Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 80 of 89

Page 123

Wani irin zaro ido mom tayi, lokacin da idanun ta sukayi arba da abin da yake nuna mata, gaban ta ne ya shiga faɗuwa hankalin ta ya tashi, cikin rawar jiki ta ƙarasa gaban bed ɗin ta miƙa hannun ta dake karkarwa ta ɗauki pepan ta miƙa mishi. Kasa amsa yayi sai zuba mata idanu da yayi yana binta da kallo kamar wani dolo, ganin haka yasa tayi karfin halin warware linkakken fefan ta fara karanta abin da ke rubuce a bayyane kamar haka:

Amincin Allah ya tabbata a gareku yaku iyayena, barkan ku da wannan lokaci, kafin nace komai zan fara da Baku haƙuri akan abin da zaku tsinkaya a cikin wannan bakar wasiƙar, ina me neman yafiya da sanya albarkan ku a duk inda nake, a daidai wannan lokacin da kuke karanta wannan wasiƙar tawa, jirgin mu ya daɗe da keta hazo, zuciya ta gaza hakuri, na kasa juriya na tafi Neman aljannah ta ku sanya mini albarka, sannan kuma ku yafe min ina kaunar ku iyayena.

Tun kafin mom takai karshen karatun tuni hawaye ya gama wanke mata fuska yayin da Dad shi kuma tuni ranshi ya gama baci,zuciyar shi ta dauki wani irin zafi kamar zata fesar da aman wuta.Wani irin numfashin fusata ya shiga fesarwa, mom bata ankara da yanayin da yake ciki ba sai da taji ya fisgi fefan dake hannun ta ya shiga cukurkuɗe shi a hannun shi ya dunƙule shi da karfi, da karfi ya furta "why daughter, why Zainab me yasa zaki min haka, kece raunina ta farko a duniya, meyasa meyasa meyasaaaaaaaa?" Tuni hankalin ta ya ƙara tashi ganin halin da ya shiga cikin kankanin lokaci gaba daya ya fita daga kamanni shi idanun shi sunyi jajur jijiyoyin kanshi sun tashi.Tsoron ta Allah tsoran ta kar ciwon shi ya tashi, cikin kuka tace "Dadyn zee ka tashi duk ba wannan ya kamata muyi ba, duk yadda akayi daughter gidan mijin ta Asl..." Katse wa maganar ta yayi sakamakon lafiyayyen Marin da ya ɗauke fuskar ta dashi , tsananin firgita saida ta taune harshe, dafe kuncin tayi ta zuba mishi idanun ta da ke zubar hawaye , tun da sukayi aure da shi yau kimanin shekaru talatin kenan cif a duniya bai taba koda zagin ta bane balle har takai ga mari.

