Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 12 of 89

Page 23 & 24

Biki nata gabatowa yau saura kwana goma , kota ina sai shirye shirye akeyi , amma banda amarya Asmah , ta zama wata iri da ita kullum cikin kuka, amma batayi gaban mutanen gidan, shiga toilet takeyi ta kulle kanta taci kukanta ta koshi,......

Aslam ne ya fito daga part din Alhaji baba ranshi a hade da kaganshi kasan ranshi a mugun bace yake idanun shi yayi jajur.....direct part dinsu na samarin gidan ya nufa , da baya da baya ya fada kan daya da cikin manya manyan sofa set d'inda ke falon hannayenshi ya hada cikin juna ya dunqulesu da karfi...rintse ido yayi yana sakin wani zazzafan nunfashi ,......ba komai ne ya jefa shi cikin wannan yanayin ba sai d'an kace nace daya faru tsakanin shi da alhaji baba..... Aslam ya kafe kaida fata na cewa bazai auri Asmah ba nan dai alhaji baba ya shiga rarrashin shi, rufe ido Aslam yayi ya shiga zazzagawa alhaji baba rashin kunya yana gaggaya mishi maganganun dayasan zai fusata shi har yasa yayi fushi yace a fasa auren, saidai kuma hakan bata faruba don alhaji baba miqewa yayi ya wawwanke Aslam da zafafan maruka har guda har sau biyu sannan ya nuna shi da yatsa yace "kai Muhammad wlh karya kakeyi baka isa ba, ni zaka kawowa rashin mutunci," nuna shi da yatsa yayi yace "to ko ubanka abdullahi bai isa ba, ballantana kai qaramin alhaki, kuma ka sani aure ne sai an daura babu fashi, kaje kayi duk abinda zakayi, dai dai nake da kai , duk rashin kunyar dake damunka ni nan zan sauke maka shi"hmmm ran maza ya baci,.... Miqewa Aslam yayi yace "yace haka kace ko to shikenan" yayi kwafa ya fice daga falon..... Dalinlin shigar shi halin da yake ciki kenan, saqa ya shiga yi da warwara har ya samar wa kanshi famitan da yake ganin zata fille mishi, mataki biyu zai dauka idan ya kwada na farkon bai yuwuba, to zai aiwatar dana biyu Wanda zai girgiza kowa,

Asmah bata qara tsanar Aslam ba sai ranar da yasa mummy ta turo mishi ita part dinsu , mummy da kanta ta shiga har d'akinsu , ta sakata ta wanke fuska ta shafa hoda da 'kolli, Wanda rabonta da su tun ranar da zataje gidan alhaji Mallam , hijab ta zumbula har qasa ta dauki hanky tana tafe tana share hawaye da majina ,

mummy kam ganin ta tafi ba musu yasakata a ranta ta dinga yin hamdala tana murna gani take duk yadda akayi sun fara sasanta Kansu ne tunda gashi har yana kiranta su tattauna, Dan shi cema mummy yayi zasu Dan tattauna ne yaji shirye shiryen ta akan bikin,

Asmah na qara kusantar part dinsu Aslam gabanta na tsananta faduwa haka dai ta daure ta qarasa ta shiga falon da sallama a bakinta , ganin shi tayi zaune a falon sanye da qananan kaya yayi kyau sosai fuskarnan nashi a hade ba alamar mutunci, amma ita a idonta gani takeyi ba Wanda ya kaishi muni a lokacin , ko sallamarta bai amsaba ya watsa mata wani mugun kallo mai cike da tsana .....tsugunawa tayi daga can gefe ta rakube kamar tana jira ace tak ta ruga da gudu, watazabgegiyar wuqa Aslam ya zaro daga cikin gidanta mai shegen kaifi irin Wanda tsab za'a iya fille kan mutum dashi tashi daya, miqewa yayi daga inda yake zaune da wuqar a hannun tsirara , nufo inda take tsugune yayi gadan gadan , ganin haka yasa jikin Asmah ya fara rawa ta sadaqar yau kwananta ya qare,tasan tabbas Aslam zai iya mata abinda yafi kisa ma a yadda ya tsanetan nan, don haka ta fara maimaita Kalmar shahada a zuciyarta rintse idonta tayi da qarfi donma kar taga sanda zai caka mata , ji tayi yace cikin tsawa"keee mayya look up " dago da kanta tayi da sauri jikinta na rawa cike da tsoro , guntun murmushin mugunta ya saki saboda hango tsantsar tsoratan da tayi a cikin kwayar idonta, dama abinda yake son gani kenan kafin ya kora mata kyakkyawan warning din da yake son ya mata .........

