Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 83 of 89
Page 126
Kamar yadda daddy ya faÉ—a karfe biyar na yamma daidai ya sauke zee a farfajiyar gidan Aslam, makulli part É—inta daya amsa a hannu Aslam É—azu ya damka mata, har kasa ta tsuguna cike da ladabi tana godiya, yace "Ba komai zainab É—a na kowa ne, Allah ubangiji ya Baku zaman lafiya da zuri'a É—ayyaba." Ta na tsaye har motar shi ya bar harabar gidan, mai gadi ya maida get ya rufe. mai da kallon ta tayi kan É—aya plat É—in da yake nan sak irin nata, ji tayi wasu siraran hawaye sun ziraro mata ko shakka babu nan ne part É—in Asmah, compound É—in gidan tabi da kallo tsab tsab dashi yana nan yadda ta sanshi a baya, sai dai a yanzu yafi da kyau sosai nisa ba kusa ba, domin ga dukkan alamau yana samun gyara da kulawa fiye da lokacin da ta ke gidan a baya.
Jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban na ta part ɗin ta saka makullin da daddy ya ba ta buɗe, sai da ta yi addu'o'i sosai sannan ta kama hannun little suka shiga da sallaman ta a bayyya ne. Falon dumɗum da dubu ba haske kuma ko ina a kukkule, makunnin wuta ta laluba ta kunna take kuwa haske ya gauraye mai falon, bin ko ina ta shiga yi da kallo, take ranar ta, ta karshe a falon ya shiga dawo mata fresh a kwakwalwar ta, ranar da take ta malelekuwa a tsakiyar falon nan jini na kwaran ya daga jikin ta, ranar da Aslam ɗin ta ya saka hannu ya buge ta kamar yana bugun kato tsaran shi, kallon little tayi da yake ta wasan shi, a falon babu damuwar komai a tare da shi, samun kanta tayi da durkushewa a hankali a gurin da take tsaye tare da fashe wa da kuka tunawa d tayi duk abubuwan da suka faru akan zuwan shi doron duniya ne, gashi karshe duk gwagwarmayar da aka sha sai da ya shaki iskan duniya, tayi imani da maganar magaba ta da suke cewa, a duniyar nan babu wanda ya isa ya kashe wani ruhi face sai idan lokacin wannan ruhi yayi, sai dai kawai mutum ya zama sanadi amma badai shi ya kashe shi ba, Allah ne mai kashe wa kuma mai rayawa a duk sanda yaso, shi yake fitar da rayayye cikin matatce haka nan shi yake fitar da matatte cikin rayyaye kamar yadda ya faɗa a cikin alkur,ani mai tsarki.
Ta kusa kwashe 30 minutes a haka sai kuka take tana ƙara tunani da miƴa wuya akan lamarin ubangiji, sai da little ya gaji da wasan shi ya dawo ya faɗa jikin ta yana ce mata zai sha ruwa sannan ta dawo hayyacin ta.
