Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 33 of 89

Page 59 & 60

Da kallon mamaki suke bin junan su, lokacin da wancen karon ya faru ya É—aÉ—e bai manta fuskar yarinyar ba , tsiwar ta da rashin kunyar ta ya dade yana bashi mamaki,

Itama tayi matuƙar mamakin ganin shi a gidan su , kuma a part din mummy, amma hakan bai hanata ɓalla mai harara ba, cikin tsiwa , tace" wai kai Mallam me kake nema danine, ko wani lokaci muka haɗu sai ka bangaje ni, to wallahi kayi na farko kayi na karshe, duk sanda ka sake bangazata saina sa Allah ya isa" ta qareshe cikin murguɗa baki,

Shi abin ma dariya ya bashi, amma ya dake baiyi ba don kar ta rainashi, don ya lura yarinyar kwata kwata bata da kunya, kara hade rai yayi, cikin dakewa yace"waike me yasa baki da nutsuwa ne, kullun in zanganki kina cikin gudu sai kace wata qaramar yarinya , koda yake yarinyar ce, don da ganin ki ba kifi twelve years ba"

Cikin zaro tace "kan uba, nice Mara nutsuwa"

Kafin ya bata amsa su Asmah da kamal sun karaso wajen

Hannu kamal ya bashi suka gaisa, su Zahra ma suka gaisar da shi , a fakaice yake satan kallon Asmah, a zuciyarshi kuma yana raya "lallai kamal yayi dace, yanzu dama Aslam wannan zuqeqiyar yarinyar aka aura mai ya saki, lallai ya tafka babban kuskura, yayi wasa da damar shi ta farko, gashi kuma bai samu dama ta biyu ba,

Ganin sunzo gurin yasa batool ta hadiye sauran rashin kunyar da tayi niyyar sauke mai , amma fa sai banka mai uban harara takeyi, duk yana lura da ita,

Shigewa ciki yan matan sukayi yayinda Dr bash da kamal suka tsaya suna magana,

Suna shiga batool ko gaida mummy batayi ba tace" mummy dan Allah mutumin daya futa yanzu daga part É—innan meye alakar mu dashi ne, ni wlh haushin shi nake ji, ya fiye shegen iyayi wlh"

Mummy zuba mata ido kawai tayi tana kallonta ta inda take shiga bata nan take fita ba sai masifa takeyi , kamar zata ari baki

Suma su zahra duk tsayawa sukayi suna kallonta, saida tayi mai isarta , sannan ta lura da kallon da suke binta dashi,

Kwashewa tayi da dariya mummy tace"sannu mandiya ci gaba mana, ko har kin gama kenen,"

Cikin dariya tace "wlh mummy mutumin bashi da mutunci rannan fa wai marina zaiyi, ranar dinner ya Aslam, har ya daga hannu kome ya tuna naga ya sauke hannun yana kwafa kamar ya Aslam na tafe yana binshi a baya,"

Mummy tace " ai wlh bashir bai biya ni da kakkafta miki mari ba tunda ke kince baki da kunya"

Cikin tura baki ta tashi tana haurawa sama tana dan gungunin, a hankali "tab wlh yana wanka min mari zan rama"

Mummy tace" me kike cewa , ki tsaya kiyi a gabana mana, rasa kunya,"

Su Asmah gaisar da mummy sukayi , sannan suka haura sama dan su kimtsa kafin su fito suyi lunch.

Dr bash yana tuki yana tunanin batool , shi kadai sai murmushi yake yi, can kuma a fili ya furta " kan uba nice mara nutsuwa " cikin kwaikwayan muryanta,murmushi ya kuma saki, kafin a hankali ya furta "ta cika tsiwa" haka kawai ya tsinci kanshi cikin wani irin nishadi na musamman,

Da haka ya iso gidan Aslam , gaisawa sukayi da mai gadi, nan yake shaida mishi matar gidan bata nan amma me gidan yau kwana uku bai saka shi a ido ba, kuma ya tabbata yana cikin gidan bai fita ba , don inda ya fita zai sani ,tunda shi zai bude mishi get,

Cikin mamaki yace ka "tabbatar yana ciki " megadi "yace kwarai yallabai , don ko jiya da hajiya ta dawo ta tabbatar min yana ciki kuma yana lfy"

Dr bash yace " anya kuwa yana lfy, yanzu dai zanje na dauko dan uwan shi Amir zamu shiga mu duba , idan kuma madam ta rigani dawowa ka gaya mata Dr bashir ya zo,"

