Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 74 of 89
Page 118
Saidai sukayi zaman fiyye da awa uku sannan layi yazo Kansu, zuciyar beebaloo wasai yau tazo inda take da tabbacin za'a share mata kukan ta, tare suka shiga cikin bukkar mallam ɗin ita da hajo, guri ya nuna musu suka zauna kan shimfiɗar buzu, so ɗaya beebaloo ta iya kallon fuskar mallam kamsusi da sauri ta dauke kai gabanta na faɗuwa, duk inda muni yake Allah ya tattarawa mutumin nan, baƙi ƙirin dashi, gashi dan cukuli kamar a kife da kwando sai katon kai, yasha wani uban rawani ƙato a kanshi, gaban shi kuma kasa ne mai kyau fari tas , hannun shi rike da wani dogon carbi irin mai guda dubu ɗinan yana ja sai wani musmus yake yi da baki.
Tun shigowar su ya kafe mici micin idanunshi akan beebaloo, yana kare mata kallo daga Sama har kasa, yana sauraren radar da aljani dan misra ke mai a kunne game da ita, lallai ta tafi da nutsuwa shi, gani É—aya yaji ranshi ya biya kuma bawai na lokaci daya ba inso samu ne yana bukatar ya aureta, ido ya zura mata kamar mai bukatar hango wani abu a jikinta yayin da ita kuma ta kasa kara dagowa ta kalle shi.
Hajo ne ta fara cewa cikin dukar da kai da tsantsar ladabi "barka da war haka ya babban malami,
malamin malamai na duniya baki daya, gani na sake dawowa gareku da bukatata,fatan na same ku lafiya" sai lokacin ya dauke idanunshi akan beebalo ya dawo da shi kan hajo, fuska a murtike babu alamar fara'a yace "mun amsa gaisuwa hajo, fatan kin isa gida lafiya" tace "lafiya lau mallam aiki yayi kyau tun kafin na ƙarasa gida ma komai daidaita yanzu haka ko kara na ajiye baya iya tsallakewa." Sai lokacin mallam kamsusi ya saki wani shegen murmushi, cikin sa'a saidai lokacin beebaloo ta ɗago kai da niyar ta saci kallon shi a karo biyu, idanunsu ya sarke dana juna, ba shiri ta mayar da kai kasa tana karanto duk addu'an daya zo bakinta, ita wallahi tsoro yake bata, gaba daya fuskar shi kamar ta buri hancin nan a nane.
Lokaci daya ya maida fuskar shi ya murtike sannan ya fuskanci hajo yace"kwarai kuwa muna da labarin komai domin tun kina nan gabanmu zaune muka aika dan auta yaje ya cika miki aiki,yanzu me ke tafe dake." Hajo tace "Allah yaja zamanin babban malami wannan kawata ce itace na rako gareka da bukatar ta." Maida kallon shi yayi kan beebaloo, yana ci gaba da binta da wani irin mayen kallon har wani lashe lips yakeyi kamar wani tsohon maye.
Saida ya kalleta son ranshi sannan yace"menene bukatar ki." Firgita tayi ta kara kasa da kai jikinta na rawa jin yana mata magana, shiru tayi ta kasa magana, ganin haka yasa hajo ta mika hannu ta tsunguleta a gefen ciki, dagowa tayi ta kalli hajo suna hada ido ta mata alamar yi magana mana, baki na rawa tace"ma malam, umm dama dama, wani ne Wanda nake son ya aure ni, nake son shi, shi kuma baya sona kwata kwata baima San kalar fuskata ba, shine nake son dan Allah a taimaka min ya soni ya aure, dan Allah mallam."
