Complete Hausa Novels

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 15 of 41

Da Gudu Salma ta fada cikin gidan, babu kowa palo sai motsin Mom da taji tana kusurniya a kitchen, dakinta ta nufa tayi cilli da wayanta ta fada cikin bathroom, ruwan shawa mai sanyi gaske ta sakarwa kanta, ba karamin tafasa zuciyan ta yake ba, wani mugun tsanan Mujahid takeji aranta, haushi ta daya da yayi kissin dinta a banxa, yaci bulus alhalin babu So ko kauna tsakanin su. Kukan da ta dade batai ba arayuwanta ta fashe dashi, sosai take kuka ba kakkauta, saida tayi awa biyu sannan ta fito daure da towel bayan ta cire kayan jikinta, dakyar ta iya fadawa gado ta zube kaman mataciya, hawaye take tadau wayarta dake gun ta tura mai text msg kamar haka .
"i hate you with passion," sannan ta kashe wayar.
(Ni xarah nace Salma you too dey exaggerate, d'an kiss kawai duk kin ishe mu da kuka as if you know enjoy am).

[27/07 1:22 PM] Mujahid na komawa gida kasa zaune yayi, nan tsakiyar palo ya tsaya yana kai komo kaman wani zautacce, ganin text msg dinta yasa shi gigicewa, "nashige su, meke faruwa ? Ya fada, flashes din abunda ya faru ke yawon mai akai, nan yahau tryping no dinta yajita akashe, cilli yayi da wayan ya shiga daki, dakyar yasamu yayo wanka ya kwanta kan lausassiyar bed dinsa amma tuni bacci ya k'warace ma idanunsa, juyi yayi tayi akan gado da tunanin barkatai, abubuwa da dama zuciyarsa ke sakarmai saidai ya kasa gasgata komai, mikewa wa zaune yayi yana fadin "no, it cant be...", ganin zuciyar sa na neman tarwatsewa ya mike ya dauro alwala yahau nafilo da neman gafaran Ubangiji.

****
Washegari Salma ta tashi da zafanfan zazzabi da saida aka kwantar da ita asibiti, hankalin Mom sosai ya tashi dan tunda take bata taba ganin Salma cikin yanayi haka ba, kwanan su uku Salma ta fara dawowa daidai, data tuno encounter dinta da Mujahid wani mugun bak'in ciki take ji, haka dai suka dawo gida ta koma sabgogin gabanta bayan tama kanta alkawari fita harkan Mujahid koda ace zai kasheta bata kuma tanka shi.

Acikin kwanakin nan Mujahid shi kadai yasan irin tashin hankalin daya shiga, kullim da salmw yake kwana yake tashi, ba yadda bai ba dan yakaceta aransa amma ya kasa shi kuma yasan ba sonta yake ba, kiranta awaya da tura mata aplogy text ba wanda baiba saidai shuru kota kansan bata bi, gidansu yaje yafi adurga bai samun ganin ta.

Yau da wuri ya shirya cikin kananu kaya ya fita office, office din Mubarak ya nufa yahau shi da masifan yaja masa matsala, Dariya sosai Mubarak yayi yace "bafa sonta kake ba, miye kuma xai dameka dan taki kulaka har yanxu"
Haushi ya kama Mujahid yace "ai bance ina sonta ba, hakuri nakeson bata dan nayi realizing ban kyauta mata ba"
Tsayar da Dariyan Mubarak yayi yace "inada wani plan"
Harara Mujahid yakai mai yace "banso wani absurd plans dinka, tashi zakayi muje gidansu ka gyara abunda ka bata..
Ware ido yayi "ni kuma asuwa mi zance mata..Salma kiyi hakuri nina turo abokina yayi kissing dinki..." Cikin salon rainin wayo da Dariya Mubarak ya karashe maganan.
Takaici ne ya rufe Mujahid, afusace yabar office din, mikewa Mubarak yayi yabi bayansa yana fadin "muje kafin kayi kuka" bai kuma bar dariyan ba.