A matuƙar fusace ya nuna ta da yatsa tare da cewa cikin kakkausar murya "wannan shine hukuncin ki a duk lokacin da kikayi gigin sake ambatar sunan wannan la'anannen yaron a gaba na, nasan da haɗin bakin ki zainab ta bar gidan nan domin tun farko kin nuna kina goyan bayanta, to ki sani kiyi duk yadda zakiyi ki dawo min da ɗiya ta gaba na, idan kuma ba haka ba wallahi wallahi zan dauki ƙwaƙƙwaran mataki akan ki daga ke har wancen ƙaramin dan iskan." Yana gama faɗin haka ya fice a ɗakin a fusace da wani irin sauri kamar zai tashi sama, tunda ta ɗaura hannunta a fuskar ta kafe shi da idanu ta kasa koda kefta ido ne, ita Abdus-salam zai Mara yau akan ƴar shi, ƴar da ita ta dauki cikin ta a jikin ta na tsawon wata tara da daɗi ba daɗi, yar da ta tsaga jikin ta ta fito, par da ta shayar da ita da nononta, par da taci kashi da fitsarin ta, lallai zata nuna mishi ita ɗin uwa ce,zata nuna mishi matsayin uwa a gurin ƴarta, lokaci yayi da zata dawo daga rakiyar Abdus-salam. Tunanin ta ne ya katse jin wani irin gurnani da hayani ya na tashi daga compound din gidan, muryar Dad ta jiyo yana cewa "wlh sai na kashe ka, da haɗin bakin ka ɗiyata ta bar gidan nan, munafiki ka gaya min da saka hannun ka ko A'a." Da wani irin gudu Mom ta fito daga cikin gidan tun daga nesa ta hango shi ya shaƙi wuyar get man da ke musu gadi shekara da shekaru, sai kwalfa mishi mari yake yi bai ko kula da cewa a girme kila mutumin ya girme shi ba kokuma suzo tsara. Kara girgiza shi yayi tare da cewa a tsawa ce "Da kai nake magana fa, baza ka bani amsa ba saina illata rayuwar ka." Daidai lokacin mom ta ƙaraso gurin ta rike Dad ta baya tana ƙoƙarin ta raba shi da me gadi, ina ko gezau baiyi ba da alama ba a cikin hayyacin shi yake ba. Ganin ta kasa ga me gadi na wani irin numfashi kamar ran shi zai fita yasa ta sake shi ta durƙushe kasa tare da fashe wa da wani irin kuku, mai ban tausayi. Daidai time din kuma aka buɗo karamin get din gidan aka shigo, hango yanayin da suke cika yasa alhaji Abdur-rahaman da wani mutumi ƙaraso wa cikin gidan da gudu, ganin ƙanin nashi na shirin yin kisa yasa baiyi wata wata ba ya dauke fuskar shi da maruka har biyu lafiyayyu.

Take jini ya fara bulbula ta hancin Dad kafin kace kobo kuma jikin shi ya saki idanun shi ya shiga kakkafewa a hankali ya saki me gadi, yayi baya zai fadi da gudu daya mutumin da suka shigo da Alhaji Abdur-rahman ya tallabe shi yayin da shi kuma Alhaji Abdur-rahman ya tallabe mai gadi da shima yayi taga taga zai faɗi, ganin haka yasa Mom fasa wani irin gigitaccen ƙara tare da cewa"innalillahi wainnailaihi rajiun, na shiga uku shikenan Abdus-salam ya tafi ya barni, wayyo Allah naaa!!"

~9JA~

Niger tsate airport mekunkele. Janye take da katon trolley dinta a hannun ta na hagu yayin da hannun ta na dama ke rike da hannun ɗan kyakkyawan yaron ta dake sanye cikin wasu irin shegun kayan Sanyi masu masifar kyau kafar shi sanye da kwambas mai mugun tsada,kanshi sanye da hular sanyin dake jikin rigar ,yayinda ita kuma take sanye da kayan ta na gado ƙananan kaya riga da wando saidai ta daura after dress mai kauri a saman su yayin da ta yane kanta da mayafin rigar.
Kallo daya zaka musu ka tabbatar tafiyayyu ne daga wata kasar dabam wacce ba Nigeria ba ba kuma maƙotan ta irin su niger da sauran su ba.

Wani irin daddaÉ—an iska take ji yana ratsa huhun ta da duk wani kafar iska na jikin ta, rabonta da shakar irin wannan iskar tun ranar da ta saka kafar ta tabar Nigeria yau kimanin shekara daya da rabi kenan cif. Wani irin kwanciyar hankali da ta Dade bata ji irin shi bane taji ya saukar mata lokaci guda take ta shiga sauke wani irin ajiyar zuciya tana lumshe fararen idanun ta.

Daga bayan ta taji yana cewa "Hajiya salamu alaikum." Da sauri ta juyo ta sauke idanunta akan dan matashin saurayin dake mata magana, sai lokacin taji hankalin ta ya tashi sai lokacin ta tuna in da ya kamata ta dosa, take zuciyar ta ya bata amsa da gidan mijin ki mana, yayin da É—aya sashen ke cewa gidan iyayen shi, domin sune babban matsala shin da wani ido zasu karbi little a matsayin jinin su kuma jikan su É—an Aslam wanda basu San da zaman shi a duniya ba. Muryar dan saurayin ne ya kara katseta da cewa "Hajiya baki amsani ba Nine driver da mai gida ya turo domin na kaiki masauki." GyaÉ—a mai kai kawai tayi alamar ok, amsar trolley É—inta yayi ya nufi inda ake parking motoci ya sanya a cikin motar shi, buÉ—e mata baya yayi ta shiga yayin da shi kuma ya buÉ—e gefen driver ya shiga ya tada motor suka É—auki hanya.

