Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 17 of 89
Page 31 & 32
Gaba daya gidan ba wani mai farin ciki da wannan auren na Aslam, mummy kam ma fakewa tayi da matsayin sa na d'an fari, tace ita ba ruwanta da batun aurensa, su mami ne uwayen shi ita ba d'anta bane, da haka ta zame hannayenta cikin lamarin ta bar su mami da ummi a ciki.
Su suka had'a lefe bayan Aslam ya basu card d'inshi, yace su cire ko nawa zai isa,
Sunko cire Dan lefe na gani na fad'a suka hada ba algus ko baqin ciki a ciki,
Ta bangaren zainab kam shirye shirye sukeyi ba kama hannun yaro, daga ita har iyayen ta abunka da wayayyu yan boko partyn da suka shirya ya kai kala bakwai, don tun ana saura sati d'aya daurin aure zasu fara program, ta nan bangaren ma Aslam ba qaramin kud'i ya sake musu ba , kamar bai San zafinsu ba
Shiko anashi bangaren shi kadai yaketa shirye shiryen shi, ya qara qyara gidan shi na London road dan can zasu zauna _ part dinshi ba part din da aka kai Asmah ba.
;
Dole ya nemo amir ya bashi hakuri akan abinda ya mishi a wancen lokacin, don yasan duk wani zirga zirga bazai iya shi kadai ba,saida mataimaki, kuma amir d'inne, kadai zai iya tsaya mai yamai komai tsakani da Allah, abinka da 'yan uwa kuma aminai, take amir ya manta da komai na baya suka shiga zirga zirga tare...
Yau yan matan mummy suna cike da farin ciki kasancewar admission d'insu ya fito kuma alhmdllh dukansu sun samu abinda suke so, Asmah da batool masscom, zahra da amira pharmacy , duk university daya suka samu babban university na minna, ranar Monday kuma zasuje su fara registration,
Zaune suke a d'akin su, suna fira batool tace "biki fa na qaratowa inaga yau saura 2 week fa ;". Zahra ta ta'be tace "nifa ko akaina bana kawo wannan bikin, da ayi da kar ayi duk uwarsu daya". Amira tace"ni Allah yasa ma kafin lokacin mun fara attending class , da ko bani da lecture ranar sai naje school "
Asmah tayi murmushi ta fahimci duk wannan abin da sukeyi , sunayi ne don tayata jin haushin wulaqancin da d'an uwansu ya mata ne, tace " duk kallon ku nakeyi ai wlh baku isa ba, bikin ya Aslam sukutum kuce wani ba ruwanku da shi , harda me cewa zata je school ranan ko, akan me to na fahimci ni kuke tayawa jin haushi ko , to wlh na yafe , aini wannan abinda da ya faru gaba ta kaini , ba gashi yanzu xanyi karatuna hankali kwance ba, da bai sakeni ba da yanzu inacan Allah kadai yasan halin da nake ciki" ai ni in kuna sona da gaske har haka kamata yayi ku taya ni murna, don haka ku manta da wannan caftar ku dauka kamar ba'abayi ba, har ankon yini dana dinner na zabar mana a wurin anty ummi,wani atamfa da wani material na gani a status dinta masu kyau sababbin shigowa , anjima bello zai karbo mana gobe sai mu mukai dinki daga nan mu biya gidan ya rabi'ah.
Haka ko akayi washe gari tunda safe bello yaje gidan anty ummi a unguwan darussalm ya amso musu atamfar da material din da Asmah ta zabar musu a matsayin ankon bikin, mummy ce ta biya musu kudin kayan da kyar don da tace ba wani ankon da zasuyi saida suka ta roqonta ta amince,
Wuraren sha daya da rabi suka cikin shirinsu na zuwa kai d'inki daga nan kuma zasuje gidan ya rabi'ah, kamar yadda suka tsara. part din mummy suka biya don gaisheta kamar yadda suka saba kullum, mami bata falo tana ciki don haka suka nemi guri a falon suka zauna jiranta, zamansu ba jimawa mami ta fito cikin shirin fita anguwa, ganinsu yasa ta fadada fara'arta, nan suka shiga gaisheta tana amsawa cikin kulawa
Mami tace"sai ina kuma haka naga anci wannan kwalliya ". Zahra ne ta amsa"mami zamuje mukai dinki ankon mu ne daga nan zamu biya gidan ya rabi'ah kullum complain take mana bama son zuwa gidan ta " mami tace"lallai yaran mummy kunaji da wannan yayar taku harda wani anko kukayi"
Batool tace "eh mami Asmah ce ma ta nace sai munyi ankon, itace ma ta zabar mana atamfar ta yini data dinner ' mami ta kalli Asmah tana mata hararan wasa tace"wato shine mu baza'a nuna mana ankon bako" a ranta kuma tana mamakin sauqin hali irin na Asmah , ace duk wannan wulaqancin da Aslam ya mata har tana wani fitar da anko dan zaiyi aure"
Asmah ce ta katse mata tunaninta da cewa "mami AI ankon fa na yan mata ne ba naku bane " mami tace "ba namu ba mu suwa". Asmah tace "tsofaffi mana". Mami ta zaro ido tare da cewa "ja'ira nice tsohuwa ".