Tunda ta fara magana mallam kamsusi ke gyada kai,shi kadai yasan me yake sakawa a ranshi, yace "to zamu taimaka miki mu miki abinda ya dace, kuma bama bukatar ko sisin ki, zamu muki aiki da zaici kamar yankan wuka, amshi nan" ya karashe maganar yana mika mata wani Abu nanade cikin ganye, hannu na rawa ta karba tana godiya ammafa idanunta na kallo gefe don ta kasa haɗa ido dashi, yace" kije ki daka wannan ciyawar ki shanya ya bushe ki raba shi gida biyar ki jiƙa kashi ɗaya kisha, kashi ɗaya ki zuba a ruwan wanka, kashi ɗaya kiyi hayaƙi dashi kashi ɗaya ki zuba a baki ki tattauna kashi daya kuma ki kwaba da fitsarin ki ki shafe a jikin ki da daddare idan zaki kwantar, to insha Allah in dai kikayi yadda nace zaki mallake shi duk inda kike zai biyo ki ya aureki, zai soki sonda bai taba yiwa wani mahaluci a duniya ba, zaki juya shi sai yadda kikayi da shi da dukiyar shi." godiya suka shiga jero mai ita da hajo kamar bakin su zai tsinke.
Dakatar dasu yayi mici micin idanunshi nakan beebaloo sai murmushi yake yi, yana lasar lips, lambar wayar shi ya rubuta ya mika beebaloo dan yasan tabbas ta aikata abinda ya umarceta daidai dole zata bukaci lambar shi.
Yadda suka shatata da kafa sukaje haka suka kara shatatowa suka fito saidai wannan karan ko kadan beebaloo bata ga wahalar hakan ba tunda ta samu biyan bukata, dan gani take kamar ta auri Aslam ta gama, banda yadda zata sha soyayya da Aslam da yadda zata zuba mulki a gidan shi babu abinda take tunani,sai alkawarurruka take ma hajo kala kala, harda cewa ita ce zata zama mai bata shawara na hannun daman ta, a wannan tsukukun kauyen suka kara kwana washe gari suka kara hawa kabu kabu ya fitar titi suka samu mota suka dawo gida.
Koda ta dawo bata bi takan faɗan da iyayenta ke mata ba suna tambayar ta ina ta je ta kwana har kwana biyu, tace musu tafiya tayi kuma bata ga daman ta gaya musu bane,taja tsaki tare da shigewa dakinta ta banko kofa yana gungumi da kananun zage zage ƙasa ƙasa.
Kuka mahaifiyar ta ta fashe da shi, tana cewa "ni kike zagi beebaloo insha Allah saikin haifi wacce zata miki dukan tsiya kije kici gaba duniya ce ai faɗi gareta." Mahaifinta ne ya shiga rarrashin mahaifiyar ta, yana kwantar mata da hankali da cewa"yi hakuri marka baryi mata baki, aiko baki buɗi bakin ki kince komai ba, wannan hawaye da tasaka kika fitar hakkin su ya ishe ta." Cikin kuka mahaifiyar ta tace"mallam barni nayi mata baki, wannan wannan baza taga annabi ba, taƙi zaman aure tasa ana zagin mu a gari, sannan mu kuma a gida bata kyale mu ba, cin mutuncin yau dabam na gobe dabam, aiko bamuyi tsirar komai ba baci albarkacin haihuwar ta da mukayi, wasu ma banza da bamu Haifa ba sun girmama mu balle ita." Girgiza kai mallam yayi cikin tsananin takaici, yace "wallahi babu abinda yafi ban takaici game da beebaloo irin kin zaman aure da tayi abin yana taɓa min zuciya bani fatan na mutu na barta a haka tana gantali."
Tana jinsu daga É—aki sai tsaki takeja, tace " yen yen yen yen, mugaye kawai yan bakin ciki, zanyi aure ai zan auri zabin raina cikar burina, kyakkyawa mai kuÉ—i dan babban gida, wallahi inna yi kudi bazan taimaka muku ba yadda na same ku a tsiya ce haka zan barku ku mutu a tsiya ce." Ita kadai take ta sababin ta basu ma San tanayi ba.
A ranar ko hutawa batayi ba ta aikata duk abinda mallam kamsusi ya umarce ta dayi, cike da annashuwa take aiwatar da komai, duk yadda yace mata haka tayi ba tare da ta yi mistake ba, da tazo kwanciya tayi fitsayi ta kwaba kashi na, karshen ta shafe jikin ta da shi, takwanta da yaki nin ta auri Aslam ta gama.
