Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 28 of 41
Kusan rabin awa Mujahid yayi yana playing b-b kanan ya koma cikin gidan, jikin sa sharkaf da zufa, so yake kadai yayi freshen up dan samun dadi jikinsa, Salma naji shigowarsa ta maida dubanta garesa, dogon tsaki taja ta hararesa hade da dauke kanta, bai ce mata uffan ba ya haye sama, aranshi yana fadin "bari nayi wanka na sauko zakici ubanki ne"
Toilet ya fad'a ya sakarwa kanshi ruwan shower mai dumi, shower gel din yadau ya matso hade da shafawa a fuska daidai kan idanunwa sa, runtse ido yayi sakamakan azaban daya ziyar ci idon, "wanna yajin daga ina kuma" yafa d'a aranshi, kara tasar gel din yayi yakuma shafawa dan wanke idon da kyau, raradi ya kuma ji yayi azama kashe warm water aganinsa yajin daga ruwan dumin ne, ruwan sanyi ya kunna ya kuma murza gel din a ido, azabar tafi ta daxu, wulli yayi da shower gel din yahau murza ido da ruwan sanyi saidai ina ko alamun sauki baiji ba banda radadi da idon suke, sosai suka sauya launi zuwa jajir. Ganin ba madafa yasa ya dau sabulun dake gurin yayi wanka adaddafa idanu a kulle.
Murumshi kawai Salma keyi ita daya, jira take taji ihun sa shuru bataji ba, jin taku ana saukowa yasata azama mik'ewa tsaye hade da kallon gurin. Jaafar tagani, laptop rike hannusa yanai sakar mata murmushi.
Yace "har kin tashi ?
Risina tayi
"Yaya ina kwana ?
Lapia" ya amsa, aranshi yana mamakin bata kirashi da Habibi ba.
"Yaya fita zakayi"
Kai ya girgiza, "garden zan futa na zauna, akwai aikin da nakeyi nagaji da zaman d'aka"
"Muje na tayaka zama" Ta fada hade da daukar wayarta dake ajiye kan kujera.
Murmushi yay yayi gaba ta mara mai baya.
Duk akan Idon Junaina dake makale bakin kofa kitchen, haushi ne yakamata.
"matar nan sai shishigin tsiya wlh, da farar safiya ko miye nabinsa waje" ta fadi, tsaki taja wata zuciya tace kema kije gurin masoyinki Mujahid mana, kai ta girgiza tace aikuwa dai kila ma bacci yake bara naje na tasoshi muje waje. Da sauri ta haura saman.
Dakyar Mujahid ya iya bude ido, sosai sukayi Jajir, ko lotion bai iya shafawa ba ya shirya cikin kananun kaya, black shade yasanya a fuska ya koma toilet yadau shower gel din yana kalla cike da mamakin sabon al'amari.
Ahankali Junaina ta turo kofar dakin ta shigo, babu kowa ciki tayi tunanin koya fita, wayarsa data gani kan gado yasa ta karasa ciki hade da daukar wayar, camera ta shiga zata dauki kanta Selfi ya fito daga toilet. A tsorace ta dire wayar, cikin inda inda tace "Good morning".
Mamaki ne yakama shi, yaushe Junaina ta renashi haka harda shigomai daki batare da izinin saba.
Fuska ya murtuke "ke!!! Miya shigo dake nan..
Kaman marar gaskiya ta ware idanu, "dama wai kiran ka zan..."
Katse ta yayi da cewa "wato bincike kika zo yimin ad'aki harda daukan wayata, gayamin waya aikoki ?
Yadda yake magana yasa ta tsorota, bata ga alamun wasa tattare dashi ba, kaman zatayi kuka tace "wallahi yaya ba bincike nazo yi ba ?..
Cikin tsawa yace "karya kike, ni nasan halin ki am sure kuma rahoto kikazo samu dan kaiwa gaba".
Kasa magana Junaina tayi, gabanta na dukan uku uku, ga kuma haushi kalamansa daya turnuk'e ta, koda take nemo rahoto aishi take kawo wa shine kuma yau zaiyi turning tables around.
"Get down on your kneels" ya fada cikin harsh voice.
Kuka ta fashe dashi "yaya dan Allah kayi hakuri"
Rab'awa yayi ta gefenta ya wuce yana cewa "bari na dauko belt, yau sai kin gayamin ubanwa ya aiko ki"
Da sauri tayi kneel down tana rokansa, belt ya dauko ya tsula mata daya abaya, ihu tayi tace "na shiga uku, yaya wlh da akwai zafi"
Jinjina kai yayi yana tunanin anya ba ita tasamai abu mai yaji a shower gel dinsa ba, dan kuwa kafin yafita playing b-b yayi wanka da gel din baiji yaji ba.
Fuska ba annuri yace "wato daxun kin shigomin daki ko ?.
Ware ido tayi cikin rashin fahimta, yace "badake nake ba" daka belt yayi zai tsula mata.
