Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 8 of 89
Page 13 & 14
"Maqasudin abin da yasa na tara ku anan shine "miqama Daddy takardan sakin da asmah ta kawomishi yayi,
Hannu biyu daddy yasa ya karbi pepan amma bai bude ba yana jiran umarni.
CI gaba Allah ji baba yayi da fad'in "wannan shine sakomakon abin da aslam ya sakamin da shi ,
Tunda nake cikin yayana da jikoki na ba'a taba aikatamin abinda aslam ya aikatamin yau ba, amma ba komai rayuwace"
Alhaji baba ya qarashe maganar cike da bacin rai a muryarshi"abdullahi bude takardar Ku gani mana" daddy da duk jikin shi yayi sanyi qalau yayi karfin halin bude pepan da bismillah a bakin shi.....abinda ya gani rubuce cikin pepan ne ya sakashi sakin pepan ba tare da ya shiryaba, abbane ya miqa hannu ya dauki takardar ya duba..... Miqewa shima yayi a zabure ya maimata innalillahi wa innailaihi rajiun kafin ya bude baki yace "wani irin haukane aslam ya aikata haka" Ummi ne ta karbi takardar ta duba itama ta miqa ma mummy da mami , kowa hankalin shi ya tashi a falon nan idan ka cire asmah da alhaji baba....
A zabure daddy ya miqe yayi hanyar waje, Alhaji baba ya dakatar da shi da cewa "abdullahi dawo ka zauna" ba musu daddy ya dawo ya zauna ,
Alhaji baba kallan mummy yayi yace "Aisha kin kiramin shi ?"
Amsawa mummy tayi da "na kirashi bai yi picking ba amma na mai text nasan inya gani zai kira yanzu" gyada mata kai alhaji baba yayi alamar gamsuwa......
Daidai wannan lokacin kuwa aslam ne ya fito wanka daure da towul a qugun shi, yana goge kanshi da karamin tawul d'in dake hannun shi, saida ya gama goge jikin shi ya dauki body lotion dinsa ya shafa da body spray dinsa mai shegen tsada da tsananin dadin kamshi, ya shirya cikin kayan barcinsa farare riga da wando marasa nauyi, pray mat ya shimfida ya gabatar da shafa'i da wutiri yayi addu'o'inshi , so yake ya kwanta barci da wuri , kallon agogo yayi ganin goma da Rabi na dare yasa ya Dane gado ya kwanta ya kashe fitila mai haske yabar dim light, wayar shi ce tayi qara alamar message ya shigo kamar ya share Dan d'azuma yana ji ana kiran shi ya share ko dubawa baiyiba balle yasan waye, shi duk zaton shi zee ce ko yanzuma yana zaton ita ce ta mai message , daukar wayar yayi da niyar kashe wa gaba daya don da gaske bacci yakeson yi da wuri, sai kuma ya tsaya don ganin message din daga mummy ne, ganin abinda ta rubuta ya sakashi saurin lalubo numberta ya kira jiki na rawa, daidai lokacin alhaji baba ke cema mummy ta sake kiran shi,
Ringing wayar mummy ya fara ganin Aslam dinne yasa yasa mummy saurin d'agawa ko amsa sallamarsa batayiba tace a kausashe"kasameni a gida nan da minti goma kuma umarni nake baka ba shawara ba idan har ni na haifeka...... Idan kuma nima zaka bijiremin d'inne to bismillah shege ka fasa" git ta kashe wayarta ta barshi da way a manne a kunne, Nan shima hankalinshi ya tashi jin yadda mahaifiyarshi ta mai magana cikin bacin rai, ga dukkan alamu sakon abinda ya aikata ya iskesu kenan.....hankalinshi ya dan tashi jin muryar mummy cikin bacin rai da tsananin fishi don yasan fishinta ba sauqi har gara fishin daddy yafi sauqi akan nata, amma ko dar baijiba akan abinda ya aikata balle yayi nadama
Tashi yaya ya shiga cikin qananan kaya ya dauki key din mota da wayarshi ya fice daga hotel din zuwa gida minti 15ya kaishi gida , direct sashen alhaji baba ya nufa son yasan sunacan suna jiranshi ,
Da sallama a bakinsa ya shiga parlon Abba da mami da hajiya mama ne kawai suka amsa mishi a fili , samun guri yayi ya zauna kusada abba, kanshi a qasa ya fara gaida mutanen parlon, kamar dazu daddy da mummy basu amsa mishi ba amma alhaji baba ya amsa mishi wannan karon,
Kallon asmah yayi kanta duqe a kasa nan take ya qarajin tsanar yarinyar a ranshi, kamar ya shqeta ta mutu kowa ya huta haka yake ji a ranshi duk ita ta jawo mishi wannan matsalar da yace ciki iyayenshi na fushi dashi akanta,
Kowa ya nutsu a parlon ana jiran hukuncin da alhaji baba zai yake gyaran murya yayi kafin ya fara da fadi "fadin Muhammad naga saqonko kuma na code amma ka Sani ka tabka babban kuskure Wanda zakayi Dana Sani nan gaba , lilokacin da Dana sanin bazai amfaneka da komai ba zakayi nadama loacinda nadaman ka baida amfani, kuma ka rubuta wannan maganar ka ajiye ko bayan raina zaka tina na taba gaya maka shi, "dago kai aslam yayi zai fara bada haquri,,
Dakatar dashi alhaji baba yayi da cewa"banyi fushiba Muhammad kankan ka cuta baniba, wlh kayi babban asara , domin zabin da namaka zabine daya a ciki dubu amma kasa qafa kayi tafali dashi, har kana sakinta ranar da aka daura muku aure waidon ka kunyatani..kanka kama,
ita kuma Asma'u zataci gaba da zama damu anan, Allah zai bata mijin da yafi komai tayi aurenta na aurad da ita kamar yadda nama kakanta aminina alkawari
Yusuf inason idan zaka je yima yan biyu da amira registration ka hada da asmah, tunda auren bai yuwuba karatu zata ci gaba da shi kafin Allah ya kawo mata wani mijin "
Sannan Abu na gaba"abdullahi ,Aisha,Yusuf, maryam da amina, inason Ku zama shaida na kamar yadda aslam ya Nina baya qaunar zabina asmah, to naji amince, amma babu aure zakanin shi da asmah a nan gaba na harantashi.......na haramta aure tsanin Muhammad da asmah ko bayan raina ban amince ba duk Wanda ya sake bashi auren asmah ko bayan raina ban amince ba,"
"Abu na karshe kai Muhammad ka sanar da iyayen ita yarinyar da kake so din cewa rana ita yau iyayenka zasu shigo gida ayi magana"
Yana gama fadin haka ya miqe yabar parlon matarsa ma bin bayanshi tayi don ta rarrasheshi ganin ranshi ya baci sosai ,
Daddy ne ya fara miqewa yabar parlon Mummy ma bin bayansa tayi ko kallon inda aslam yake basuyiba , ummi ma da ranta ke matuqar bace da abinda aslam yayi ta kama hannun asmah suka fice daga falon,
Sosai abbah kema aslam fada mami na taya shi saida suka tabbatar jikinshi yayi sanyi sannan suka qyaleshi ganin dare yayi
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.