Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 19 of 41
Har kafar Tara su Daddy da jaafar na zauna suna jiran salma, shuru babu labarinta, sau kusan hudu Daddy na kiran wayarta babu respond, ransa ne ya bacci, nan yahau tambayan Mom, cemai tayi skull ta shiga karatu saboda exams da zasu fara, jin shaanin karatu yasanya Daddy yayi calming down, dan yasan lokacin exam Salma bata wasa. shikam Jaafar dadi yaji, amma aransa mamaki yake ace yarinya har yanzu bata dawo ba, jinjina kai yayi "anya ta arziki ce kuwa" azuci yayi maganar.
Hira kadan suka tab"a Daddy yace mai yayi hakuri idan ya dawo daga tafiyar sai yadawo kafin nan diyarshi ta gama exams sai ayi magana, Jaafar kam bai damuba, gaba ta kaishi gobarar titi a Jos, san samu ma kar Daddy ya kuma mai zancen. Sallama yayi masu yabar gida.
Mujahid kuwa shiriritar da Salma yahau yi, bayan tea yayi sanyi k'insha yayi wai zaiyi amai, saida ta kuma had'amai Black tea sannan yadan sha kadan da maganin bayan tasha walaha da lallaba shi sannan ya iya shan pill na magani guda daya, acewarsa daci yayi yawa. Bayan nan kuma ta tashi da niyya tafiya ya langwabe da ciwon kai, saida ta tayi zaman kusan 30 minti tanai mai sannu.. Karshe dai saida yaga 11 tayi sannan ya koma normal, tace mai zata tafi dare yayi, ba kunya yace suje ya kaita gida, itakam mamaki ne ya kamata mutum sai kace mai aljanu, tunani tayi anya ba raina mata wayo yake ba. Haka dai tabishi suka shiga mota, sai janta yake da hira, kasa magana tayi tsananin yadda taganshi garau, wayarta ta duba taga miss calls na Daddy, tsaki tayi aranta tace "Allah yasa banyi ranshi surprise dinnan ba"
Nan baki gate ya sauke ta tamai sallama ta shiga gida, Mom ta tarar zaune palo, dan tuni Daddy ya shiga ya kwanta, ganin Salma yasa hankalinta ya kwanta, fada tayi mata sosai akan dawowan dare amatsayin mace bai kamaceta ba, hakuri Salma ta bata, itadai surprise din takeson sani, tambayar Mom tayi taki fada mata komai sai ce mata tayi bayan exams zataji komai daga bakin Daddy.
***
Washegari langwabewa Mujahid yayi bayan yayi shirin sa tsaf na fita office, Salma ya kira yace ta taimaka ta kaishi office dan baya jin dadi, bata kowa mai aranta ba dukda dai zuciyar ta na kisyasta mata wani abu, kuma jiya taji dadin karatu a office dinsa. Gidan taje ta dauke sa suka tafi.
Tun ranar abu kaman wasa, kullum Salma na tare da Mujahid iyakacin taje skull tayi exam tadawo ta koma office dinsa ta zauna karatu, ko shopping zataje saidai ta zauna shi yaje yayi mata, sam bayaso ta fita ba tare dashi ba gudun kar yan'uwansa su ganta, balle jaafar da har yanxu neman ta yake.
Har azuciya Mujahid yasan ya kamu da son Salma saidai yayi alwashin rama abunda tamai dan kuwa bazai barta taci bulus ba, ganin yadda ta dukufa da karatu yasa ya bata lokaci dan gama exams dinta, ita kuwa Salma zuciya daya take zaune dashi, abu daya ke daure mata kai yadda bai furta yana sonta ba alhalin soyayya kuru kuru yake nuna mata, tanason sani mike zuciyarsa game da ita.
Ta b'angaran Junaina bata daina cusa kai gurin mujahid ba, ko tusa akai a gida saita buga ta fadimai, wataran rohoton sumai amfani wataran kuma data fara fadin abunda bai dameshi ba katse wayan yake. Kullum a rokonshin take ya dawo gida.
Yauce ranar da Salma ta gama Exams, tana fitowa Hall tayi kicibis da Faiza zata shiga next hall supervision, Hararan juna sukayi kowa ya wuce, kowane da abunda yake zak'awa game da junan su aranshi, K'wafa Faiza tayi aranta tace "yar banzan yarinya very soon zai jefar dake".
Tuni Salma tabaiwa banza ajiya, kobi takan Faiza bata kuma ba tq fada mota taja zuwa gida, karfe sha biyu ne lokacin, so take tayi wanka ta huta kafin taje gurin Mujahid tamai albishir din gama exams danba sani yayi ba.
Tana isa gida parking tayi ta fito, kokarin kulle motar tayi taji muryan Salim abayanta.
"Yau kuma baki je wajan sa karuwan ci ba ? Fuska babu annuri yayi magana.
Mamakine ya kamata, ta juyo tace "yaya karuwan ci, a ina, yaushe, ?
Mugun kallo yakai mata wanda daga gani asama yake, cikin zafin nama ya riko hannuta da karfin gaske wanda saida tadan tsaki kara, "ni zaki rainawa wayo Salma, gayamin uban mi kikeyi a office dinsa"
Kokarin kwance hannuta tahau yi takasa, bata rai tayi tace "zan kira Daddy idan baka sake niba.."
