Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 76 of 89

Page 120

Ta ke duk wani annuri dake kan fuskar Dad ya bace ɓat cikin abinda baifi second ba, yayin da wani mummunan bacin rai ya bayya na ƙarara a fuskar sa.kallon kallo suka shiga yi shida mom, wannan kalma data fito daga bakin zee ya matukar razana Dad, kwata kwata bai yi tsammanin jin wannan Kalmar daga bakin ta ba, ya riga ya gama sakankan cewa ta cire Aslam daga zuciyar ta, duba da yadda kwata kwata ta daina zancen shi ta tattara lamarin ta watsar, ta cire duk wani damuwa a ranta.

Ita ko idanunta ƙer akan Dad amsar da zai fito bakin shi kawai take jira. Miƙewa yayi bayan ya ajiye little Aslam dake hannun shi akan bed, ba tare da ya bata amsa ba, ya nufi hanyar fita daga dakin fuskar shi a haɗe kamar bai taba dariya ba, da kallo suka rakashi ita da mom, har ya kama handle din ƙofar zai buɗe,sai kuma ya dakata ba tare da ya juya ya kalle su ba yace"Wannan ya zama karo na karshe da zaki sake ambatar sunan wannan tsinannen yaron a gaba na, zan iya yi miki kome kike so a duniya nan amma banda barin ki a hannun wannan yaron Wanda baisan darajar ki ba." Yana gama faɗin haka yasa kai ya sa kai ya bar dakin a fusace.

Wani sabon Kuka ne ya kufce mata mai ƙarfi wanda yafi nada, fadawa jikin mom tayi ta kamkame ta, tana risgan kuka kamar ranta zai fita.bubbuga Bayan ta mom ta shiga yi tana rarrashinta tare da kwantar mata da hankali,cikin kuka tace "mom ina son mijina shima ya na sona, menene yasa kuke ƙoƙarin raba mu, me yasa kuke ƙoƙarin son ku raba sunnar ma'aiki, Wlh mom ina son miji na shine farin cikina, duk abin da ya faru ba laifin mu bane nida shi munaƙisa aka shirya mana, masu son ganin bayan mu don su farraƙa tsakanin mu, dan Allah kiyi wani Abu akai, ke mahaifiya tace. ke mace ce, zaki fi Dad fahimtar damuwa ta."Ta karashe maganar cikin matsanancin kuka.

Cikin lallashi mom tace "ya isa daughter ki share hawayen ki, na fahimce ki kuma insha Allah zan tsaya miki zaki koma dakin mijin ki, Dad ɗinki yana da tsatsauran ra'ayi, idan ya tsani Abu da wuya ya dawo daga baya ya so shi, amma nasan kodan saboda little boy dole zai hakura ki koma ɗakin ki, nasan shima bazai so yaron ya taso yana tambayar ki wanene ubansa ba, alhalin kuma shi ba shege bane, karki damu zan taya ki yaƙin domin farin cikin ki shine nawa."

Hankalin ta ya dan kwanta jin mom ta fara supporting dinta, tasan mom takan iya sauya ra'ayin Dad, idan ta tirje, duk da abune mai baƙar wuya, amma tana da tasiri agurin shi, da idan ta nace yaja taja yakan saki.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.