Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 45 of 89
Page 81 & 82
Tun daga farkon layin gidan alhaji baba har karshen sa motoci ne laye iya ganin mai hange, wanka amare sukayi mami da kanta ta shirya su shirin barin gida, sai sharar kwalla sukeyi, Asmah kam da yake bata da lafiya wata kanwar mahaifiyar ta da suke uwa daya uba daya , da suka zo biki, ita ta mata wanka ta shirya ta har zuwa lokacin jikin da zafi kau.
Bayan sun idar da sallan magriba, ummi har falon alhaji baba ta musu rakiya, acan suka samu daddy da Abba da sauran yan uwa da abokan arziki, zubewa su kayi a tsakiyar falon kowacce kanta a kasa tana hawaye, alhaji baba ya fara buÉ—e taro da addu'a, kafin ya daura da nasiha mai ratsa jiki take jikin su ya kara sanyi, bakajin sautin komai a falon bayan amon muryar alhaji baba sai shehsshekan kukan amare, yana gamawa, Alhaji Mallam ya É—auka daga nan sauran abokanan su kowa saida yasa musu albarka, Daddy da Abba ma sun musu nasiha sosai.
Daga nan wurin hajiya mama aka kaisu, itama ba'a barta a baya ba, haka aka ta bi dasu, suna sallaman dangi, mummy kam ɗakinta ta shige ta ɓame, koda ummi ta tura ƙofar dakinta taji shi a rufe a waya ta kirata wai tana inane amare zasuyi sallama da ita, jin haka dama abinda take dugarma ke nan, sai cewa tayi bata cikin gidan su tafi kawai Allah ya bada sa'a.
Mutane Æ´an zakiyar amare tuni kowacce ta samu mota ta kame, Æ´an dama ta biyu fans haka suka lodu cikin motoci wasu kan cinyan wasu, wasu ma har a boot, nima allah ne ya soni har zan shiga boot dan ban samu guri ba ,kiy kurs ta yafito ni na zauna a cinyarta, su kakus dai ana boot ido ya raina fata, tare za'ayi tafiyar' ma'ana zasu raka junan su, za'a fara kai batool daga nan akai Asmah, sai Amira, sai kuma a zarce bidda inda za'a kai zahra,. Kowacce motar da aka kawo na musamman domin ta aka nufa don sakata saidai hakan bai yuwu ba , dan zahra da batool kam kankame juna sukeyi , suna wani irin kuka mai ban tausayi ganin haka yasa dole aka saka su a guri É—aya,.
Gidan batool aka fara zuwa dake nan M,I sauka akayi aka shiga da ita gidan sama ne dankarere Wanda misalta muku shi bata lokaci ne, sabo dal haka ma kayan cikin gidan sababbi ne, ga kuma sabuwar amarya, da sabon ango,Abin zad dadi,.
Bayan dangin Dr bash waÉ—anda da suke nan dan kar bar amarya sun karbe ta, abincin tarbar amarya mai rai da lafiya aka gabatar musu kasancewar suna sauri yasa suka saka a mota idan an koma gida aci,.
Tashi aka shigayi ana fitowa domin tafiya, nan fa kallo ya koma sama dan amare dai kamkame juna sukayi su hudu suna sharban kuka, da'ker aka samu aka banbare su daga jikin juna,.
Kasancewar basu da wasu kawaye sosai yasa wasu kawayenta sabbi ne ma dan a school ta haÉ—u da su su biyu suka tsaya da ita zuwa sanda ango zai shigo suma su san nayi a bar ango da amaryarsa,.
Ganin abinda sukayi a gidan zahra yasa lokacin da suka isa gidan Asmah, ba'a bari Amira da zahra sun fito daga mota ba, a nan aka barsu aka shiga aka mata rakiya,.
Itama dankarern gida ne mai girman gaske don yayi Na batool biyu, saidai shi part uku ne a gidan dan haka aka lalubi nata aka sakata, itama sabbin kawayenta ne suka tsaya da ita,.
Haka aka garzaya gidan Amir dake albishir, daga nan kuma waÉ—anda zasu koma gida suka koma waÉ—anda zasuyi rakiya zuwa bidda kuma suka dauki hanya, saidai muyi fatan Allah ya kaisu lafiya,.
nikam dai bani cikin yan zuwa bidda dan allah allah nakeyi naje gidan batool naga ya zasu kwashe da dr bash, harna kama hanya na ni kaÉ—ai zan tafi, na dawo cikin sanÉ—a na yafito ummu muhammad naser, na mata kuskus a kunne, itama saÉ—aÉ—owa tayi ta biyo ni, ganin haka yasa ameera dake ankare da duk wani motsin mu yasa ta biyo mu a baya da gudu ba yacce muka iya dole muka tafi da ita.