Megadi ya amsa da to "to yallaɓai a dawo lfy"

Motar shi ya shiga yabar gidan , don zuwa ya dauko Amir,

Karfe biyar daidai na yamma motar brr Adam ta parker a harabar gidan alhaji baba, fitowa yayi daga cikin motar sai zuba kamshi yakeyi, yaci kwalliya cikin dañyar shadda ash colour, sai maiqo takeyi, gsky brr Adam ma ya hadu over,Baki ne dogo kyakkyawan gaske mai siffar dakakkun maza, kallon daya zaka san ma'abocin ibadah ne , saboda yadda fuskar shi ke cike da kamala da haiba, na hasken musulunci,

Megadi ne yamai iso gurin daddy, daddy dama ya riga yasan da zuwanshi don , kuma yasan ba wurin shi yazo ba gurin Zahra ne, don haka ya bada umarnin a kaishi sitting room , a kuma je a gaya wa mummy baƙon zahra yazo

Haka ko akayi mummy dama ta riga tasan za zancen, don jiya daddy ya fada mata komai, itama tayi na'am dashi ganin yadda mijin nata yayi na'am dari bisa dari, tasan bazai yi na'am da abinda zai cutar da É—iyar wani bama balle É—iyar shi,

Wayarta ta laluba ta kira zahra, tace ta sameta a falon ta yanzu yanzu,

Zaune suke dama suna karatun alkur'ani da sukeyi duk bayan sallan la'asar, ranar da Mallam ɗinsu bazai zoba dama haka sukeyi su biyama junan su, dogon hijabine har ƙasa a jikinta irin mai dan kwalin nan,

Miƙewa tayi tace ma su Amira tana zuwa ,mummy na kiranta, a falo ta samu mummy, zama tayi a gabanta tace"mummy ganin,"

Kallonta mummy tayi kafin tace"kinyi baƙo, yana sitting room din daddy, dauki ruwa da lemo ki kai mishi , daga nan kuma ki saurari meya kawo shi gareki "

Cikin dan mamaki tace"tace mummy baƙo muka, nifa banba kowa izinin zuwa gidan mu ba, ita a tunanin ta wannan lecturer ne daya dameta a school,"

Mummy tace "to tunda ya riga yazo sai kije ki gani ko" amsawa tayi da to mummy sannan ta fice , kitchen ta fara biyawa ta É—auki abinda mummy ta umarceta sannan ta nufi hanyar sitting room d'in,

Da sallama ta shiga falon, yana zaune ya ƙurawa ƙofar shigowa ido jira kawai yakeyi yaga ta inda zata bullo, yarinyar da tun gani na farko har yau ya kasa cireta a zuciyarshi daidai da minti daya,

Amsa mata sallaman yayi shigowa tayi cikin natsuwar ta, gabanshi ta nufa ta ajiye tiren hannunta , sannan ta koma baya ta nemi kujera ta zauna,

Sai sannan ta dago kai ta kalleshi, ji tayi gabanta ya yanke ya fadi, da sauri ta dake kai daga kallonshi, don yayi mata kwarjini sosai, gani takeyi kamar tasan fuskar shi amma kuma ta manta inda tasan shi,

Cikin siririyar muryarta tace "ina yini" taja bakin ta tayi shiru,

Tunda ta shigo yake binta da kallo sai yanzu ya tabbatar Ashe rannan ma kallon tsoro ya mata, yanzu ne yake qare mata kallo mai sunan kallo,

Cikin kulawa da maida dukkan hankalin shi gareta ya ̃amsa mata da" ina gajiya faɗeema, ya gida ya makaranta " ta amsa da lfy qlau,

Shiru sukayi dukkansu sai can ya katse shirun da cewa " nasan kin manta ni ko" dagowa tayi ta kara kallonsa a karo na biyu, still bata tunashi ba,

Murmushi yayi yace "dama nasan ni kadai nake kiÉ—a na da rawa na,"

A karo na biyu tace" kayi hakuri dan Allah ban gane kaba, amma kuma kamar na taba ganin fuskar ka a wani wajen"

Cikin jin É—aÉ—i yace"well hakan ma na gode tunda kin tuna kamar kin sanni,naji É—aÉ—i kuma nagode, amma kinga ni tun gani na dake na farko ko daidai da second daya ban qara manta ki a cikin zuciyata ba, nine abokin Abban hanifa, nan da muka hadu a gidan kwanaki kika kawo min ruwa "

Cikin mamaki ta dago tace "Ooh sai yanzu na gane ka, dan kayi hakuri ban gàne ka bane da farko, ya hanya ,ya iyalai".