Ko ina yayi kura a part ɗin tun daga kan falo kitchen dakunan barci toilets da sauran su, gashi kuma yamma yayi, hakan yasa cikin sauri ta kau da duk wani tunani da damuwan ta gefe, cike da himma ta fara gyara falukan ta cikin kankanin lokaci ta ƙalƙale shi fess nan kuma ta koma kitchen shima haka tamai ta goge na goge wa ta wanke na wanke wa, dakin barcin ta ta shiga yana nan yadda ta barshi ga kayayyakin ta nan ba'a kawar da komai ba, toilet ta shiga ta fara wanke wa sannan ta dawo dakin shima, ko kafin ta gama duk wadannan abubuwan magrib ta gaba to alwala ta daura, tayi sallah, sannan ta duba store kayan abincin ta data bari na nan yadda ta barsu komai akwai amma bata jin zata iya cin komai a cikin suu, ga kuma little dake ta dan mata kukan rigima alamar yana jin yunwa, hijjab ta zura tare da dauko kudi ta nufi bakin get, mai gadi na ganin ta cike da mamakin ya shiga gaishe ta, rabon shi da ita tun ranar da ya kira hajiya makofciyar su, suka dauke ta rai a hannun Allah zuwa Asibiti,tun daga ranar kuma bai gani ko jin labarin ta ba, yau kuma koda yaga Alhaji babba ya sauke mace da yaronta ta shiga ciki bai taba tunanin ita bace, yadda ta amsa mishi a mutum ce ba kamar a baya ba da wani bin ma sai taga dama zata daga mishi hannu shi karan kanshi abin ya bashi mamaki, cikin girmamawa da dan jin nauyi ta gabatar mai da bukatar ta nasan ya siyo mata ruwan gora saboda sha, taliya idomie da kayan shayi sai mai dasu magi, da dai sauran abin da zata bukata nan kusa irin su sabulu da amo sannan ya biyar ya mata takeaway a safara foods, ba tare da damuwa ba kuwa ya amsa da to ta kawo ba damuwa, kudi mai yawa ta bashi wanda yafi karfin abin da ta bukata tace harda na napep amma dan Allah yayi sauri saboda yaro. Sai lokacin ya kalli yaron, zaro idanu yayi cike da al'ajabi magana fal bakin shi amma ba daman yi, haka ya tafi aiken yana tafe yana sambatu, to abin ne da daure kai, shidai yasan ance ciki ne a jikin ta a ranar da suka kaita asibiti kuma ya ɓare, yanxu kuma ya ganta da yaro mai kama sak da mai gidan.
~Asmah~
Bacci tayi sosai dan sai bayan la'asar ta farka, mummy kam koda akayi azahar bata tashe ta ba, ta barta ne tayi barcin sosai ko zata samu natsuwar zuciya, sai dai tana yi tana leka ta lokaci lokaci, ganin anyi la'asar bata farka ba yasa ta nufi dakin da nufin ta tashe ta, tayi sallolin dake kanta kuma taci abinci. Tana shiga dakin ta tarad da ita a zaune bakin bed ta dafe kanta alamar tashin ta kenan, itama jin motsin an turo kofar yasa ta dago kai mummy ce, kamar yadda dama ta zata, murmushi mummy ta sakar mata, tare da nufar ta ta taba jikin ta don taji koya zazzabin ya sauka, salam kuwa babu alamar zazzabin, alhmdllh ta furta tare da cewa "sannu Asma'u kin tashi ya karfin jikin kuma." Gyada kai kawai tayi alamar da sauki don ji tayi bakin ta ya mata nauyi, mummy tace "to sannu kinji ki daure ki tashi ki lallaɓa kiyi wanka da ruwan dumi zaki ji daɗi sai kizo kiyi sallolin dake kanki kinji." Nan ma sake gyada kai tayi, tana yunkurin tashi, taimaka mata mummy tayi ta mike a hankali ta nufi toilet din wanka tayi da ruwa dumi kamar yadda mummy ta umarce ta, ta kuwa ji daɗin shi sosai, alwala ta dauro ta fito daure da towel, samu tayi mummy ta ajiye mata abaya mai kyau sabo fil da hijab gashi kuma ta shimfida mata pray mat, ko mai bata shafa ba ta saka rigar bayan ta maida kayan ta na ciki data cire tunda bata da wani a gidan, tana cikin sallah mummy ta shigo dauke da tray da kuloli a kai, ajiyewa tayi a gefe, ta zauna tana jiran ta ta idar.