Sai da suka daidai ta akan babban titi ta buɗe baki a karon farko tayi magana"kure area zaka kaini." Dan juyowa yayi ya kalle ta tare da cewa "Ok hajiya, amma mai gida cewa yayi na kaini shaanu wani sabon ƙaramin gidanshi da ya saya kwanan nan gama keys ɗin gidan nan a hannu na." Tace "no ka kaini kure area kawai." Yace "toh hajiya." Bai sake cewa komai ba sai daukar hangar unguwar data ambata mashi yayi, motar su na kara kusantar unguwar gabanta na kara faduwa yayin da hankali ta ke kara kwanciya, ta rasa wanne ne ya rinjiyar wani tsakanin kwanciyar hankali da nutsuwar zuciyar da take ji da kuma faduwar gaban da ya tasa ta a gaba.

Dai dai kofar tamfatsetsen gidan Alhaji baba ta umarci driver da yayi parking, bai musa ba kuwa yayi parking din tare da fitowa ya buɗe mata ƙofa, ta fito sannan ya buɗe boot ya fito mata da akwatin ta, jakar ta na hannu ta rataye a kafaɗar tare da riƙe hannun little suka doshi get din gidan yayin da drivern ke binta a baya dauke da trolley ɗinta.

Cikin sa'a karamin kofar gidan a buɗe yake, da bismillah ta sanya ƙafar ta cikin gidan, hannunta rike dana little, juyowa tayi ta kalli drivern ta sakar mashi murmushi tare da miƙa mishi hannu alamar ya bata trolley ɗinta. Ba musu ya mika mata kuwa, tace " n
Nagode sosai fa." Murmushi yayi tare da cewa "Ba komai hajiya akan aikina nake." Sallama sukayi ya juya ya tafi yayin da ita kuma ta fuskanci cikin gidan tana ƙare wa ko ina kallo.

Babu kowa a compound ɗin gidan kasancewar gida ne da babu ƙananan yara a ciki, tambayar kanta take yi wani part zata dosa, sauke idanun ta tayi akan part din Mami, wanda nan ne part din da taɓa shiga har tayi zaman fiye da awa ɗaya a cikin shi.

A hankali ta daga ƙafarta ta fara takawa zuwa part ɗin mami, sai da tayi bismaillah sannan ta danna doorbell, so ɗaya ta dauke hannunta tare da jiran tsammani.

Mami da sakkowar ta kenan falon ta fito da nufin ɗaukar wayar ta data manta a falon ɗazu da safe, taji ƙarar ƙofa, hakan yasa ta nufi ƙofar ta buɗe domin duba ko wanene. Kusan suman tsaye tayi lokacin da idanun ta suka sauka cikin na zee, cike da tsantsar mamaki tace "zainab! Kece da gaske ko idona ne." Ga mamakin ta sai gani tayi zee ta sakar mata wani irin kyakkyawan murmushi, tare da kallon little dake dan jan rigar ta, sai lokacin idanun mami suka sauka akan little dake tsaye kusa da mahaifiyar shi hannunsu sarƙe dana juna.

Gaban ta ne ya yanke yayi wani irin faɗuwa rass, take ta ƙure yaron da kallo bata ko keftawa, ba kowa take gani ba fa ce Aslam a wasu shekaru masu ɗan nisa da suka shuɗe, lokacin da aka auro ta gidan tana amarya.

Dago da kai tayi ta kara kallon zee ta sake kallon little, ko shakka babu wannan jinin Aslam ne, ko shakka babu wannan jinin daddy da Abba ne ko shakka babu wannan yaron jinin Alhaji baba ne, babu bukatar ta tambayi É—an waye domin ko makaho ne kuwa ya laluba zai tabbatar da hakan balle kuma ace mai ido biyu.