Bari mu fara da mutuniyar taku😜
~BATOOL~
Bayan wucewar su ummi kukanta taci gaba da rerawa, kawayenta sai tsiya suke mata, ko kulasu batayi ba, wata matashiyar mata ne ta shigo cikin dangin ango waɗanda suka amshi amarya da basu kai ga wucewa ba zama tayi a bakin gadon da batool ke zaune can kurya sai sheshshekan kuka takeyi, kasa kasa, hannayenta ta miƙa ta kamo na batool ta rike cikin nata tana dan murzawa a hankali, jin haka yasa batool ta ɗago kai a hankali ta sauke idanunta akan matar matashiya ce don duka duka baza ta haura talatin ba, tsananin kamar ta da Dr bashir yasa batool ta raya a ranta duk yadda akayi kanwar shi ce, murmushi mai kayatarwa ta sakar mata, a hankali cikin sassayan muryarta tace"haba amaryar mu wannan kuka haka sai kace sato ki mukayi, oya ki daina kuka haka bana son yaya yazo ya same ki haka bazai ji ɗaɗi ba, kinsan yadda yake sonki bazai so ganin hawaye a idanunki ba, nasan kina kukan rabuwa da family ɗinki ne ko," gyada mata kai batool tayi, ido jajur ansha kuka, taci gaba da cewa "to kidai na kuka jinki, insha Allah mu zamu zame miki sabon family masu kaunar ki zakiji dadin zama da mu ƙilama fiyye da naki familin" dagowa ta sakeyi ta kalleta jin tace wai fiye da familin ta, murmushi ta mata tace "eh mana nan gaba zaki tabbatar da abinda nake gaya miki, kedai kawai ki kula mana da babban yaya,kuma sai kinyi hakuri kin zama jaruma,kinsan yaya na tuzurune sai a hankali" daga bakin kofa suka ji wata murya shigen na wannan tana cewa "yayi kyau zubaida, kuma kamar a kunnen yaya kika faɗa , ba tuzuru ba, shuka kikai a idan makwarwa, zuwa zañyi nace kinje kin samu amaryar shi kina ta tsoratata harda cewa idan bata bika a hankali ba sai ka dinke ta kamar kwarya" kwalalo ido tayi tare da cewa " dan Allah yaya amrat ki rufa min asiri yadda yake dokin amaryà n nan, wlh kina faɗa yarda zaiyi kijamin bakin jini ɗan alert din da nake ji karshen wata kisa wannan watan nan naji wayam," Dariya yaya amrat tà kwashe dashi, tace"to cigaba da tsoratar mai da mata, Allah zan saka ya saka ki a black list wannan month din, oya ki taso mu wuce anzo daukar mu".
Kallan batool tayi tace "amaryan mu zan wuce anzo daukar mu,amma zan dawo very soon, ni sunana ashmat, sister na kuma amrat dukan mu kannen Dr ne amrat ke binshi a haihuwa sannan ni, dukkan mu matan aure ne amma akwai sauran kannen mu mata su uku, zaki sansu very soon, autar mu ma kila kuzo mate da juna, dan Allah a kula mana da yayan mu muna sonshi sosai shi kadai ne namiji a cikin mu,"sake hannun batool tayi saida ta kai bakin kofa kusa da yaya amrat tace "amaryan mu a buɗe ma yayana ƙafa da kyau anjima fah" dariya kawayen batool suka kwashe dashi, yaya amrat kam kunnen ashmat ta kama ta jata, suka fice tana cewa"kedai bakin nan naki har yanzu bazai tsarkaka ba ko?".
Batool manya wata uwar harara tà raka su dashi,tare da jan wani dogon tsaki tace"A'a ba ƙafa zan buɗe mishi ba baki zan bude mishi, iskancin banza kaii" cikin dariya daya daga cikin kawayen ta tace"bakin ma inta kama ki bude, budewan zakiyi" aiko dai nan batool ta hayayyako mata da masifa kamar zata cinye ta ɗanye, haushin su ashmat data kunsa duk ta sauke shi akan ta, suko kasancewar sunsan halin mutuniyar yasa basu kulata ta ba saima dariya da suke mata saida tayi mai Isar ta tayi shiru.
Ita yanzu duk Wanda ya shafi Dr bash haushin sa takeji, balle kuma Wanda zaice tamai biyayya, ji take kamar ta shake mutum, shi karan kanshi jiran shi take yi dan ta kudiri aniyar antaya mai bahon rashin mutunci a ka , har sai ya gaji da halin ta ya maida ta gidan su, tunda dai ita bata Ce tana sonshiba,.
