Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 47 of 89

Page 85 & 86

~ASLAM~

Zuwa yanzu jikin Aslam yayi sauki sosai har idan ba mutum ya Sani ba bazai taba yarda yayi wani ciwo makamancin wannan ba, ramace dai kawai yayi sai kuma hasken daya kara, hakan ko ba karamin kyau ya karamai ba,.

Washe garin ranar da aka miƙa amare dakin su ranar lahadi kenan, a ranar aka bashi sallama daga asibiti, babu kowa a tare dashi a lokacin sai Abba, bayan Abba ya gama biyan duk abinda ya kamata a biya, wani cleaner ya hahhaɗa musu kayan su zuwa motar Abba.

Sallama Aslam yayi da Dr James nan ya kara bashir shawarwari game da yadda zai kara kula da kanshi dan gujewa sake faÉ—awa irin halin da ya faÉ—a, sosai yama Dr James godiya , Abba na tayashi, sannan suka kamo hanya.

Lokacin da suka hau kan babban titi Abba ya juyo ya kalli Aslam, yace "nasan kanada labarin daurin aure ko" shiru Aslam yayi kafin daga bisani ya amsa da "eh Abba" Abba yace "to masha Allah , amarya tana gidan ka, tun jiya" da sauri ya juyo ya kalli Abba jin abinda yake cewa, a zuciyar shi yana cewa, wannan wani irin azarbabi ne ba sai a bari a sallame ni daga asibitin ba tukun a kawota

Tunanin shi ne ya katse lokacin da yaji muryar Abba yana jehomai tambayar "gidan ka zan kaika ko family hause" a zuciyar shi yace gida na gurin uwar wa, a fili kuwa yace "A'a Abba a dai kaini can gida na ƙara hutawa , na gaida alhaji da gajiyar biki, inyaso zuwa dare sai na je can din" Abba yace "to ba matsala hakan ma yayi kyau", kafin ya dauki hanyar family hause.

Gidan har yanzu akwai sauran baki na nisa dukda wasu sun dauki hanya yau da sassafe , yayinda wasu sai gobe zasu wuce.

Abba na parking ya bude motar ya fito, Abba ma fitowa yayi ya kalli Aslam d'in yace kaje tsohon part d'in ku kayi wanka ka kimtsa zan sanar ma maminku ka dawo ta hado ma abinci ,idan kaci saika shiga ka gaggaisa da mutane, ka huta zuwa dare sai ka tafi gidan ka kamar yadda kace, Aslam ya amsa da to Abba.

Tsohon part dinsu ya nufa kamar yadda Abba ya umarce shi, fallon ba kowa, saidai akwai datti ba'a kai ga gyara wa ba, haurawa upstairs yayi ya nufi tsohon dakin shi, dakin nanan tsab kamar yadda ya bar shi saidai dan kura da yayi, take ranar da yan sanda suka zo har kofar dakin suka tafi dashi ya fado mai arai, inbai manta ba rabonshi da dakin tun ranar , kai gidan ma baki daya, yana wannan sake saken gaban shi ya yanke yayi wani mummunan faduwa sakamokon tunowa da yayi da zee, amma tunawa da abinda ta aikata mai yasa take yaji wani haushin ta ya turnikeshi, fatali yayi da lamarinta ya fada toilet ya hada ruwan zafi yayi wanka, a É—arare yake wankan kasancewar bayin ya kwana biyu ba'ayi amfani dashi ba duk yayi kura abinka da komai fari, ji yake da zai iya daya fara wanke toilet d'in tukun to amma jikinshi ba karfi bayajin zai iya yin hakan.

Fitowa yayi daure da towel a kugunshi , wani karami kuma a hannunshi yana goge suman kanshi dashi, gaban mirror ya tsaya yayi shafe shafe shi, wardrobe ya bude ya dauki ƙananan kaya ya saka, take ya fito fess dashi, ana ciwo ayi muni shi Aslam wani kyau da haske ya karayi, masha Allah.

Daga bakin kofa yaji ana sallama , basai ya tambaya ba ya gane muryar mami, amsa sallaman yayi, ya nufi kofar ya bude, amsan tray hannunta yayi tare da cewa "sannu da kokari mamina" marmushi mami ta sakar mishi tace "masha Allah my son jiki yayi kyau Allah mungode maka" baice komai ba sai murmushi da yake ta binta dashi.

Karasawa tayi har cikin dakin ta dauki kofi ta hada mishi tea ta kuma zuba mai abinci, a plate ta tura mai gaban shi, daukan kofin tea din yayi tare da cewa "nagode mami na".

Zama dashi mami tayi har ya kammala cin abincin, yadan ci sosai kuwa ba laifi, bayan ya gama ta ballo mai magungunan shi ta bashi yasha,.

Kallon mami yayi yace "mamina bamu gaisa ba, ina wuni ya gida ya akaji da jama'a kuma ya gajiyan biki" mami yace "my son alhamdulillahi anyi taro lafiya an gama lafiya amare kowacce na dakin ta , saidai mu biku da addu'a Allah ya Baku zaman lafiya," da "amin thumma amin" Aslam ya amsa, mami ta sake cewa "yanzu tunda kaci abinci kayi wanka kasha magani, ba kwanciya zakayi ba , ka tashi ya je part din mummy ka gaishe ta ka mata bangajiya daga nan kuma kaje ka gaida alhaji baba da hajiya, dama sauran dangi da kenan" Aslam ya amsa ta "to mami".

Tare suka fito daga part din mami ta nufi nata shi kuma ya nufi na mummy.

A Palo ya tarad da mutane musamman yan uwan mummy na nesa da suka zazzo, binsu yayi daya bayan daya ya gaida su, amsawa suka shiga yi cikin so da kauna da kulawa, suna kuma yimai murnan auren da yayi,.

Mummy bata falon don haka bayan sun gama gaisawa ya mike ya nufi dakinta, sallama yayi a bakin kofar, daga cikin mummy ta amsa mai shiga yayi , zaune ya sameta bakin gado handset dinta rike a hannunta, gama wayarta kenan da ummi tace mata suna hanya sun kusa isowa, zama yayi a gabanta sanan ya shiga gaisheta da mata gaisuwar gajiyan biki, amsa mai tayi tana binshi da kallo, sannan itama ta tambayeshi shi jikin shi, ya amsa mata da cewa da sauki.

Shiru ne ya ratsa dakin na wasu sakanni, kafin mummy ta katse shirun da cewa"Aslam" dagowa yayi ya kalleta don mawuyacin abune mummy ta kira sunan shi, CI gaba tayi da cewa "a baya ka aikata babban kuskure, Wanda yasa mukayi fushi mai tsanani da kai, to amma yanzu alhamdulillahi komai ya wuce, ka nemi afuwar wadanda ka batawa, kuma kowa ya yafe, a yanda lamarin ya sauya lokaci daya ma, ba karamin abin mamaki bane, amma ba'a mamaki da ikon Allah, abinda nake so na gaya maka shine, Aslam ga zabi nan alhaji ya kuma maka a karo na biyu," duk da yasan da maganar amma jinta daga bakin mahaifiyar shi saida gaban shi ya yanke ya fadi kamar yanzu ne ake gaya mai batun, ji yayi kamar yace ma mummy wacece ita, amma ba hali don babu yar haka a tsakanin su.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.