Durkushewa tayi ta maida tsawonta daidai na little kafin kuma ta kaima yaron wani irin runguma sannan ta fashe da kuka, ba komai ne ya saka mami kuka a daidai wannan lokacin ba face tunawa da irin yadda Aslam yake kaunar yaga gudan jinin shi a duniya, kamar yadda yake ta faɗi tashi yaga ya samu ɗan kanshi a doron ƙasa, ta fi kowa sanin sirrin Aslam tafi kowa sanin yadda yake kaunar yaga ya haihu, yana iya boye ma kowa sirrin shi a duniya amma banda ita zata iya rantsuwa banda Asmah data kasance abokiyar rayuwar shi itace mutum ta biyu da zata bugi kirji ta faɗi wanene Aslam.

ÆŠagowa tayi tana share hawaye ta kalli zee tace "Zainab muje cikin gida wannan lamarin ba abinda zaki tunkare ni da shi ni kaÉ—ai bane." Daukar little tayi ta ta rungume ta doshi part din Alhaji baba,yayin da zee ta rufa mata baya.

Kabbara Alhaji baba ya shiga yi a bayyane yayin da hajiya mama ta shiga sharar kwallah, a lokacin da suka yi arba da little. Tuni jikin zee yiyi sanyi mekefaruwa ne,to kodai Aslam ya mutune, take gabanta yayi wani irin mummunar faÉ—uwa, take itama hawaye suka shiga wanke mata fuska hannun mami dake zaune kusa da ita ta damke da karfi Wanda saida mami ta juyo a firgice ta kalle ta, ganin hawaye a fuskarta yasa mami bule baki da sauri da nufin tambayar ta mekefaruwa saidai muryar ta ya katse ma mami hanzari, cikin sheshekar kuka tace"Mami ya mutu ko, Aslam ya mutu ya barni ko."Da sauri mami ta shiga girgiza mata kai kafin ta bule baki tace "A'a zainab karki sake faÉ—in wannan Kalmar Aslam bai mutu ba yana nan da ranshi da lafiyar shi." Zubawa mami idanu tayi tana kallon ta bawai dan ta yarda da abin da take gaya mata ba, ita yanzu idan ba ganin Aslam tayi ido da ido ba babu wanda zai ce mata yana raye ta amince.

Mummy ce ta fara shigowa falon domin amsa kiran gaggawar da Alhaji Baba ya mata, a ruɗe take matuƙa don tasan irin wannan kiran gaggawa daga Alhaji baba, ba karamin muhimmin Abu bane, tana shigowa idanun ta akan little dake rungume a jikin hajiya mama ya sauke, wani irin wawan burki ta taka, yayin da doguwar sallamar da ta rafko ya katse, bakin ta ne ya shiga rawa alamar tana son ta furta wani Abu amma kuma ta kasa buɗe baki, hajiya mama ne tace tana share hawayen farin ciki"kyayi abinda yafi haka ma Aisha karaso ciki." Mami ne ta Ƙarasa gare ta ta riƙo hannunta zuwa cikin falon ta zaunar da ita kusa da hajiya mama, mummy kam dama bata iya ruɗewa ba, lokacin da tayi arba da zee sai ta kura mata ido kamar tana son ta tuno inda tasan ta harga Allah ji tayi kamar an mata formatting lin komai daga kwakwalwar ta.

Daidai nan daddy ya shigo Amir na biye dashi ko zama basuyi ba Abba ma ya rafko sallama, duk da suma sun kaÉ—u da ganin zee tare da yaro mai kama da Aslam hakan baisa sun ruÉ—e ba kasancewar su mazaje masu dakkakkiyar zuciya.zama sukayi domin amsa kiran Alhaji baba, babu Wanda ya furta koda A ne daga cikin su, domin duk sanda Alhaji baba yayi irin wannan kiran kowa natsuwa yake yi ya saurare shi babu mai ikon yin magana har sai yaba da umarnin yin hakan, kamal ma ya karaso daga gurin aiki yake ma ya dauki excuse ya taso, Allah yasa ba sa wani Abu mai mahimmanci.

