Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 18 of 41
Alokacin kuwa had'e book dinta Salma tayi cikin jakarta sannan tabar dakinta, gurin Mom ta shiga ta mata sallama ta fito cikin sauri, library na skull takesan zuwa karatu saboda jibi ne zasu fara exams.
Kokarin bude motar tayi taga kiransa, murmushi tayi ta dauka.
Daga can Bangaran cikin sweet voice dinshi yace "Angel of my life, son kowa kin wanda ya rasa"
Dariya tayi kasa kasa, tace "ka fara koh, how am i even sure am your angel"
Yace "believe me, ba karya nake ba, idan ma baki yadda ba God knows it.
"Kaga ni library zani, inada exam jibi, kana ina?
Yaji dadi abunda tace, aranshi yace "perfect, nasan abunda zanyi"
Afili yace "ina driving, ki jirani nazo nayi picking dinki saimuje inda babu wanda zai dameki dan kisamu kiyi karatu, nasan ki da tsokana kar kije kiyi dambe da mutane a library" karashe maganar yayi cikin zolaya.
Shagwabe fuska tayi kaman yana ganinta, tace "nifah bani da tsokana, ko dambe ban taba yibaaa.."
"Hmm, kedin, ki jirani am coming" katse call din yayi, ta fita can bakin gate jiran shi, baafi 20 mins ya karaso ta shiga motan ya kama hanyar office dinsa, tagane hanyar, tace "lailai ma office dinka ne bazaa dameni ba?
Wani shumin kallo yayi mata da saida taji shi a kwakwalwar kanta, murya kasa kasa yace "duk wanda ya dameki cikin cell zan wurga shi..
Ware ido tayi adan tsorace, "cikin cell sai kaca a film"
Dariya yayi bai kuma cewa komai ba ganin yadan tadan tsorata, suna isa parking yayi, suka fito suka shiga elevator har zuwa cikin office dinsa, ita batama san akwai elevator ba kasancewar ta stair security yabi da ita kwana kin baya.
Office din babba ne mai shegen kyau can gefe inda Couch da center table yake takarasa ta zauna shi kuma yA karasa gurin table dinsa ya zauna kan kujerar sa hade da fara aikin danna laptop din gabansa, sosai yaci serious da abunda yake batare daya dubi Salma ba.
Itakam abunda take so kenan, bude handout dinta tayi ta dukafa da karatun General studies da suke dashi.
Bayan kaman awanni uku Mubarak ya shigo office din, ganin Salma yasashi dariya, zama yayi gurin mujahid yana zolayar shi murya kasakasa, b'ata rai Mujahid yayi, yafara magana cikin fad'a, duk ahankali suke magana, Salma bataji komai ba kuma bata damu dason jiba, sund'an jima sannan Mubarak ya fice office din.
Gyaran murya yayi, Salma ta dubeshi
Yace "bani labarin samarin ki ?
Dariya tayi
"Banda saurayi, infact ni bana soyayya"
"Miyasa ?
Ajiye pen din hannuta tayi hade da yin tagumi, amaraice tace "Sanadin So Ummata tasha wahalan rayuwa, daga karshe ma Abbana ya rabu da ita da tsowon ciki, bansan lokacin ba, bansan anyi ba amma ayadda naji labari yadda komai ya faru yasa kwata kwata na cire so araina"
Kallon tausayi yayi mata, tunda yake gida bai tabaji labarin Ummanta abakin Hajiya ba, saidai zaiso sani..
Kaman wanda baisan da rasuwan Umman ba yace "ina umman take ?
Kaman zatayi kuka tace "ta rasu, lokacin daban santa ba, i was 3years old tym din".
Maida dubansa Mujahid yayi bisa laptop din yace "bai kamata ki cire so aranki ba, tunda iyayan ki daban ke daban"
"Hmm, am sacred banso ayi breaking heart dina"
Shuru Mujahid yayi baice komai ba, bayason cikata da surutu, bari yayi sai kuma gobe ya kara jeho mata wata tambayar.
Cigaba da karatun Salma tayi, lokaci Sallah azahar nayi ya nuna mata toilet dake office din sannan yafice zuwa masallaci, bayan ya dawo ya tura aka kawo wa salma abincin take away, godiya tayi.
Karfe bakwai Daddy ya dawo Gida, nan ya tsarawa Mom batun zuwan Jaafar, sosai taji dadi da batun daddy dan kuwa ta kagara Salma tayi aure ko zata nutsu, nan daddy ya shaida mata bayan Sallah Isha'i Jaafar zaizo ganin Salma, dadi sosai taji, wayarta tadauka dan kiran Salma.
Bayan Salma ta idar da sallar Magrib, Qur'an dake ajiye a office din tadau ta karanta sannan ta ijeye ta cigaba da karatunta, lokacin Mujahid yafita masallaci bai dawo ba, kirar Mom tagani tayi azaman dauka.
