Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 10 of 89

Page 17 & 18

Duk wannan abinda ke faruwa a tsakanin su iyayensu basu da labari, iya yara yaran gidan ne kawai suka san abinda ke faruwa su kuma ba daman fada tsoranshi sukeji kar su fada ya dake su,
Kamal ne ma yake qoqarin hanashi in yana dukkanta yai ta bashi haquri amma ko kallon banza baya isansa, Rabi'ah kuwa tun ranar da tayi mai magana ya tsinka mata mari lokacin batayi aure ba taja bakinta tayi shiru ta zuba ma sarautar Allah ido.......

Kamal yana matuqar tausayin asmah saboda irin abubuwan da aslam ke mata, haka zai sameta yaita rarrashinta yana bata baki akan tayi haquri wata rana sai labari, wani irin kulawa yake bata Wanda ko qannenshi baya basu irin wannan kulawan, kamal ya kasance mai yawan magana Dan haka zaizo yasata agaba yaita mata labaran ban dariya duk Dan ta manta da abinda aslam ke mata agidan...
A hankali wani irin shakuwa ya shiga tsakanin,

Su asmah sun shiga jss 1 lokacin aslam na shirye shiryen wucewa karatu kasan waje,,, FGC abbah yakaisu inda asmah da batool A class zahra da amira B class su hudu suke rayuwarsu gwanin sha'awa,, basuda wasu baren qawaye su hudun nan sune qawayen junan su.

Ranar da aslam da amir zasu tafi makaranta a kasar Malaysia zo kuga murna gurin y'an mata mummy, bama kamar asmah har wani Dan qaramin party suka hada a dakinsu su hudu na murnan tafiyan aslam ...

Tabbas y'an matan mummy sunji dadin tafiyan aslam, asmah tuni ta saki jikinta a gidan don dama aslam ne kadai matsalarta ... Agidan kowa nasonta babu mai nuna mata wani banbanci ta zama yar gida babu mai sanin rikonta akeyi a gidan ,,, alhaji baba ma qarara yake nuna mata soyayya fiye da sauran jikokinsa, domin ita din jinin amininsa ce mutum mafi soyuwa a gareshi, sosai yake kula da dukkan lamarinta,, hakan ya saka mata wani irin matsanancin kaunar tsohon da ganin girmanshi a zuciyarta, sosai take girmama shi, sosai take girmama dukkan lamarinsa, yanda ko layi yaja yace kar ta tsallake to bazata taba tsallakewa ba kuwa har illah masha Allah,

Ta bangarenb kamal kuwa shaquwan dake tsaninshi da asmah ya rikide ya koma soyyaya a gare shi ,domin kuwa shi kadai yake kidanshi da rawanshi ita batasan yanayiba, ta dauka kawai sabon da sukayi ne yasa yake mata wasu abubuwan kamar na soyyayya, saidai kuma duk Wanda yaga yadda suke mu'amala saiya saka musu ayar tambaya❔, su zahra sunsha tambayarta wai kod'ai soyayya takeyi da yaya kamal, takanyi murmushi tace musu a'a ita yaya kamal yayanta ne ba wannan maganar a tsakanin ta dashi,, sukance mata ba wani nan intayi wari maji,

Su aslam sunacan kasar Malaysia suna karatu hankali kwance tunda ya tafi bai taba dawowa gida Hutu ko ganin gida ba , yanadai kiran iyayenshi a waya suma suna kiranshi musamma mummy da mami,
zuwansu da shekara shida suka hada karatunsu akan business, amir ya tattaro ya dawo qasarmu ta gado, shikuman gogan ya zauna ya fara aiki acan da wani babban kamfanin mahaifin abokinsa da sukayi karatu tare.....
A Malaysia ya hadu da zee school dinsu daya amma ba Abu daya suke karantawa ba,
zainab abdussalam yariyan wani. Hamshaqin attajirin Dan boko ne haifaffan Nigeria ma zaunin Malaysia,, zainab yar gata ce gurin iyayenta kasancewar ita kadai suka Haifa sangartatciya na qarshe,, bata iya komai ba sai rashin kunya, sai kuma ayi wanka a qure kwalliya a fita yawo da qawaye akashe kudi kamar basusan ciwonshi , kodayake basuwan ciwonshi ba tunda basu ke wahalar nemowaba,
Zainab ta kasance kyakkyauwa ce yar kwalisa kuma macece mai class don ba kowani gara take kulawaba saita tabbatar kai wani ne ko Dan wani sannan zata yarda ta kulaka kuyi soyayya,, kana kawo mata maganar aure zaku watse don ita kwata kwata babu aure a gabanta, haka iyayenta, a cewarsu bata isa aureba shekara ashirin da shidda, wai saitakai thirty five zasu aurad da ita,

Ranar da zainab ta fara ganin Aslam ta kamu da matsanancin soyyayyar shi, saidai shi baima son tanayiba kasancewar sa ba mai kule kule kulen mata bane , a hankali zee tafara shigema aslam, bayan tayi bincike sosai akanshi ta gano ko shidin wanene , sosai ta saka mishi ido a school din inyana waje zatazo ta zauna ta dauko book din ta tana karatu, tun bai lura da ita har ta fara daukan hankalinshi, tun bai riqe face dinta ba har yayi making face dinta a kwakwalwarshi ,, zainab ta hada duk abinda aslam yakeso a y'a mace , yana son kyakkyawar mace kamardai zee, yanason wayyayyar mace yar boko wacce tayi karatun boko mai zurfi,, yanason mace mai aji wacce ta iya daukar wanka wacce batada rawan kai irin na yan matan zamanin nan wacce in ya shiga da ita cikin taro baza'a raina shiba, zee ta gama hada duk wadan nan qualities din,bai tunkaretaba saida yayi bincike akanta ya gano ko ita wacce ce, sannan ya baiyana mata manufarshi, ba wani dogon Jan aji ta amince masa nan da nan suka qulla zazzafan soyayya

Date: Oct 4, 2022

💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayenmu}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.