Aslam kawai ake zaman jira kasancewar an bashi umarnin ya taho harda Asmah, kuma yana office dole saiya biya gida ya dauko ta hakan yasa yayi jinkirin isowa, falo yayi tsit sai kallo kallo akeyi a tsananin juna, fuskar kowa cike da zaƙuwan sonjin ta yaya akayi matankaɗi ya shiga gora, domin dai dukkanin su kallo daya suka ma little suka tabbatar cewa lallai shiɗin jinin su ne, kamar yadda yaron ya kasance mai farin jini da saurin shiga rai tun haihuwar sa, farin jinin shi nanan har yau babu abinda ya dakushe a ciki saima ƙaruwa da yayi, domin dukkansu a kallo ɗaya yaron ya shiga ransu kaunar shi ya kama zuciyoyin su kowanne su burin shi ya ɗauki yaron saidai babu daman yin hakan saboda girmama wa ga Alhaji baba har sai ya gama fadar abin da yasa ya tarasu sannan zasu samu daman yin hakan.

Bayan kamar minti goma da haduwar kowa da kowa a falon Alhaji baba, motar Aslam ta faka a farfajiyar gidan, jiki a sanyaye ya buɗe motar ya fito, tunda ya tashi barci yau gaban shi keta faɗuwa lokaci zuwa lokaci har sai da takai ya gayawa Asmah, abin da ke damun shi, har yake cewa shi bai da tafiya bazai iya fita office ba, ita ta karfafa mai gwuiwa tare da cewa yayta ambaton innalillahi wainnailaihi rajiun, a haka ta samu ta lallaɓa shi ya tafi. Lokacin da kiran gaggawa daga Alhaji baba ya riskeshi ji yayi bugun da kirjinshi keyi ya nunku fiye dana da.

A bangaren Asmah kam ita ma kwarai da gaske jikin ta a sanyaye yake tunda maganar kiran nan ya risketa haka kawai take ji a jikin ta wani Abu Mara daÉ—i zai bakunci rayuwar ta.

Kasa fitowa daga motar tayi saida ya buɗe Mata tare da cewa "bismillah husnah muje Allah yana tare da mu koma meke ciki in-sha Allahu zaizo mana da sauƙi." Mika mata hannu yayi yana sakar mata murmushin karfafa gwuiwa, itama martanin murmushin ta mayar mai kafin ta mika hannun ta ta saka cikin nashi ya mayar ya damƙe gam kamar wani zai kwace mishi ita a haka suka doshi falon Alhaji baba hannun su cikin na juna............

Oum Ummeetarh
07041130088

💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya,Allah kajiqan iyayen mu}

*ASSALAMUALAIKUM SISTERS*

abun d mamaki Tayanda watan axumi yaketa qaratowa cikin Dan taqin lokaci,
Me kika tanadarwa kanki dama yaranmu yar uwa?
Munada kyawawan kayan Yara na dinki masu kyau sosay d bama zakice dinkawa akayiba yaro/yarinya sufito gwanin burgewa kowa yanasan barka,07046881166

Kayanmu sauqinsu yyi har kamar kyautane,zaki iya samunsu dga 2k harzuwa abunda yyi Sama,kizo kiyi sarin kayanmu kisamu alkhairi me tarin yawa,07046881166

Akway takalma Suma kyawawa dgakan 1k zuwa sama,07046881166

Sannan munada tsala tsalan frames d madubai n gyaran gida masukyau d arha sosay,07046881166

Akway leshina d atamfofi,abayas sewanda kikazaba duk a farashi mesauki,07046881166

Karna cikaku d surutu ku kira:07046881166 domin qarin bayani,karku manta alkhairin Tari maganin mantuwa zaku iyashiga Instagram handle namu don ganin kayayyakinmu: everythng_handmade,

Semunjiku 07046881166

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.