Yace "lafiya qalau sunce ma na gaida ki"

Tace "aiko nagode ina amsawa,"

Dan shiru sukayi kowa da saƙesaƙen da yakeyi cikin ransa,

Can dai brr Adam ya katse shirun ta hanyar cewa"a gaskiya faɗeema wani magana ne mai muhimmanci ya kowa ni gareki, fatan zaki bani aron hankalinki, kuma ki saurareni da kunnen basira, a gaskiya tun ranar dana fara ganinki , kikayi awan gaba da tunani na , na koma gida na kasa samun natsuwa a zuciyata, kaunar ki tayimin kamun farat d'aya, bansamu kwanciyar hankali ba har saida na dangana da mahaifinki, yayi na'am dani kuma shine ya bani daman nazo gareki na nemi yardar ki da soyayyar ki, ina fatan zaki tausaya min ki karɓe ni da hannu bibbiyu a matsayin mijin aurenki "

Sunkuyar da kanta kasa tayi tunda ya fara magana , ta kasa ƙara dagowa ta kalle shi, wani bala'in kunyar shi ne ya lullbeta,

Kallanta yayi ganin bata da niyar cewa wani Abu yasa yaci gaba da cewa" nidai sunana Adamu Aliyu badegi , ni mutumin bidda ne kuma ƙabilar nufawa, nasan kinji hakan a muryata, ko?" ya qarqare maganar yana murmushi,

ƙarayin kasa tayi da kanta , ci gaba yayi da cewa,"inada matata ɗaya maryama, da yara hudu, ni lawyane me zaman kanshi, bayan wadannan ki faɗi duk wani abin da kike son sani game dani sai na faɗa miki,"

Shiru dai ba amsa, kara zama yayi kusan na 20 minute yana zayyano mata kalaman soyyaya, Wanda shi karan kanshi baisan ta yaya akayi suke fitowa daga bakin shi ba,

Ganin dai bazata ce komai ba yasa yace mata zai koma amma taje tayi shawara da zuciyar ta, zai kirata a waya anjima inya isa gida, amma dan Allah ta yanke shawara mai kyau,

Da haka sukayi sallama bayan ya ajiye mata yan dubu dubu guda a shirin, yace ta saka kati.

Saida taji tashin motarshi , sannan ta iya fitowa daga falon, cikin sauri ta qarasa sashen su,

Dr Bash har wajen aikin Amir yaje ya É—auke shi , suka nufi gidan Aslam har lokacin zee bata dawoba, shiga cikin gidan sukayi, ba kowa falon upstairs suka haura duka sauran É—akunan a buÉ—e suke harda na zee,

É—aki dayan da suka gani a rufe suka shiga knocking, shiru ba amsa,

Daidai wannan lokacin Aslam ya gama sheqa aman shi a nan kan gadon don zuwa yanzu ko tashi matuq'ƙar wuya yake bashi, baga ɗaya, ya fice a hayyacinsa damuwa taima zuciyarshi mugun kamu,

Jin ana knocking yasa ya kasa kunne sosai , muryar Amir dana Dr bash yaji suna sallama , mƙewa yayi daƙer yana layi yana ganin jiri ya nufi ƙofar ya bude musu , yana bude ƙofar ya fada jikin Amir daya fi kusa dashi,

Cikin gigicewa da tashin hankali suka shiga jijjigashi amma ina, daƙer yake bude ido yana lumshewa , kallon Dr bash amir yayi cikin tashin hankali yace " Dr pls do something" bash yace "muje asibiti dashi kawai shi zaifi kaga nan ba wani kayan aiki"

Cikin abinda baifi minti ashirin ba suka isa asibitin da Dr bash ke aiki, ganin su tare da Dr yasa cikin gaggawa aka kawo keken tura marasa lafiya aka shiga da shi ciki, direct emergency akayi dashi

Dr bash ne ya shiga duba shi tare da wasu abokan aikin shi har guda biyu,

Amir kuma yaje bude mai file na asibitin,

Kusan awa É—aya suka kwashe akan shi kafin su gano taka maiman meke damun sa , ruwa aka daura mai, da alluran bacci masu karfi,

Lokacin da su Dr bash suka fito Amir tuni har ya kira gida ya faÉ—a mami, da Abba da hajiya mama tuni har sun iso,

Mami ne ta nufi Dr bash tace "Dr bashir ya ake ciki ina my son a wani hali yake ciki"