Dukkansu dariya suka sa mata , inda suka tashi suna cewa mami sai mun dawo , tace"to Allah ya tsare, ku gaida min da Rabin da wannan mummunan yarinyar nata mai kwace miji " Asmah da zahra suka amsa mata da to mami, batool tace" kai mami kodai kina kishi ne ta fiki kyau, ta kwace miki miji " mami tace wanna beran tama isa ta kwace min miji ne da wani hancinta kamar Biro, dariya suka saka suna fita falon tare da ce mata mami sai mun dawo.
Asmah ce gaba suna fitowan part din mummy suna kwasan dariyan da mami ta basu hankalinta , kwata kwata baya kan kofar sai ji kawai tayi ta gwabza karo da mutum, da sauri tayi baya tana riqe goshinta tare da cewa wasshh subhanallah...
Shima Aslam dan baya yaja don ganin da wa yayi karo haka, idanunsu ya sarqe cikin na juna , da sauri ta dauke kanta daga kallon shi tare da furta "sorry " a hankali yadda bama lallai yaji ba, amma yajin,
Suma su batool dake binta a baya ganin abinda ya faru , yasa suka shiga firgici da tsoro duk a tunaninsu mari zai kai mata kamar yadda ya saba marin ta a baya. Amma sai sukaga akasin hakan,
Bi tayi ta gefenshi ta wuce suma ganin haka yasa da sauri suka bi bayanta. Mota suka shiga bello yajasu suka bar compound din gidan,
A tsaye yake a inda ta barshi ko qafanshi ya qasa dagawa daga wajen, tunda idanun su ya sarqe da juna ya tsinci kanshi cikin wani yanayi mai wuyan fassaruwa ga kuma faduwan gaban da muddin zai hadu da ita sai ya tsinci kanshi acikin shi, ya tasar mai wannan dalinlin yasa yake kiranta mayya, yoo imba maita ba ace kullum idan ka hada ido da mutum sai faduwan gaba, abinda ya bashi mamaki har yasa ya kasa motsawa kuwa ba komai bane sai ganin yadda yarinyar ta canza gaba daya ,a lokaci daya, ya tabbata inda Dane yadda sukayi karonnan da tuni ta zube a kasa tana kuka tana bashi haquri cike da tsoran shi, amma yanzu ji yadda ta kalle shi a wulaqnce tace mishi wani sorry ta gifta shi ta wuce ba wani damuwa a tare da ita , qwafa yayi ganin mami ta fito.ganin shi nan tsaye yasa tace "yawwa Aslam muje ko" shima sausauta fuskar shi yayi tare da cewa "to mami " , parking lot suka nufa suka shiga mota ko ina zasu ohoo.....
Wani babban shagon dinki inda suka kai dinki sukaje, bada dinku nan sukayi telan ya nuna musu style a wayanshi suka zazzaba sanna suka bashi rabin kudin dinkin suka fito, direct gidan ya rabi'ah bello ya kaisu inda ya barsu said a yamma zai koma ya daukosu......
Sun tarad da ya rabi'ah tana tsaka da aiki kace kace , abokin mijinta barrister Adam zaizo kuma ba qaramin ji dashi mijin ta keyiba don abokin shi ne tun na yarinta, a secondary school suka hadu Wanda yake boarding ne , Allah ya hada jininsu shikenan abota mai karfi ya qullu a tsakanin su , Wanda ya kaiga har iyayen su suma suka zama abokai sanadiyar su.
Barrister Adam ba yaro bane don a kalla zaikai shekara arba'in da biyar ko hamsin, amma abinka da dan gayu dan boko , ba kowa ke gane ya kai wadannan shekarun ba zaka dauka baifi 35 zuwa 38 ba yanada mata daya maryam da yaya hudu, banufen bidda ne iyayen shi gaba da baya nufawa ne amma kuma wayyayyun yan book ne,.