A nutse ta gabatar da sallan ta, bayan ta gama kuwa daga hannun tayi ta shiga kwararo addu'o'i sosai akan lamarin dake tunkaro ta, da kuma rokan allah ya sassauta mata kishi ya bata hakuri da juriyar jure abin da zata fuskan ta a gaba.Tun tana yi a ciki har bata San sanda ta fara yi a bayyane ba, karshe ta fashe da kuka, duk mummy najin ta tana kuma amsawa da amin, a tare suka shafa addu'ar da mummy, tasowa tayi daga kan pray mat din ta iso gaban mummy dake zaune a bakin bed, daura kanta tayi akan cinyar mummy ba tare da tace komai ba, hannu mummy ta daura akan ta, ta shiga shafa mata kai a hankali, sauke ajiyar zuciya ta shiga yi, sun dauki tsawon minti 10 a haka, kafin mummy cikin rarrashi tace "Asma'u ki kwantar da hankalin ki, na fahimci abin da kike tsoro, kar ki saka ma kanki damuwa Aslam yana sonki bazai taba wulakan ta ki ba, idan ma yace zaiyi ninan zan tsaya miki sai inda karfina ya kare, ki kwantar da hankalin ki kinji, in sha Allah kema zaki samu naki É—an da yardan ubangiji ki cire tsoran komai a ranki kinji." Gyada kai tayi alamar to! Mummy ci gaba tayi da kwantar mata da hankali tana gaya mata maganganun masu sanyi ma zuciya natsuwa. Daga yadda ta nutsu tayi shiru ta daina sauke ajiyar zuciyar da take yi mummy ta fahimci zancen ta na shiga ta sosai, hakan yasa cikin dabara ta shiga kowar da ita dabaru zama da mutanen cikin hikima yadda baza ta cuci kowa ba kuna baza a cuce ta. Kwarai ta samu nutsuwar zuciya sosai daga kalaman mummy, ta samu karfin gwuiwar da ta rasa a É—azu, zafin da zuciyar ta ke mata da ragu sosai daga kashi talatin cikin dari. A baki mummy ta bata abinci don tasan idan tace ta ci ba ci zata yi ba, duk da haka bata wani ci ba. Bayan sun gama still mummy bata gaji ba ci gaba tayi da koya mata wasu abubuwan da zasu taimake ta a zamantakewar ta na yau da kullum.
A massallacin kofar gidan yayi sallan isha'i, ana kuwa idar wa bai ba bata lokaci ba ya shigo cikin gidan a kagare yake daya sanya ta a idanun shi, ya damu matuka da son sanin halin da take ciki, haka kawai zuciyar shi ke bashi tana cen tana kuka, duk da yasan mummy baza ta bar ta tata kuka ba.
Koda ya shigo falon mummy ba kowa sai TV dake ta zuba shi kadai, kasa hakuri yayi ya nufi dakin mummy dan yana da tabbacin tana can, da sallama ya tura kofar dakin ya shiga, tana zaune a bakin bed tayi tagumi bata san ma ya shigo ba, ita kadai ce a dakin mummy ta fito ta dauko mata sako, wanda bata San sakon menene ba. Ganin ta a halin tunani yasa da sauri ya karasa gaban ta duƙawa yayi a hankali ya saka hannun shi ya sauke mata tagumin data yi, zuba mishi idanunta tayi da suke nan a ƙorɗe babu kalli ko ɗis gashi sun kumbura sunyi luhu luhu, kallo daya mutum zai san taci kuka yau taba uku lada. Shima idanun nashi ya zuba mata yana kallon ta, take yaji zuciyar shi tayi kunci take yaji wani haushin zee ya kara turnike shi, duk ita ce musabbabin wannan fitinar yana zaman zaman shi ta zo ta jagula mai lissafi, shi wlh da ace shi ta tunkara kai tsaye da amshe ɗanshi zaiyi ya miƙawa husnah kuma bazai taba barin ta ta isa wajen iyayen shi ba balle har su tursasa mishi zama da ita. Cike da tausayawa yace "husnah kuka ko?" Rintse idanun ta tayi saiga wasu sabbabin hawaye sun ziraro, kafin yakai ga kara cewa wani abu mummy tayi sallama, hakan yasa da sauri ya sake mata hannu tare da amsa sallaman mummy,batayi wani mamakin ganin shi a dakin ba domin dama tana tafe tana tunanin kila ya ƙaraso domin kuwa ita tace mai bayan isha'e. Guri ta samu ta zaune take