(Hmmmmm nikam dai nace batool abi a hankali yanzu dai gidanku daya da Dr Allah yasa ya iya jure rashin M dinki, kada shima ya miki kalan nashi rashin M d'in).
Su ashmat na wucewa, motocin abokanan ango suka fara dira a compound d'in gidan, falo kawayen batool suka fito, su biyar ne harda angon, samari yan kwalisa, sunsha wankan shadda sai tashin kamshi sukeyi , bayan yan gaishe gaishe da addu'o'i zaman lafiya, akayi siyan baki , aka dan taba wasa tsakanin abokan ango da kawayen amarya, nan sukace tunda sun siya baki a fito musu da amarya su gaisa, Dr bash yace "wata amaryan za'a kira muku ku gaisa, abeg ku tashi na rakaku jooo, koni banji muryar ta ba tukun saiku gandan gandan daku"dariya suka saka suna cemai yayi duk abinda yaga dama zasu rama ne,daya daga cikin su yace dan allah dr abi mana ƙanwa a hankali fa.
Rakiya ya musu suka tafi tare da kawayen batool d'in zasu sauke sua gidajen su
Batool kam tun jin shigowar su kawayenta suka fita mikewa ta yi ta shiga toilet tayi wankan ta ta fito ta É—auki kayan bacci Riga da wando ta saka ta faÉ—a gado abinta ta kwanta, acewar ta ita ba amarya bace tunda auren dole aka mata da mijin ba sonshi takeyi ba,.
Dr bash na dawowa ya buÉ—e bayan boot ya fito da tsarabar amarya da abokan shi suka siyo, ya nufi dakin amaryar a falo ya ajiye ledar shi ya nufi dakinta da addu'o'i fal bakin shi.
Tsaya wa yayi a bakin bedroom din da yake da tabbacin tana cikin sallama ya shiga yi a hankali, shiru ba amsa , har yayi so uku ganin haka yasa a hankali ya murda handle din kofar ya shiga gaban shi na faduwa dan baisan mai zai tarar ba, dakin duhu ba haske wayar shi ya laluba ya haska ya kunna wuta mai haske, a kan gadon ya hangota kwance ta gudun dune da bargo baka ganin komai nata sai fuska, "ikon Allah" Dr bash ya furta a zuciyar shi, ya saba kallo ko a film amare lullubi suke sha ango yazo ya bude musu fuska, amma shi tashi amaryar ta fita daban da sauran amare,.
Duk sallaman da yake ta kwadawa tana jinshi ta share,saidai ta amsa a zuciyar ta,jin ya kunna wuta yasa ta bude idanunta da sauri, sai cikin na bash kallon kallo aka shiga yi, ba komai ya fado mata a rai ba sai zanan da mummy ta mata ranar da ta hau iskan karya, take wani haushin shi ya kara turnike ta, Daga kwancen da take tace"lafiya Mallam?" bai tanka ba sai karaso wa da yayi bakin gadon zai zauna ta wani zabura ta karasa can karshen gado tana antoyo mai harara, shi dariya ma ta bashi amma ya dake baiyi ba, zaman yayi abinshi, yana kallonta, shiru ya ratsa na wasu mintuna shi yana kallonta ita kuma tana hararan shi, can dai yace "ke baki iya gaida mutane bane, ko haka aka ce miki ana ma miji," cikin tsiwarta tace "mijin wa Allah ya kiyaye nidai kai ba miji na bane ehee , tun wuri ka nemi matarka dan ni ba sanka nake ba auren dole akayi min" bash yace"to nima sonki nake aka gaya miki , mace sai muni haka , bari na gaya miki abinda baki sani ba, ina zaman zamana Alhaji baba ya kirani, da nazo yace, wai ga batula nan dan Allah na taimaka na aure ta tayi kwantai duk , yan uwanta an kawo kudin aurensu amma ita bata da mashin shini na taimaka, ganin bazan iyamai musu ba yasa na karba, badan inaso ba don ni inada budurwata Fateema, da muke soyyaya ita zan aura, amma tunda an riga an manna min ke dole haka zamu hakura mu zauna da juna mu hayayyafa, kila albarkacin ƴaƴan naji na dan fara sonki kaɗan" batool da tunda ya fara magana bakin ta ke bude tana binshi da kallon mamaki jin abinda yace wai su hayayyafa bata San sanda tace "kutumelesi, kaida wa zaka hayayyafa, to wlh ahir dinka karma ka taɓa tunanin ko yatsar hannunna zaka samu tabawa balle jikina, balle har ta kaimu da haihuwa, jikina rabon masoyina ne , ba wani ƙato ba, " tunda ta fara magana dan bakin ta yake kallo yadda take masifa tana wani tsuke shi ba karamin burge shi yake yiba,aiyana irin taushin da lips ɗinta zasuyi in ana kissing ɗinsu yakeyi, zuciyar shi ce ta bashi shawara da cewa yaudai gaka ga wannan ɗan bakin da ke hanaka sukuni, kadan tsotsa mana ka rage zafi, kallon ta yayi yace" tunda dai baki da masoyin yanzu jikin naki ya zama raboda ai tunda na biya sadaki bari ma ki gani" mika hannu yayi zai riko ta, aiko ta daka tsalle ta dira daga gadon zatayi waje da gudu, fisgota yayi ta faɗa jikin shi baiyi wata wata ba ya hade bakin shi da nata ya shiga kissing dinta cikin wani irin salo mai birkita tunanin ɗiya mace,.