Tace "yaya wlh yanxu nashigo, daxu dai naga Adda Ummi ta sauko daga stairs bansani ba konan ta shigo" kuka sosai ta fashe dashi
Cize Lab'a Mujahid yayi aranshi yace "lailai yarinyar nan ta cika yar daba" kallon Junaina yayi yace "b4 d count of three tashi ki bace anan"
Mikewa tayi ta fita da gudu tana sosa baya.
Nisawa Mujahid yayi yakarasa bakin mirror, cire glass dun fuskar sa yayi yanai kallon idonsa dayai jajir ya duru da ruwa, wani irin raradi da azaba yake ji.
Sunan Salma kadai yake ambata aranshi, shi kadai yasan rashin mutumcin dazai mata.
A can Garden kuma.....
To be continued......
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION...
Allahu akbar kulu'nafsi za'ikatu mauti, Allah yaji kanki da rahma Maman besty Yar ficika. May jannatul Firdausi be ur final destination.
58
Acan Garden kuwa zaune suke kan d'aya daga cikin kujerun, Jafar kam duk'ufa yayi da danna laptop dinsa kasancewar wani babban aiki dayasa agaba, Salma kuwa wayarta kadai take latsawa, so take ta kira Mujahid amma tafasa gudun karya dago abun data mai, ajiye wayar tayi a cinye hade da sauke ajiyar zuciya.
"Kin gaji ne ? Jafar ya fad'a yana cigaba da aikin sa ba tare daya dube taba.
Dubansa tayi.
"Bakai ka shareni ba" ashagwabe tayi maganar.
Dariya yayi
"Kinga wani case nake bincike akai, mayb zuwa next week zanje Kaduna"
Dadi Salma taji aranta, idan ya tafi zata samu sararin yiwa Mujahid rashin mutunci.
"Murna kike zan tafi ko ? Ya jeho mata tambaya.
Kunya ce takamata, ta dake tace "yazaka ce hakan bayan kai yayana abun alfahari nane, ni wlh banso ka tafi kaine kaidai good abu arayuwa ta"
Murumshi yayi, ciki ciki yace "naga alama kam".
Bataji abun da yace ba, zatayi magana suka ji ana rangad'a uban horn daga can bakin gate, maida dubansu sukayi b'angaran, wata mota jeep ce ta shigo ta karasa maajiyar motoci ta tsaya.
Salma tace "suwaye ne..
Mikewa tsaye yayi itama ta mike suka fara tawaka gurin....
Wata kyakyawar tsohuwar matar ce ta zuro kafa daga motan ta fito, da ganinta kasan ta hada alak'a da masu gidan, da azama driver ya zagawo gurin ta hade da risinawa ya mika mata wani sliver walking stick, amsa tayi tanai karewa gidan kallon hade da sauke sanyayyiyar ajiyar zuciya.
Gaban Salma ne yafadi, tagane matar data gani a hoto ce, murya jafar taj yace "Granny dinmu ce, mahaifiyar Daddyn mu"
Yaken dole Salma tayi, kwakwata bataga alamun annuri a fuskar taba, shuru tayi suka cigaba da takawa gurin da take tsaye tana shakar sanyayyar iskar gurin.
Daga inda suke tagowa Jafar yace "wa nake gani kaman Annah." Karashe maganar yayi cikin zolaya.
Dariya Annah tayi har hakoranta suka bayyana.
Ga mamakin Salma taga Annah ta juya wani bangaran tana lalube, cewa take "Jafar kaine ko kuwa kunne na ne ?
Karasawa yayi ya rikon ta, yana dariya gani tanan".
Tace mikomin gilashi na yana mota, dauko mata yayi ta amsa tasa sannan ta kallesa "wato kun gurma ko ganin ku baa yi, tunda baku iya zuwa gurina gani zo gurinku"..
Dariya yayi.
"Kai Annah daga zuwa sai neman sababi ?
"Kaga ni bani guri" ta fada, wucewa zatayi Salma tace "Annah ina wuni ?
Kallon Salma tayi, bata amsa ba sai tab'e baki datayi ta wuce.
Jiki sanyaye Salma ta dubi shi.
"Bata gani ne ?
Alamun tayi shuru yayi mata, saida Annah ta masu tazara yace "zaki sha duka idan taji kinci mata bata gani, tana gani amma sai da glasses,
Ware ido salma tayi.
"Miya sameta halan
"Bakomai, ciwon idon gada sukayi gurin babansu, sai dai nata yayi worst, sau biyu ana mata operation"
"Allah sarki, amma naga ku yaran Hajiya baku gada ba"
Dariya jafar yayi, yace "inji wa, koda yake niban da matsalan ido, Aunty Bilki da Mujahid suka gado ta"
Mamaki ne yakama Salma bata ga alamun ciwon ido ga mujahid ba, dama ma Aunty Bilki tanasa glass.
Shuru tayi suka cigaba da tafiya ciki.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.