Kama mata aikin sukayi nan da nan kuwa suka kammala, daidai lokacin kuma uncle nura mijinta ya kira waya yace mata
barrister Adam din ya iso, ta kawo mishi abin mosta baki daganan su gaisa, yana falon baqi,
OK tace mishi tana ajiye wayar, ta kalle su tace" kunji ba wai ya iso yana falon abban hanifa gashi ni kuma ko wanka banyi ba sai warin kitchen nakeyi". Zahra tace "to yaya ki kai mishi abin motsa baki daga nan ki gaishe shi , sai kizo kiyi wanka ki koma ' shiru tayi alamar tunani sai kuma tace" no zahra ba haka za'ayi , barin had,a miki abin tabawan a tire kije ki kai mishi, ni kuma nayi wankan sai inje mu gaisa " OK kawai zahra tace mata,...
Kitchen ta shiga ta hado komai data shirya domin taran barrister Adam a tire ta miqawa zahra tace takai palon Abba hanifa ita kuma ta shigab room dinta donyin wanka, ..
Tiren zahra ta dauka ta nufi falon uncle nura da sallama a bakin ta kutsa kai cikin falon, dagawo dukkan su sukayi suna kallonta tare da amsa mata sallamarta ,
A hankali cikin nitsuwa ta qarasa stakiyar falon ta jawo wani dan table dake gefen kushin ta daura tiren akai ta dan matso dashi gaban gaban Barr Adam , dagowa tayi fuskanta sake tace "ya nura ina wuni" Abba hanifa ya amsa da "lpy qlau , yau yan biyun mummy ne agidan namu"murmushi yayi tace "eh yau mun kawu muku ziyara' yace "to madalla munko gode, ina sauran yan'uwanki"tace "suna ciki"yace "ok" juyowa tayi ta kalli barrister Adam da tun shigowarta ya kamata da ido baiko qeftawa tace "ina wuni " shiru yayi don baima jitaba , hankalinshi yayi nisa , gashi dai yana kallonta amma baijita ba said a abban hanifa yace "barrister ana gaishe ka " dan firgigit yayi yace "oh sister ya kike "tace "lpya qlau ya hanya "yace "alhamdulillahi mun sameku lfy tace "lpy qlau " yace"masha Allah"...
Miqewa tayi ta fice daga falon , da kallo barrister Adam ya rakata harta qurema ganin shi , saida abban hanifa yayi gyaran murya , sannan ya juyo da sauri ya kalle shi, d'age mai gira daya Abba hanifa yayi tare da cewa "yane" ajiyar zuciya barrister Adam yayi tare da cewa"finally yau Allah ya hada ni da ita , a cikin garin minna " Abban hanifa yace "ita wa kenan"
"Amaryata da naketa mafarkin na aura"abban hanifa yace"bangane amaryanka ta mafarki ba me kake nufi"barrister Adam yace"kona maka bayani yanzu bazaka taba ganewa ba, yanzu dai bari na tambayeka don Allah ". Abban hanifa yace "ina saurarenka ". Kasa yayi da murya kamar wani zai jisu yace "wannan beautiful young lady dinnan da ta fita yanzu wacece ita" murmushi abban hanifa yayi don ya gano abokin nashi kamar ya zurma yace "kanwar madam ce yan biyu ne ma suke bi mata a haihuwa" barristers Adam yace" wonderful Ashe shiyasa yau tunda na tashibacci naji kamar magnet na Jana zuwa minna a she abinda zan samu babba ne"abban hanifa yace"kamar yaya banfa gane abinda kake nufi ba Mallam" barrister Adam yace "ina nufin ina sonta, ina son aurenta, inason ta zama matata kuma amaryata " bata rai Abban hanifa yayi na wasa yace "kaga Mallam ayi haka dani ba kaima kasan nida maryam 5&6ne bazan bada goyan bayan a mata kishiya ba", Barr Adam kai dai ka Sani tunda ka fara wannan maganar nasan bazakamin abin arziki ba don haka ta hannun rabi'ah zan bi, "oho nidai ba ruwana kaida maryam,". Yace" eh din dama Vance da ruwanka ba ai"
Ranar su Asmah a gidan ya rabi'ah suka wuni sai magrin bello yazo ya daukesu.
Washe gari Monday suka fara shiga school don fara yin registration dinsu.........
Finally zahra ma ta samu nata rabon💃💃💃💃💃💃💃
Date: Oct 13, 2022
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wanna book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.