Wohohoo Dr bash an samu abinda aka dade ana mafarkin samu, gaba daya wutar kanshi daukewa yayi, yadda yake tunanin zakin saliva din ta abin ya wuce haka, yadda yake tunanin laushin lips dinta abin ya wuce haka, uwa uba yadda yaji taushi da tsantsin fatar ta ga wani mahaukacin kamshi dake fitowa daga jikinta yana shiga hancin shi, ai sai ya birkice mata gaba daya,.
Ita kam batool da farko tsoro ne ya kamata , tunda take ba'a taba kissing dinta ba sai yau, tanajin kiss a baki amma bata taba sanin haka yake ba sai yau, da farko kokawar kwatar kanta ta shigayi amma da yake ba rikon wasa ya mata ba yasa ta kasa kwacewa , da tafiya tayi tafiya lukusss tayi a jikin shi tana amsan sakon da yake aika mata, (maganin hajiya addawiyya na aiki),.
Bashir kam gaba daya ya fita daga control, shida yayi niyar kiss sai gashi yana neman wuce gona da iri, tuni ya fara kai hannunshi sassan jikin ta, rigar jikin ya shiga kokarin zarewa , jin haka yasa hankalinta dawowa jikinta kuka ta fashe dashi tana ci gaba da kokawar kwatan kanta, zuwa time din jikin shi gaba daya ba karfi, hakan yasa tayi nasaran kwatar kanta a dis time, toilet ta nufa ta rufo kofar da karfi ta jingina bayanta a jikin kofar tana maida nunfashi,.
Dr bash kam kifa wa yayi ya kwanta akan bed din ya runtse ido yana sauke ajiyar zuciya, hannunshi ya mika ya kama ya kama AK47 dinshi jin yadda take harbin iska,.
Saida ya kwashe kusan thirty minutes a haka, kafi ya yunkura ya mike ya fice daga dakin gaba daya,.
Madam batool kam saida ta gama maida numfashi, hankalinta ya gama dawowa jikinta , taji yadda lips dinta ke mata wani irin raÉ—aÉ—i, gaban mirror dake tsaye a toilet din ta karasa gani tayi lips dinta yayi jajur, gashi ya dan kumbura, kuka ta fashe dashi tana shafa lips dinta, ruwan dumi ta hada tayi wanka tanayi tana ma bash Allah ya isa, data gama ta fito ta canja wasu kayan bacci ta hau gadon ta ta kwanta tana mastar kwallah,.
Bash kam wani bedroom din ya shiga , tube shaddar jikin shi daya gama cukurkudewa yayi ya fada toilet, wankan janaba yayi sannan ya daura dana sabulu, yana fitowa shiryawa yayi cikin kayan bacci dogaye, ya lallaba ya koma É—akin batool, dan shidai bazai yarda da kana wani É—aki matar ka na wani ba,gara su saba kwana tare tun yanzu,.
Yana shiga ya sameta can karshen gadon kudun dune cikin bargo, duk da cikin duhu ne hakan bai hanata antaya mai harara ba, ganin ya kwanta a daya side din yasa tayi wuf ta dauki pillows ta jera a tsakanin su, asuba ta gari , amarya da ango.............
nikam nida yan rakiyana ummu muhammad naser da ameera, ganin sun kwanta yasa muka lallaba muka hito bakin titi dare ya tsala aiko daƙer muka samu napep, gulma yayi ɗaɗi😜
Toh mutanena gobe da wani gidan zamu fara ne, gidan Aslam ko gidan kamal ko Amir, kokuma bidda zamuje?
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
FisabillilahðŸ™
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.