Waning ya shiga kora mata da kashedin cewa , idan ta kuskura ta bari aka daura auren nan har aka kaita gidan shi a matsayin matarsa saiya yankata da wannan wuqar ya kasheta kowa ya huta, ya qarashe maganar yanayin alamar yankata da hannun shi,
nan ya tsatsara mata abinda zatayi da zaisa afasa auren. Kuma karta kuskura ta bari sunan shi ya fito, ya qare da zageta Tass kafin yace ta bace mai da gani ,.....
Aikam da sauri ta miqe ta fice daga part din cikin gudu gudu sauri sauri tana sharar hawaye, ta shige part din mummy, allah yasa mummy bata falo tana dakin daddy don haka direct dakinsu ya wuce ta fada kan gadonta tanata risgan kuka abin tausayi , su batool dake zaune zugum zugum suna zaman jiran dawowarta, dama tunda ta wuce jinin su a qumba yake, sai gani sukayi ta shigo da kuka dama sun tsammaci hakan, lalkashinta suka shiga yi cike da tausayawa, gani duk sun shiga damuwa yasa ta tsayar da kukanta, amma a ranta ta qudiri aniyar saidai Aslam ya kasheta amma baza taba aiwatar da. Abinda yace tayi ba, ta yarda in an kaita gidanshi ya yankata ,

Sannu bata hana zuwa yau gashi saura kwana uku daurin auren Aslam da Asmah , masha Allah gidan alhaji baba kam ya cika da jama'a baki na nesa dana kusa duk sun hallara , sai shirye shirye akeyi ,..

Duk wani gata daya kamata amarya yar gata ta samu Asmah ta sameshi , musamman ummi ta dauko wata mai gyaran amare tun daga suleja ,... Matar shahararriya ce sosai ta fanin gyaran amare ciki da bai , qyara Asmah ta shiga yi tsakanin da Allah don ba qaramin kudi ta amsa ba , saidai kuma amarya kwata kwata bata bata hadin kai yadda ya kamata don gaba days bata cikin walwala saidai tana qoqarin boyewa,

Ko program da aka tambayeta cewa tayi ita baza tayi komai ba, mami ne tace ba'ayi hakaba ita ta shirya mother's night ran alhamis ran juma'a ayi walima 4pm to 6pm a alkausar hall inyaso in andawo walima asa lalli washe gari a daura aure, haka ko akayi.......

Ta bangaren Aslam kam ganin shiru shiru ba a fasa biki ba saima qarin shirye shirye da akeyi, yasan lallai Asmah batayi abinda yasata ba, don inda tayi ya tabbatar alhaji baba zai dakatar da maganar auren nan , kwafa tayi cike da jin haushin duk wani mai hannun ciki wannan hadin including daddy da mummy , don haka ya qidiri aniyar aiwatar da mataki na biyu wanda yasan shine kankat, koda amir ya sameshi da maganar da maganar tsare tsare da gayyatar friend dinsu, hawa yayi kanshi da masifa yana neman ya sauke haushi a kanshi , qyale shi amir yayi yaci gaba da abinda ya kamata , ya gayyato friends dinsu tun daga na nan gida Nigeria dake mabanbantan garuruwa har na qasashen qetare da sukayi karatunsu tare, da kuma abokanan aikinsu, ba qaramin gayyata amir yayiba , har dinner yaso ya hada amma ganin aslam din yaqi bashi hadin kai yasa ya bar maganar dinner ,friend dinsu da amir ya gayyata suka fara isowa ,wasu kuma na kiran Aslam a waya suna mishi murna abin ba qaramin qona mai rai yakeyi ba , kowa ma haushi yake bashi mussamman ma amir dake ta wani zaqewa yana wani gayyata, ga cikin gida nan ma bai tsira ba daga ace ya bada kudin kaza sai ace ya kawo kaza, karshema ganin za'a dame shi ya tattara yanashi yanashi ya bar gidan ba tare da sanin kowaba , ya kama daki a hotel babu Wanda yasan inda yake, ya kuma qudiri aniyar yadda alhaji baba ya tilasta mishi auren wannan mayyar yarinyar mai idon mayu to wlh saiya kunyata shi tunda dai ya dakatar dashi, amma yaqi ji har yana marin shi , to yaje ya daura shi kuma yayi alkawarin ana daurawa zai saketa, yasan indai ya saketa aranar da aka daura musu aure ba shi kenan ba kunga dole a qyaleshi da wannan auren jarabar , qilama alhaji baba yayi fushi ya aurama amir ko kamal ita a ranar, hakan ce kuwa ta kasance don da wannan matakin aslam yayi amfani ya rattabawa asmah saki aranar da aka kaita gidanshi a matsayin matarsa zabin iyayensa

CIGABAN LABARI
Date: Oct 5, 2022

💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.