hade dayin U turn ya kama hanyar komawa office.

Ajiyar zuciya ta sauk'e ganin motar dake binta tayi gaba, ahankali tayi reverse ta fito daga supermarket inda ta shiga tayi parking, da gudu ta kuma fizgar motar, Karar shigowan msg wayarta tayi, da azama ta duba.
"Salma kiyi sauri, Malama Fa'iza ta karaso, da alamun zata dau Attendance"
Dogon Tsaki taja hade da duba tym, 12 to 2 suke da lecture dinta, amma dan maita stupid malamar harta shiga hall just 12.05, koda yake daidai take da ita. Wani mugun wuta ta baiwa motar, bata zarce ko ina sai gwagwalada Abuja.

Cute xara'u 😘
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: [18/07 12:25 PM] aυnтy cute хaraн :
*Zuma sai da wuta*

~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ

Masu k'orafin pages sunyi kadan kumin uxuri, kuyi manaji da iya abunda xan iya baku. Idan nasamu lokaci zan kara hannu.

*Wannan shafin Naku ne House of novella da dandalin makaranta, Nagode matika da kaunar ku, ILYA*❤

3 - 10

Parking tayi daidai multi purpose hall inda suke da lecture. jakar ta dake ajiye gefe ta dau ta fiddo kayan kwalliya ta kara gyare fusk'ar ta dashi sannan ta bud'e kofar ta fito, cikin tsadaf ta fada ajin gudun kar Malama Fa'iza taji shigowarta kasancewar gabad'aya hankalin ta na bisa allon datake rubutu, kallon banza yan matan ajin suka bita dashi, bata damu ba ta karasa inda maza sukafi yawa ta zauna a sit dinta da tuni sun kama mata.
Murya kasa kasa, abokinta na gefen ta yace
"Salma yau mutumiyar ki rashin kirki take ji, ta hana kowa rubutawa wani attendance"
Ajiyar zuciya ta sauke, zatayi magana kenan, Fa'iza ta juya tanai fadin sunan topic dinsu na yau, hada ido sukai tayi saurin mazewa kaman ta jima da shigowa ajin.
Cikin rashin damuwa da ganinta Fa'iza ta cigaba da lectures dinta, tana gamawa tahau kiran attendance d'aya bayan d'aya bayan ta gargardi kar wata shegia ko shege ya bita office k'orofi, tana gamawa ta fice daga ajin.
Dariyan takaici Salma tayi, sam bataji haushi ba saidai shegia data ambata yay mugun b'ata mata rai tasan kuma babu tantama da ita take, tunda kowa was present banda ita.
Ko hira bata tsaya yi da abokanta ba, ta koma motarta taja ta at 360, department dinsu ta zarce ta fito tashiga ta tsaya bakin kofar office dinta. Hannu takai bisa kofar taji ta a bude, tsulem ta fada tanai karewa ko ina kallo sannan ta zauna tanai kallon hoton wani guy dage jikin frame akan table din. Hannu takai zata dauka taji motsi mukuli a kofar, adan tsorace ta duka kasa hade da boyewa under table.
Tsaki fa'iza tayi
"garin sauri ashe ban rufe kofar ba" ta fadi.
Turo kofar tayi ta shigo ta ajiye jakarta sannan ta shiga toilet dauro alwala.
Mik'ewa tsaye salma tayi cikin sauri tadau biro dake gurin ta rubuta "ba wani shege kowa da uban" ajikin wata takarda dake gurin sannan ta sure frame din hoton tayi waje ahankali, da gudu ta karasa cikin motar ta hade da sauke numfashi tanai kallon hoton, guy din bai wuce 36 ba, saidai kuma yayi wa Fa'iza yaro idan ma ya girme ta kadan ne
"Shi kuma wanan ya rasa waxai aura sai tsohuwar nan, lailai malama dole kanki yayi hayaki"
Surutai tahau yi ita daya.

Bangaran fa'iza kuwa, tana fitowa sallaya ta shimfud'a tahau sallahn azahar bayan ta idarne ta koma kujera ta zauna saidai wayam babu hoton data saba kalla akullum idan ta zauna, baza ido tayi tana nema taci karaf da abunda ke rebuce, mamaki sosai ya kamata tahau cigaba da duban hoton, zuciyarta na zargi wani abu rashin tabbatar wa yasa ta kawar da tunanin.

Karfe 2 da minti goma ya karasa makarantar, parking yayi a gaban department dinta sannan yadau waya kokarin kiranta.

Jakarta ta zuge ta cilla frame din ciki, sannan ta juya yin reverse, Motar dazu dake binta tagani ya rufe mata baya, guntun tsaki taja hagonsa zaune cikin suit batare da jacket dinsa ba, kansa sunkuye yanai duban wayarsa.
"kut ashe ma ba officer bane, naketa kokarin boye kaina, am sure sona yake datx y yaketa bina, aikuwa xan koyamai hankali"
Dogin tsaki taja had"e da bud'e kofar afusace.
Yana zanune yaji ana buga mai glass, bai dagoba sai wining glass kasa da yayi dan gabadaya hankalinsa nakan nambar Faiza dayake kokarin turama sakon ya iso.
"Uban wayace ga dinga bina duk inda na ratsa, ko an gayama so dolene, ko kuma ma dai ince Saceni kekeson yi dan kasamu kudi"
Ta fada cikin karaji da zare idanu,
Chak yayi da wayan ahannu, bai iya dagowa ba saboda kalamanta dayaji bambara kwai wai So, shi idan akwai abunda ya tsana bai wuce kalmar so va balle soyayya, who d hell is she dazai ma sota balle ya bibayeta, bai gaba zancen zuci ba yaji tana fadin.
"Kodayake nasan maganin ka, am calling the police saina ga ubanwa ya tsaya ma" wayarta dake aljihun wandon ta tadauka tafara dailing namba.

Shikam gabadaya ya gaba fusata, ba namijin daya taba mai cin zarafi irin haka balle mace, mata daya daukesu kanana k'wari wanda daga kuka banza sai shagwaba suka iya, murmushin dayasan munafarsa ya saki, sannan ya turawa faiza sakon ta fito nan da 30 min, dan kuwa zaman jiran dan sanda da zaizo arresting dinsa xaiyi.

Matsawa gefe Salma tayi tana wayan.
"Ya salim dan Allah karka jima, kayi sauri ka karaso kafin ya gudu.
Yace "Pretty karki damu, yanxu zaki ganni, make sure kiyi keeping dinshi bizi kafin naxo".
"I'll' tafadi.
ta katse wayan.
Maida dubanta tayi garesa, saidai har yanxu ta kasa tantance fuskasa dake duk'e, kuma window ma yayi wining dinta sama.
"Laila ma mutumin nan, mugun nan rainin wayo ne, tayama xanyi keeping dinsa busy alhalin baima kallo ni" tsaki taja tahau safa da marwa a gurin.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.