Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 1 of 89
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
Page 1&2
Bismillahirramanirrahim
Wasu k'wawawan motocine masu rai da lpy ke tafiya akan shimfidedden kwaltan dake unguwar London road dake garin minna,
Duk Wanda yasan unguwan London road. Yasan unguwace ta manyan mutane .musamman manyan yan kasuwa,
Kofar wani katafaren gida motocin nan sukayi parking gidane mai kyau. kuma ga dukkan alamu sabon gini ne ba a kai ga tarewa cikin saba,
Ahankali marafen motocin suka fara budewa. Mataye ne suka fara fitowa daga cikin motocin nan.
Yawancin matayen sanye suke da ankon wani hadadden atamfa yellow and brown colour. wasunsu kuma sanye da shiga ta alfarma,
Saida suka gama fitowa kaf d'insu na lura da wata mota guda daya daga cikin motocin nan wadda ba a bude ba balle a kai ga fitowa daga cikinta,
duka matayen nan tsayawa sukayi suna kallon motar nan. da alama jira sukeyi na cikin motar su fito ,
Marfin motar ne ya bude. A hankali wata dattijuwar mata da akalla zatakai shekara hamsin da haihuwa ta fito a motar cikin shiga ta alfarma. Sai kuma wata ta bude gaban motar ta fito ita muka sanye take da ankon dake jikinyawan cin matayen,
Hannu yar dattijuwar data fara fitowa a motar ta miqa ta kamo hannu waccce ta rage a cikin motar.wacce nake tsammanin duka matayen nan ita suke zaman jiran fitowarta ,
A hankali ta sako fararen qafafunta waje Wanda yasha wani irin design na black and red henna.
dai dai lokacin wasu daga cikin matayen nan suka saki bud'a ji kake "ayyiririririyyyyyy" wuri ya haustine da bud'a gwanin birgewa,
Sai alokaci na fahimci meke faruwa a wurin wato dai amaryace aka kawo sabon gidan nan
A hankali na qare ware idanuna akan amaryan sanye take da wani ubansun lace maroon colour mai duhu Wanda yayi masifar yima farar fatarta kyau an lilla'be mata kanta da wani babban mayafi peach colour kafarta da yasha design sanye da takalmi mai tsini shima peach dukda banga fuskar ta ba nasan wannan amaryar masha zatayi kyau ba qarya,
Matan nan biyu da suka fito mota daya da itane suka sanya ta a tsakiya suna nufar gidan sannan sauran matan suka rufa musu baya.
Dai dai get suka tsaya wannan dattijuwar matar tana karanta mata wani addua tana amsawa cikin sanyin muryarta daya shaqe tsabar kukan da tasha,
Da bismilllah ta sanya qafarta cikin gidan . wasu matane suka taso cike da fara,a suka tarbesu har cikin babban plat din dake farkon gidan
Masha Allah ginin bene ne babba Wanda ya gama tsaruwa kamar a Turai an qawatashi da kayan more Rayuwa na alfarma , saida suka sadata da bed room dinta dake upstair sannan suka firfito wasu suka zauna a falonta na sama wasu kuma suka sauqo kasa.. Nan aka gabatar musu da abincin tarbar amarya mai rai da lafiya kowa yaci abinda ranshi keso ya qoshi . nan dai wasu suka zazzaga gidan .. Gidan kam ya hadu sai sambarka
Amarya kam tunda suka sadata da bed room dinta suka zaunar da ita a gefen bed dinta kanta me duqe lilli'be da mayafinta . kuka takeyi sosai kamar ranta zai fits sai shesheqa takeyi kamar zata shiqe. Ita kadai tasan abinda me damun zuciyarta game da wannan qadddararren auren ..dasun San halin da take ciki game da wannan auren da dukkansu sun tayata kukan baqin ciki,
Dama ace zata iya bijirema Alhj baba akan wannan auren hadin daya hada data bijire mai,
Saidai kuma kash ko giyar wake tasha bazata taba iya bijire masa ba , saidai mijin da aka aura matan ya kasheta kamar yadda yay ikirarin cewa. tayarda ya kashetan akan ta zama butulu gurin bijirna umarnin alhj baba..
Tunaninta ne ya katse jin motsin mutane suna nufowa dakin da take domin yi mata sallama .
shigowa suka dingayi suna mata sallama da fatan alkhairi wasunsu na mata addua da tayata farin ciki yayinda wasu zuciyarsu kamar tayi bindiga ta fashe don tsananin baqin ciki .
Wani kukane ya
kufce mata ganin da gaske tafiya za suyi su barta a cikin wannan baqin gidan da ta tabbata shine ajalinta,
Rarrashinta suka shiga yi da bata baki yayi da masu Jin haushinta musamman yan matan dake son auren mijin nata dakuma wadanda kema yayansu ko kannensu kwadayin auren wtakeyiba
ya'kyawan santalelen matashin saurayin mai ji da kudi ga kyau ga 'kuruciya, ke mata kallon wawiya wacce batasan abinda takeyiba
Shere and comment
FisabilillahðŸ™ÂðŸÂ»
💖DAMA TA BIYU💖
BY
{AYSHA NALADO}
FREE BOOK
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.