Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 13 of 89
Page 21 & 22
Haka rayuwa yaci gaba da tafiya, tsakanin Aslam da Asmah kuwa babu abinda ya canja saima abinda ya qaru, tunda ya dawo walwalarta a gidan gaba d'aya ya ragu ba qaramin uzzurama rayuwarta yakeyi,
Saida ya cika wata uku cif da dawowa ya huta sosai har ya kama aiki a daya daga cikin kamfanonin Abba a matsayin general manager na kamfanin,
Alhaji baba ya kira dukkan yayanshi ya gaya musu qudirinsu shida aminshi Alhaji Mallam akan son had'a Asmah da Aslam aure,
Dukkan su sunyi farin ciki sosai saidai daddy ya kawo qorafin maganar karatun Asmah d'in, nan Alhaji baba ya sanar dasu yadda suka yi da Alhaji Mallam ranar da zai dauko Asmah na cewa baya son tayi karatun boko ya wuce secondary, dukkan su sun gamsu duba da yanayinsa na babban malamin addini, shike ma wasu fadan su aurad da yayan su in sun kai minzali kunga ai bazai bar nashi ba,
Sosai mummy taji d'ad'in wannan maganar don dama tunba yau ba takeda wannan buri ,
Nan Abba ya sake kawo maganar ko Aslam da Asmah din suna son juna , nan Alhaji baba yace ko basu son juna sai anyi wannan lamari saje can su daidaita, abar komai a hannunshi shi zai sanar musu da kanshi, nan dai meeting ya tashi kowa zuciyarshi fal farin ciki domin Asmah yarinyace nutsatsaya mai hankali da duk wasu iyaye na gari zasuso ta kasance surika a garesu
Alhaji baba da Aslam zaune suke a sitting room din Alhaji baba , fuskantarsa Alhaji baba yayi yace "Muhammad Aslam ba komai yasa na kiraka ba sai domin inason muyi wata magana dakai mai muhimmanci kuma na fahimtar juna, inason kabani aron dukkan hankalinka nan ,". gyada kai Aslam yayi yace "ina saurarenka alhaji" nan alhaji baba ya shiga sanar dashi abinda suka yanke nason hada shi aure da yar uwarshi Asmah cikin kwantar da murya alhaji baba yake mai magana da lalama,,... Tun kafin alhaji baba ya gama jawabinsa gaba daya aslam ya jiqe da zufa duk sanyi AC daya cika falon kuwa , qure alhaji baba yayi da ido kamar ranar ya fara ganin shi, daqar ya bude baki yace meyasa saini zaku aura ma ita meyasa bazaka aura mata wani cikin jikokinka ba , naga dai bani kadai bane jikan naka ai, to ni baba so akai kasuwa, idan hada zuri'ar Allah da annabi za ayi a aura mata kamal mana ko amir naga ai suma jikokin kane, kuma suma sun isa aure, to barin gaya maka gsky mallam tsoho bana son yarinyarnan bana kaunarta bata cikin tsarin matan da nake burin yin rayuwar aure dasu, don haka kayi gaggawar kwance wannan kullin da kayi , donni inada wacce nake son aura, wayyayya mai aji yar boko ba irin wannan kucakar yarinyar ba,"yana gama fadin haka ya miqe ya fice daga falon a fusace,
Alhaji baba da mamaki ya gama kasheshi a zaune kasa ma magana yayi tunda yake wani daga cikin jikokinshi bai taba mai rashin kunya irin Wanda Aslam ya masa yau ba , shiru alhaji baba ya zauna yanata saqe saqe a zuciyarshi kafin daga bisani ya saki wani qayatatccen murmushi a fuskarshi bayan ya samarwa kanshi mafita,
Aslam ranar daqar bacci ya daukesa bayan ya samarwa kanshi mafita yasan tunda alhaji baba ya fara wannan maganar to sai ya aiwatar,yasan tsohon da hegen nacin tsiya , don haka ya qudurci zai samu Asmah ya buga mata kyakkyawan warning akan karta kuskura ta amince da wannan hadin, yamasan ita karankanta baza tayi gogin amin cewa da auren shi ba,
Haka aka ci gaba da shirye shirye Asmah bata da labari , su zahra kam sunji lbr saidai ba wacce tayi qarfin halin sanarda asmah a cikinsu , don su karan Kansu ranar da suka fara ji abin ya matuqar firgitasu ya basu tsoro don su kadai sukasan irin tsanar da Asmah da ya Aslam sukai wa juna....
An tsaida lokacin biki nan da wata daya masu zuwa, alhaji baba ya tura Asmah gidan alhaji Mallam tace ta musu kwana biyu kuma ta duba jikin Mallam din Dan kwana biyu baiji dadi ba, da murnarta ta shiya kayanta don ta kwana biyu rabonta da gidan , ta nemi rakiyar su zahra amma dukkan su sukace mata baza su samu zuwaba, tayi mamakin yadda yau tayi musu tayin zuwa gidan Mallam suka ce a'a , alhali da su suke cewa azo aje gidan alhaji Mallam ayi Hutu, haka ta shirya ita kadai bello driver ya kaita, ta tarad da kowa lfy sun tarbeta da murna da nuna jin kewanta kamar yadda suka saba , a dakin kakanta wacce take kira da kaka mahaifiyar mahaifinta ta sauka , domin matan Mallam biyu ne ya qara aure amma matar bata haihuba har gashi tsufa yazo , gidan cike yake da yayan yan uwa da kuma daliban Mallam wasu ma harda iyalansu, domin gidan Mallam babban gida ne sosai mai dauke da sashe sashe , ..