Mugun dariya yayi yace "tunda shine ke dauramiki gindin kina iskancin da kikaga dama ko, waya sani ma kokin bashi kanki"
Wani mugun girgiza Salma tayi da kalaman sa, cike da tsantsan bacin rai takai mai azababan mari da dayan hannuta, ba shiri ya saki hannuta yanai mata kallon mamaki lokaci guda kuma zuciyar sa ke tafasa, afuce ta nuna shi da yatsa "idan kana iskancin ka yakare akaina karka kuskura kasako min iyaye, banza, dan akuya kawai, kuma kasani i hate you Mujahid nakeso bakai ba wanda baisan ciwon kansa ba"
Dafe Kunci Salim yayi yana huci, tunanin abunda zai mata kawai yake, Harara ta ballamai, wucewa zatayi yasa mata kafa tayi wani mugun faduwa kasa wanwas, adan tsorace ta daga kai ta budeshi, sosai ta tsorata da yanayin, "anya Salim baya da hankali" ta fada aranta.
Nunata yayi da yatsa yace "ni kika mara saboda da wani banza, aikuwa sai kinyi danasani zan nuna maki ni ba wawan da kike tunani bane" juyawa yayi ya tafi, zuciyarsa na tafasa, shi kadai yasan makircin da zai shuka mata gurin Mujahid din da take takaman tanaso da kauna.
Salma kam tsoro ne sosai ya kamata, mikewa tayi kokarin yi ta kasa zabar azabar dataji kafar ta guda nayi, dakyar da azaba ta mike tsaye, kaman tayi ihu dan azaba, awahale ta iya jan dayar kafar ta karasa cikin gida, bata iya shiga gurin mom ba ta wuce dakinta.
Duk akan Idon Salim, yaji dadin yadda yaga ta kasa takawa, koba komai dole ta hakura da zuwa gurin Mujahid, murmurshin Mugunta ya saki afili yace "zaki gane kuran ki .............
Ni xarah nace Toh Fah, Salma duk ke daya, enemies ta ko ina.
Allah ya karemu daga sharin masu shairi.
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty cute)
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION...
Wattpad Cutexarah
Blog xarahbukar.wordpress.com
51
Tsabar rad'adin da k'afar take mata dak'yar ta cillara ta fad'a band'aki tayi wanka ta fito ta kwanta gado, sosai k'afar tayi tsami haka dai ta daure har bacci b'arawo yayi awon gaba da ita.
Mujahid ne zaune office yana danna na'ura mai kwakwalwa dake gabansa, jifa jifa yakan k'yallarawa agogon tsintsiyar hannusa kallo, guntun tsaki yaja ganin k'arfe daya ta gota bata iso ba gashi kuma ya k'agara ya ganta.
Mubarak ne ya shigo office din tare da sallama, amsawa yayi ciki ciki ba tare daya dubesa ba, Dariya Mubarak yayi hade da zama yanai kallon office din tamkar wani sabon bak'on sa, duban Mujahid yayi, cikin zolaya yace "yau matar ka bata zo ba?
Sai sannan Mujahid ya dubeshi, murmushi yayi.
"Zata zo, na tabbata ma tana hanya"
"taku salon soyayyar daban take, wai ma yaushe zaka rama abunda tama ? Mubarak ya fada ba tare daya bar kyalkyalewa da dariya ba.
Nisawa Mujahid yayi, yace" abokina ina cikin yanayin, na rasa mai zan mata kuma ma bazan iya cutar da ita ba, koba komai yar'uwa tace ta jini, na hakura, yanzu so nake na sadata da Hajiya".
Dakatar da dariyan Mubarak yayi, yace "naji dadi ka gano gaskian zuciyanka, Hajiya kuwa sai tafi kowa farin ciki da kai, yaushe zamuje mu kai amaryar mu gidan sirika.." Cike da zolaya Ya karashe maganar, mugun kallo Mujahid yamai yamike ya fice tare kokarin gitmse dariyar data zomai.
Murmushi Mujahid yayi yadau wayarsa dan kiran Hajiya yi mata albishir, dailing nambar zaiyi, Salim ya fadomai cikin office kamar wani mayunwacin zaki.
Ajiye wayar yayi yabishi da kallon waya baka izinin shigo min office, cikin rashin damuwa da kallon dayake mai Salim yaja kujerar dake fuskantar sa ya zauna had'e da dora kafa daya kan daya, sannan cikin karaji yace "Sir ba batun aiki ya kawo ni nan ba."
Ran Mujahid yakai mak'walan baci, shuru yayi yana jiran abunda zaice.
Salim ya cigaba
"Salma tawace, tare ka fara ganin mu, tun kafin ta sanka muke mu'amala, dan Allah karka shiga tsakanin mu, muna matukar son Juna, adalilin ka yau ta zubar da cikana da take dauke dashi"
Mik'ewa Mujahid yayi, fuska daure, afusace yace "tashi ka fita kafin nasa a cilla ka waje"
"Kayi hakuri sir banxo da fad'a ba" mikewa Salim yayi had'e da risinawa sannan ya fice a office din.
Tsaki yaja ya koma ya zauna ranshi na k'una, ko kadan bai yadda da abunda Salim yace ba, yasan kafin su saba da Salma kallon marar kamun kai yake mata yanzu kuwa d'an zaman da yayi da ita ya tabbatar ba abunda yake tunani bane, kuma ma yasan ba yadda zaai Salma ta kaiwan shashashan yaron nan kanta, tsaki ya kuma ja yace "Salma tafi karfin ka, baka isa ka rainamin hankali ba, wawan banza kawai". Wayarsa ya dauka yahau kiran Salma, sau biyar ya kira tana ruri baaa dauka ba, ajiye wayar yayi zuciyar sa na aiyyana mai abubuwa, saurin kawarwa yayi ya cigaba da aikin gabansa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.