***
Fitowa Salma tayi haraban gidan, jikinta sanye da cikin red & creamy less, da madaidaicin crem veil yafe bisa kafadarta, Yau bata da lecture, sunyi da su Shehu zasu hadu Central Library yin wani Assignment da aka basu.
Motarta ta shiga ta kunna hade dayin reverse.

Mubarak ne ke tuka Motan, fuskar Mujahid Murtuke cike da haushi dariyar da abokinsa yake, suna shigowa anguwan ya hangi Motar Salma ta fito daga gidan, can hanyar titin gabansu yaga tayi, tab'o Mubarak yayi yace "kai tsayar da motar gatacan ta fito"
Tsayar da motan Mubarak yayi, Mujahid yahau kokarin bude motar dan fita.
Mubarak yace "yaukam indai taki kulaka, ka shareta kawai for good" ln serious tone yayi maganar.
Shuru Mujahid yayi ya fita daga motan, Keke napep yayi saurin tarewa ya fada ciki hade damai nuni da yabimai bayan motar dake can gabansu.

Tuki take tanai bin wakar "Love will Remember" na Selena Gomez, fuskar ta fayau bata da damuwa, bata ankara ba taga keke napep a gefen ta yanai kokarin over taking dinta, tsaki taja ta kuma baiwa motar ta wuta, ta mugun tsanan ayi overtaking dinta, shikam Muhahid sai yiwa mai napep masifa yake akan yayi sauri ya shiga gabanta, wuta Sosai Salma ke bawa mota ayayinda Keke ke binta da Kero, Ranta ya mugun bacci, kwanar Babban high way tabi taga Mai keke baibar binta ba, afusace ta gangara gefen titin hade kashe motar ta fito afusace cin durun uwar sa, tsayar da Napep din yayi gaban motarta sann ya fita da sauri bayan ya biyasa.
Mutuwar tsaye Salma tayi ganin Mujahid, bata iya taku gaba ba, tayi sauri juyawa bakin motar ta bude murfin, nufota yayi da sauri hade da rike murfi.
Amarairece yace
"Salm plz ki saurarani, we need to talk"
Ko kallan shi batai ba ta dauke kai gefe, fuskarta ta daure tamau.
Hannusa ya daura bisa hannunta dake kan murfin motan, da sauri ta zame nata hade matsawa gefe,
Am sorry" ya kuma fada kaman mai shirin kuka.