Aladab ce ta gaidata, Mom ta amsa sannan tace "Salma kibar duk abunda kike kidawo gidan yanzu nan, Daddy zai baki wani Surprise"
Farin ciki ne ya kamata, tace "momy miye ne, dan Allah gayamin i cnt wait saina zo"
Dariya momy tayi tace "idan kinason sani kizo maza yanzun nan, kuma kiyi sauri" katse call din Mom tayi, cike da Murna Salma tahau tattare books dinta ajaka, Mujahid ne ya shigo, ganin tana hade komai yace "keda kika ce sai 10 zamu tafi, kin fasa ne ?
"Eh nafasa, kaini Gida" cigaba tayi da hade komai zuciyar ta fal murna.
8.20 Jaafar ya iso gate din Gidan Daddy, bai tab'a zuwa gidan ba yasa yakira Daddy awaya dan tabbar da gidan ne, nan take Daddy ya kira mai gadi aka budewa mai gate ya shigo gidan, cikin palo gidan Daddy yamai iso, ya shiga yagaida Mom aladabce, sosai mom ta yaba da hankalin sa, sun gaisa sosai, mai aiki ta kawo mai na shasha baki, shikam Jaafar gaban sane keta faduwa, har yayi dana sanin kowa kanshi gidan.
Mom kam murmushi kawai take tana saurara isowan Salma....
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
®NWA
43 - 50
Murmusawa Mujahid yayi ganin yadda take cikin walwala. Table dinsa ya k'arasa yadau wayarsa tare da mukulin mota. Ficewa sukayi daga office suka nufi ma'ajiya motar, Salma na tafe tana waya da Mom, cikin sauri tayi gaba ta tsaya bakin motar. Wayar sace tayi ruri, ya duba yaga Junaina da kuma miss call datai mai wanda bai lura ba sai yanzu, tsaye yayi nan inda yake batare daya karasa inda Salman take ba ya dauka.
"Little sis ya ake ciki ?
Kaman munafuka Junaina tahau duben ko ina a palo gudun kar wani yajita, murya kasa kasa tace "yayA naga ya jafs ya fita, kuma naji yana waya da wani zaije ganin wata yarinya, i dont know wace yarinya ce"
"Yaushe ya fita ?..
"Yadan jima kuma bai cewa Hajiya Komai ba"
"Okay Sis, ki cigaba da samai ido, i'll call you later" katse call din yayi ya karasa motan suka shiga, sai sannan ya tambayi salma dalilin tafiyar ta, bata boye maiba ta fadi mai Mom ke kiranta kuma it urgent.
Shuru Mujahid yayi yana tunani anya ba gidansu Salma yaje ba, wata zuciyar tace it cnt be possible, miye zai kaishi gidan, saidai surprise da Mom zata bawa salma ne ya tsaya mai arai, zuciyar sam bata aminta da hakan ba, kuma baiji yana son tafiyar Salma ayanzuba. Kallonta yayi da gefe ido yaga tana latsar wayarta fuska ta dauke da murmushi..
Murmushi yayi sannan yaja wani wawan burki da saida ta tsorota, afirgice ta kalle shi, gani tayi ya daura kansa bisa steering hannusa dafe kan gefen cikinsa, murkutsutsu yahau yi tamkar wanda zai mutu.
Tsabar gigita bata san sanda takai hanunta bisa bayan saba tanai tambayarsa maike damunsa, kasa magana yayi banda cije labb'a da yake, fita tayi motan ta zagayo gurin sa. Tambayarsa ta kuma tayi, murya ciki ciki yace "am sick, can you drive ?
Kai ta gigiza alamun eh, taimaka mai tayi ya koma dayan sit din sannan ta shiga taja motar.
Kaman mai shirin kuka ta kalle shi, "wana asibiti zamu ?
"Kaini gida kawai" ya fada yana lumshe ido, shingidewa yayi akan sit kaman wani marar lapian gaskia.
Hankali tashe tahau driving ba tare data tuna kiran da Mom ke mata ba, suna isowa gidanshi ta taimaka mai suka shiga ciki ayayinda sai faman cemai sannu take, shikam dariya ke cinsa yana gimtsewa. Zaunar dashi tayi kan two sitter sannan ta dube shi, murya cike da tausayi tace "sannu yaya.."
Yi yayi tamkar baiji taba saima rufe ido dayayi, itakam tanason tafiya ga dare yafara lulawa, gyara zama tayi ta fuskan ceshi tanai karemai kallon aranta tanai kara jin sonshi. Sunkai 20mins ahaka kafin nan ya bude ido, suna kallan juna, lumshe ido yayi yace hado min tea nasha magani"
Ba musu ta mike ta shiga kitchen ta hado ta kawo mai, k'insha yayi ya ajiye akan yayimai zafi da yawa, zama tayi tanai jiran tea yayi sanyi tanason tafiya saidai bata iya barin sa cikin larura.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.