Dr bash yace "da sauƙi mami mun samu mun shawo kan matsalar, yanzu yana bacci, mum mishi alluran bacci , zaidan jima yana bacci kafin ya farka, ta haka ne zuciyarshi da kwakwalwarshi zasu huta"

Daidai lokacin daddy da mummy da Kamal suka qaraso, daddy yace " bashir meke damun shi ". Dr bash yace "daddy muje office sai na maka bayani"

Office suka rankaya kusan gaba dayan su, zama wasu sukayi wasu na tsaye, daukar file dinshi yayi yayi rubuce rubuce,

Kallon su yayi cike da tausayawa ganin dukkansu yanda suka shiga damuwa,

Yace, " a gaskiya akwai matsala Aslam ya É—auki damuwa ya saka a zuciyarshi, kuma baya barin kwakwalwar shi ya huta, saboda tunani, ga rashin bacci, ga rashin cin abinci, ulcer shi yayi mummunan tashi, sannan tunanin da damuwar da yasa a rai, yana barazana ga zuciyarshi, idan , badan Allah ya taimaka ba, da yaci gaba da zama a haka tsawon kwana uku komai ma zai iya faruwa dashi, ciki harda bugawar zuciyarshi, kokuma mu rasa shi ma gaba daya"

Tsit dakin yayi kowa da irin abin da yake saqawa a ransa dukkansu basa buqatar sanin abinda ya jefe shi a cikin wannan halin , saboda Abu ne da yake bayyane kowa ya riga ya sani,

Mami ce ta fashe da kuka tana maimaita innalillahi wainnailaihi rajun,mummy ma duk iya dauriyarta da kawaicinta saida ta share hawaye a fakaice,

Dr bash ne ya shiga kwantar musu da hankali matsayin shi na likita , duk da shima cikin tsananin damuwa yake,

Saida komai ya natsa mami ke tambayar ina zainab, nan Amir ya sanar musu abinda megadi ya fada musu na cewa ta fita tun safe gashi har dare bata dawoba,

Daidai lokacin zee na tare da beebalo, fitowa su kenan daga labour kutigi, ana wani biki , ba dangin iya bana , baba beebalo ta jata suka tafi, zama sukayi suma cikin yan biki, suka saje,dangin ango zasu zata dangin amarya ne suma dangin amarya kuma su zata dangin ango ne su,

Haka suka shiga fili suka sha rawa har sunfi wasu dangin ma'auratan zaqewa,

Bayan sun fito ne zee na jansu a mota zata sauke beebalo a gida kafin itama ta koma gida dan dare yayi, karfe takwas ake nema,

Beebalo ta kalli zee tace" kawata kince min kina da aure amma baki taba nunamin mijnki ba koda a hoto ne"dariya zee tayi tace "Abu mai sauki ". Dalleliyar wayarta ta dauka ta nemo hotunan Aslam ta miqama beebalo,

Beebalo na gani ta zazzaro Ido waje a zucyarta ta furata bantan uban can, tabdijan akwai bura'uba kenan dama wannan tsalelen saurayin ne mijin zee, tabdijan wannan shine irin mijin da ta dade tana mafarkin samu, Wanda rashin samun irin shi ya hanata zaman aure, lallai da sake, dole zatasan duk ƙulleƙullen da zatayi ta kara zee ta samu ta maye gurbinta, a gidan Aslam.

Ganin tayi shiru yasa zee tace "yadai naga kinyi shiru ko kinsan shi" cikin murmushin yaƙe tace "wlh ban taba ganin shi ba sai yau gaskiya kawata kinyi dace da miji kyakkyawan gaske ga kudi, masha Allah irin mijin novel muma Allah yasa mu a danshin ku"

Cikin jin dadi zee tace"amin amin kawata" nan ta shiga gaya mata wasu sirrikan Aslam' ita kuma beebalo sai bugun cikin ta takeyi taba nadar abin da zata Nada, kafin su rabo saida ta gama sanin abin da take Neman sani fak akan Aslam, don beebalo akwai shegen wayau, ita kina zee ba wayau sa iya hege😁

Karfe Tara daidai ta iso gida , tun kan tayi parking me gadi ya tare da mummunan labari, nan take hankalinta ya tashi, don duk iya shegenta tana matuqar kaunar Aslam,

Take ta É—auki hanyar zuwa hospital.......

💖more comment more typing💖

Oum ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fi sabilillah🙏
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book ɗin ca duk wscce ta rasa mahaifiya, allah kajiƙan iyayen mu }

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.