Wata civic ce tazo wucewa, har tayi gaba tayo baya, maza uku ne suka fito suka tsaya gaban Salma, dayan su yace "Yammata lafiya kuwa ?
Kaman zatayi kuka tace ba "ba lapia ba, wannan mutumin ke takurani
Mugun kallo suka kaima Mujahid, yace "ba wani matsala kanwatace"
Ware ido Salma tayi tace "nikam bansan shiba, mayb ma dan yankan kai ne"
Tsorata Mazan sukayi, aikuwa suka janye Mujahid suka haushi da Duka.
Da sauri Salm ta fada motan hade da sauke ajiyan zuciya, shegen nacin tsiya ta fada aranta, kunna motar tayi ta maida dubanta baya danyin reverse, abunda tagani yayi mugun girgizata, duka sosai Mazan kema Mujahid kaman an aikosu, shikuwa baya da niyyyan guduwa balle tanka su, jibga kawai suke kaman an aiko su.
"Oh my God" ta fada cike da kidema, bude motan tayi da sauri ta karasa gurin su.
"Dan Allah kuyi hakuri ku bari, yayana ne" kaman zatayi kuka tayi magana.
Tsayar da dukan Mujahid sukayi hade da kai mata mugun kallo, dayan su yace "dama yayanki ne kika b'ata mata lokacin tsayawa dukan shi, toh kinyi kadan wallahi, sai kin biyamu dan ubanki"
Iya kidima Salma takai, dagudu ta koma mota tadau jakarta, 2k kadai ke ciki da sauri ta ciro ta mika masu, basu karba ma suka raina, hakuri ta basu fir sukaki yadda, wayar ta iphone 7 ta mike masu tace "kuyi hakuri da wannan, it worth alot of Money"
Tsaki sukayi, suka juyawa suka fada motan su suka ja.
Hankali tashe Salma ta nufi Mujahid dake kwance yana tarin wahala ga jini ta baki da hanci.
Akidime ta d'ago kansa bisa ciyarta, duk ta gama gigita tama rasa abunyi, rokon shi tahau yi akan ya tashi su bar gurin kafin maza su kuma dawowa, tari sosai yahau yi kaman wanda zai shid'e, mikewa tayi ta taimaka ya tashi sannan suka karasa motar ta, baya ta bude ta shigar dashin sannan ta fada gaba taja motar.
Tuki take amma gabad'aya hankalinta na kanshi. Murya sanyaye tace "miyasa baka gudu ba, inda sun kashe ka ya kenan ?
Yunkurowa Mujahid yayi hade da sakin dan kara, hannu yasa ya shafi gefen bakinsa dake jini, dakyar yace "i dont care koda sun kashe ni tunda ke kanki ba kaunata kike ba, gwara na mutu ki daina gani na"
Nisawa tayi tace "ko bana kaunar ka altleast kana da parent, siblings da friends da suke kaunar ka"
Tari ya kuma yi bai iya cewa komai ba.
Ta cigaba "am begging you, don't ever risk your life because of me"
Ciki ciki yace miyasa kikace haka ?
Share tambayan tayi kaman bata jiba, chemist ta tsaya, ta taimaka suka shiga ciki akamai treating ko ina hade da hadomai da magunguna, sun fito ta tambayashi gidansu dan dropping dinsa, can gidansa dake Louis house ya mata kwatance, bata damu ba taja suka kama hanyar gidan, sosai take tausayamai.
Sun iso gidan, ta rikoshi suka karasa ciki, tsoro ne yakamata ganin cewa shi daya ke gidan, dakewa kawai tayi ta zaunar dashi kan one Sitter dake gurin sannan ta ajiyemai ledar maganin gefen.
"Mai kake bukata ? Ta tambaye shi
Ruwa yace yakeso dan shan maganin, hanyar kitchen ya nuna mata ta shiga ta dauko bottle wara tare da glass cup, zubawa tayi sannan ta mika mai, hannun sune ya hade tayi sauri sakar mai da cup din, Murmushi yayi yace "ki zauna mana ?
Kai ta girgiza alaman a'a, bai damu ba yahau shan maganin hade da kurban ruwa, Salma kam kuramai ido tayi tana kallon kyakyawan fuskar shi, dukda some part sun kumbura bai hana kyansa fitowa ba, murmushi ta saki adaidai tym din daya kalleta suka hada ido, daburcewa tayi tahau fadin "xan shiga kitchen wanke hannu" da sauri ta juya ta fada kitchen hade da sauke ajiyar zuciya, saida tayi mintuna Uku sannan ta dawo palom, nanta iske shi yana kokarin mikewa tsaye, ganinta yasashi komawa ya zauna yace "na dauka ko bacci kike ai ?
Kaman marar gaskia tace "a'a ni tafiya ma xanyi" kanta na kallon hanyar fita tayi magana..
Yace "inda na mutu ya zakiyi ?
Sai sannan ta kalle shi, tace "ya zanyi kuwa ? Life goes on"
Kallonta yake saidai this tym around bai fahimci komai game da ita ba, yace,
"Amma miyasa kika taimake ni ?"
Tabe baki tayi tace "friends don't abandon friends".
Lumshe ido yayi yace
"Thank you"
You're welcome" ta fada, juyawa tayi takama hanya fita, bakin kofar ta tsaya sannan ta juyo tace "Get well soon" bata jira abunda zaice ba ta fice.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.