Sai da daddare ta samu ganawa da alhaji Mallam bayan sun gaisa ya tambayeta yadda ta baro mutanan can gidan nasu tace lpy qlau nan suka Dan taba hira yana ta janta da Dan wasa na kaka da jika ita kuwa sai kunya takeji don bata saba irin wannan wasanda shi ba kuma gata bamai yawan magana bace, saida suka Dan taba hiran ya koma serious face dinshi shima, nan ya shiga sanar da ita abinda suka yanke akan aurad da ita ga dan uwanta Aslam, ya daura da yi mata nasiha mai ratsa jiki ya qare da cewa "wannan shine babban dalilin da yasa nace a turomin ke ni zan sanar miki da kaina,
Don haka ki zama mai biyayya a garemu, wannan wata dama ce Allah ya baki domin samun miji natsattse mai hankali kamar aslam a wannan zamanin abune mai matuqar wuya dan haka sai ki gode ma Allah da irin zabin da ya miki" tuni Asmah ta daina fahimtar abida alhaji Mallam ke fad'a tundai ta fahimci aure ne akeson a hadata da babban maqiyinta mutumin da ta tsana a duniya fiye da kowa ,,,...
Take wani zazzafan zazzabin farad daya ya lullubeta ci gaba Mallam yayi da yi mata nasiha wanda duk bata fahimtar komai ta Lula duniyar tunanin makomar rayuwarta, kaka ma data shigo ta same su daurawa tayi da nata nasihar,
Kafin magriba zazzabin nan yaci qarfita saida Mallam ya kira family doctor dinsu yazo ya dubata ya bata magani da allurai, kafin Safiya zazzabin ya sauka saboda qarfin alluran da akamata ,
Kwanata biyu a gidan alhaji Mallam ta dawo gida, bayan dawowanta sai ta koma wata iri da ita bata walwala gata dama ba mai yawan magana ba sai ta qara komawa wata silent , kullum saidai ta zauna tana tunani duk ta rarrame kamar wata Mara lpya , koda yake itama Mara lpy ce don garama wani na kwance a asibiti a kanta ,.....
Alhaji baba ma yasa an kirata shima dai nasihar ya mata sanna ya maimaita mata abinda Mallam ya riga ya fada mata, ya qara da cewa "amma baza muyi miki dole ba inkinga zaki cutu game da wanna lamari to kiyi magana wlh ni zan tsaya miki a fasa wanna auren, duk da cewa wanna cikar burinmu ne zamu haqura , haka Allah yaso ". Duqad dakai Asmah tayi qirjinta na bugawa wata zuciyar tana raya mata kawai ki gaya mishi bakison shi suyi haquri, yayinda wata zuciyar kuma ke tuna mata matsayin alhaji baba, daddy da mummy, a gareta bazata ta'ba iya cewa bata son jinin su ba intayi haka tayi butulci ,, wata zuciyar ta qara tuna mata da karatunta kenan yanzu onta yarda burinta na zama yar jarida yasha ruwa kenan sai dai taga su zahra suna zuwa school ita banda ita ,,,dago kai tayi da niyar furtama alhaji baba batason aslam kawai sai ta tsinci kanta da furta"alhaji bani da ja akan wannan zabin da kukamin, kune gatana , ban isa in take maganrku ba duk da kun bani zabi ,na amince da auren Dan uwana kuma yayana ya Aslam domin cikar burin ku na alkhairi , Allah ya tabbatar mana da alkhairi " qara duqad da kanta kasa tayi tana dauke hawayen dake zubo mata a idonta da wayau don kar alhaji baba yagani, ...
Murmushi alhaji baba yayi yace alhamdulillahi, Allah ya yi miki albaraka dama nasan ke mai biyayyace a garemu, bazaki taba kunyatamu ba tashi kije insha Allah zaki samu y'ay'an da zasu miki biyayya fiye da yadda kika mana ,...
Ta bangarn kamal da yaji labarin auren Aslam da Asmah ba qaramin tashin hankali ya shiga ba ranar da zazzabi ya. Wuni saida yayi kwana uku a kwnace kafin daga bisani ya lallashi zuciyarshi , ya tabbatar ya rasa asmah rashi na har abada, .... Shi babban tashin hankalinshi yadda aslam da Asmah zasuyi rayuwa a gida d'aya daki d'aya a matsayin mata da miji, yafi kowa sanin abinda ke tsakanin su ,tabbas yasan in akayi auren nan akwai matsala , yana dai roqon Allah yasa komai yazo da sauqi , ji yakeyi aranshi da zai iya da yaje ya samu iyasumu alhaji baba ya fada mai , amma ina! Ko giyan wake yasha yasa bazai taba iya tunkaran alhaji baba da wannan maganar ba
Date: Oct 7, 2022
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.