Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 18 of 89

Page 33 & 34

A kwana a tashi ba wuya yau gashi saura kwana uku daurin auren Aslam da zee , tun ranar Monday aka fara program ba kama hannun yaro ,

Ta bangaren zee biki akeyi gagarumi yayinda ta bangaren Aslam abin dai gashi nan kadaran kada han, don mummy ma cewa tayi bazata gaiyace kowa ba,yoo ta gayyaci mutane ta ce musu me , bayan ko wata uku ba'a rufa ba data gayyato su bikin Aslam, yanzu kuma ta sake ce musu suzo bikin Aslam again, gsky baza ta iyaba.

Biki dai ba wani bare daya zo duka dai yan gida ne wadan da zuwa bikin ya zame ma dole,

Yau ne akayi kumbo kuma yaune ango ya fara halartan program daya daga cikin ukun daya zaba zaije,

A babban hole din dake mai jama'a hotel akayi 4:pm aka fara aka tash70:pm, daga dangin ango kam ba wanda yaje. Sai shi kadai da abokansa sai ko kamal, su zahra dama sukayi niyyan zuwa kuma mummy tace bazasuje ba, haka suka haqura,

Misalin qarfe takwas da rabi na dare, Aslam ne da wasu daga cikin abokan shi zaune a palon shi suna fira, su niyara ne Aslam, amir, Dr bash, sai wasu baqin fuska su biyu,

Fira sukeyi suna dan rahan su irinta abokai suna dariya, kamal ne yayi sallama ya shigo , ganin su a palon yasa shima ya zauna akaci gaba da hiran da shi ,

Amir ya dubi Dr bash yace"bash kasan ni ban iya boye, boye ba arayuwa ko mutum zaiji haushi na saina fadi abinda ke raina" Dr bash yace"kwata kuwa nasan da haka " amir yace "a gaskiya ina taya abokina kuma dan uwana jaje" duka sauran abokan nasu da shi kan shi Aslam din maida hankali sukayi kan shi don jin me zai fada,Dr bash yace "jajen mefa" amir yace "na rashin kyakkyawa kuma natsatsiyar yarinya kamar Asmah mana" hade rai Aslam yayi ganin amir na naman yaci mai mutunci, bash dake kunshe dariyar shi ganin yadda lokaci daya fuskar Aslam din ta koma, yace, "amir me kake nufi kana nufin kace ita zainab bats da kyau da nastuwa ne " amir yace"a a nifa bance ba ta da nutsuwa ba tanada nutsuwarta dai dai gwargwado, amma batun kyau kam abarshi, mace a tsaye sambal sai kace bigun katako " dariya sauran abokan suka saka, anas yace "gaskiya amir baka da mutunci wlh".

Aslam kam qara hade fuska yayi tamau iya kunnuwa kuwa ya kunnu sosai , ji yake kamar ya tashi ya rude amir da duka, amma ya fuska ya qyaleshi,

Amir ya amsa ma Anas da cewa "nida shi wayafi wani rashinmutunci , ai tunda ya wulagantamin qanwa akan wannan figaggiyar yarinyar mai zubin tabarya , wlh daga shi har ita sun shiga uku dani, kuma wlh asaran shi don nayi imanin bazai taba samun kamar taba balle wacce ta fita, tun yanzu AI gashi nan Allah ya fara kamashi, kaga bashir na daya Asmah akwai natsuwa, hankali, ladabi, biyayya kunya , ilimin addini Dana book tarbiya, uwa uba gata da wani irin kyau mai fisgar duk wani lafiyayyen namiji, asalin figure 8 nake gaya maka mallam, komai yaji " miqa mai hannu bash yayi suka fata suna dariya , yaci gaba da cewa "wlh badadon nayima kaina wani tanadaiba da ba abinda zai hanani yin wuff da ita kuma ko yanzu ma bata baci ba "

a fusace Aslam ya miqe kamar wani mayunwacin zaki ya kaima amir wawura, amir da tun dazu yake ankare da Aslam din sanin da yayi hakan zai iya faruwa, yayi wuff ya miqe yayi hanyar qofa, tsayawa Aslam yayi yana huci ganin bai samu nasaran damqarsaba yace"banza dan iska kawai" juyawa yayi ya wuce sama fuuuu daki ya shiga ya buga kofa da qarfi ji kake bamm, don ranshi ba qaramin baci yayi ba inyace zai tsaya yin magana lokacin bazai fadi alheri ba,

Amir daya gama tikar dariya ,ya dubi su bashir yace ku tashi na rakaku ku tafi, yayi qwafa tare da cewa "ai wlh dani kake zance Aslam duk wula qancin da kamin a lokacin wancen bikin saina rama" tashi sukayi suka fice suka bar kamal shi kadai,

Kamal da yayi mutuwar ......

Manage pls
Date: Oct 14, 2022

💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wanna book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.