ya shiga gaishe ta amsawa tayi adan sake ba kamar ɗazu ba, duk da dai ba wai ta sake gaba daya bane. Gyara zama tayi tare da cewa "Aslam! Aslam! Aslam!." Ya amsa da "na'am mummy." Tace "sau nawa na kira ka." Yace "sau uku." Tace "dakyau, ga Asma'u na nan zan damka mika ita a hannun ka a yau, koda gigin wasa kada ka kuskaura kace zaka canja mata ko zaka wulakan tamin ita saboda dawowar matar ka uwar ɗanka, nasani ne ku maza kuna da wuyar sha'ani kuma Baku da tabbas shi yasa tun farko nake buga maka warning karka kuskura kar naji kar na gani, domin wallahi! wallahi! wallahi! A wannan karon bazan laminci ka tozar ta min ɗiya akan wata matar ka ba." Cikin tashin hankalin yace "Mummy dan Allah ki dena fadar irin waɗannan kalaman, tsoro suke bani." Daga hannu yayi sama yace "ya Allah kada ka nuna min ranar da zan juyawa husnah ta baya, idan kuma ka kaddara hakan zai faru a rayuwa ta ya Allah na roke ka, ka dauki raina kafin lokacin." Tuna Asmah ta shiga girgiza kai tana hawaye jin abida yake cewa wai Allah ya dauki ranshi, to ita kuwa meye makomar nata ran idan babu nashi ran, domin Aslam shine ran nata ran. Ita kanta mummy sun bala'in bata tausayi har saida ta dauke kwallah a kafaice, ta kima kara tabbatar wa ba karamin so Aslam yake ma Asmah itama Kuma ba karamin so take mishi ba, shiyasa ta ke tsananin kishin shi. Lallai zee ta shiga hakkin su, amma kuma baza suyi jayayya da ikon Allah ba domin Allah kadai yasan abin da yasa ya turo ta cikin su a daidai wannan lokacin ita dai adduar ta shine Allah yasa zuwanta cikin su yazame musu alkhairin duniya da lahira. tana da tabbacin yadda suke son junan su soai haka mawuyacin abu ne aslm ya juya mata baya sai fai idan sun haɗu da shu umancin mace domin dai tasan wasu matan shu,umai ne Kasa ci gaba da faɗin abin da tayi niyyar faɗawa Aslam ɗin tayi, domin idan tace zata yi magana zata iya fashe wa da kuka, mikewa tayi ta mikar da Asmah tsaye ganin haka yasa shima ya mike, mika mata wani babban leda tayi tace "in kinje ki duba na miki bayanin komai a ciki, kuje, ki bishi kuje gida Allah ubangiji ya muku albarka, Allah Kuma ya cika muku burin ku ya baku ƴaƴa masu albarka." Rungume mummy tayi ta fashe da kuka, shi kam Aslam gaba yayi ya bar ɗakin ya dawo falo, domin sauraren kukan ta zai iya saka shi shima ya fashe da kukan a yadda yake jin kukan ta na taba zuciyar shi. Dakyar mummy ta samu ta raba ta da jikin ta, ta kamo hannunta ta zuwa falo tana zuwa ta kama hannun Aslam ta saka mishi hannun ta a ciki tace "kuje Allah ya baku sa'a." Da sauri ta juya ta haye upstairs. Jawo ta yayi ya tallabe ta a jikin shi ta gefe, a haka suka iso parking lot ya buɗe motar shi ya sanya ta a gefen mai zaman banza shima ya zagaya ya shiga gefen direba, ya bar gidan yaso ya kaita tayi sallama dasu Mami da Kuma Alhaji baba da hajiya mama, to yadda yaga yanayin ta yasan hakan bazai yuwu ba, har suka iso gida babu wanda yace ma wani kala a cikin su, zuwa lokacin ta daina kukan sai shehsheka da ajiyar zuciya take sauke wa akai akai. Lokacin da motar su tayi parking a compound ɗin gidan su daga shi har ita idanun su akan part din zee ya sauka, ganin wuta a kunne ko ina ya dauki haske hakan ne ya tabbatar musu da cewa daddy ya cika aikin shi wato ya kawo zee gidan ta a matsayin matar Aslam a karo na biyu kamar yadda ya faɗa......
Allah sarki Mr and Mrs Aslam sabuwar rayuwa muna muku fatan alkhairi nida mutane yana dana ta biyu fans
Oum Ummeetarh
07041130088
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.