Washe gari beebaloo ta farka da wani saban lamari, tun da ta farka taji a rai da zuciyar ta babu Wanda take son gani sai mallam kamsusi, zuciyar ta babu Wanda take so da kyauna sai mallam kamsusi, da ta rufe ido mummunan fuskar shi ya mata gizo, zuciyar ta har wani tafasa takeyi saboda tsananin kaunar shi, ji takeyi idan bata sanya shi a ido ba zuwa dare zaucewa zatayi tuni ta manta da wani Aslam, mallam kamsusi kawai take ji da gani, hannu na rawa ta jawo Jakarta ta zaro number shi daya bata, ba shiri ta antaya mai kira, yana daga wa, ta sauke wani wawan ajiyar zuciya kamin baki na rawa ta shiga gaishe shi, tare da cewa "mallam beebaloo ce kawar hajo." Daga cen bangaren yace "nagane ya akayi beebaloo." Take ta fashe da kuka kafin kuma ta tsinci bakin ta da cewa "mallam dan girman Allah ka taimaka ka aureni wlh sanka nakeyi, bazan iya rayuwa babu kai ba, na fasa auren Aslam É—in yanzu kai nakeso na maji na tsane shi kwata kwata a rayuwar dan Allah ka taimakeni ka taimakeni ka aure mallam." Wani shedanin murmushi mallam kamsusi ya sake tare da cewa "karki damu beebaloo zan taimakeke na aurenki kamar yadda kina bukata, zaki zauna dani inada mata biyu, kuma a wannan kauye da kikaje anan nake rayuwa ta kin amince zaki zauna acen." Baki na rawa tace "wlh mallam na amince ko ta biyar ce ni na yarda, kauye kuwa ko gaba da nan ne zan je." Yace "to shi kenan ki sanar da mahaifan ki zanzo jibi."
Kafin jibin kullum sai ta kirashi fiyye da so goma a rana, ta zama wata zautacciya soyayyar mallam kamsusi kawai ke nukurkusar zuciyar ta,gaba daya bata cikin haiyacin ta, ta sanar da iyayen ta za'a zo Neman aurenta jibi, mahaifinta dan murna kamar ya zuba ruwa kasa yasha, ko ba komai zai rabu da mugun iri.
Jibin kuwa mallam kamsusi ya dira a cikin garin minna shi da mukarraban sa su uku, ba ɓata lokaci ya kira beebaloo, da kanta tazo ta tare su, jikina rawa ta masu jagora har cikin zauren gidan su saida ta gabatar musu da lafiayyen girkin da ta musu suka cinye Tass suka kora lemon kwalba sannan ta musu iso gurin mahaifinta, wanda shida kanin shi da abokin shi ne suka tare su.
Mahaifinta yayi mamakin ganin mal kamsusi amatsayin Wanda beebaloo ta tsayar zata aura, kasancewar ya San burin beebaloo nasan auren mai kuÉ—i kuma kyakkyawan na miji, amma wannan ai ko cikin munanan sarkin su ne, yadda take ta rawan jikin ya dauka wani shahararraen dan masu dashin da take burin aura ne ta samu.
Cikin abinda baifi awa daya ba suka gama tsayar da duk abinda zasu tsayar ciki harda daura auren beebaloo da mallam kamsusi, a ranar kuwa ya bukaci tafiya da ita,ba Wanda ya hana shi matar shi, suma iyayen nata neman kai suke da ita, itama kuwa burin ta kenan ta ganta gidan shi matsayin matar sa shine kwanciyar hankalin ta.
Mutum biyu ne kawai suka mata rakiya daga kanwar mamarta uwa daya uba daya sai, kanwar ta mai bi mata da take aure nan kusa da su da Æ´aÆ´an ta biyar.
Tun a hanya yan rakiya suka fara shan jinin jikin su, itako beebaloo ko a jikinta, basu shiga tashin hankali ba saida suka ga yadda ake ta zurarawa da su cikin gungurmin daji a mashin, tafiya yaki karewa, hankalin su bai idasa tashi ba saida akazo gurin tafiya da kafa, sunayi suna hutawa ,kanwar mamarsu kuwa sai zagin beebaloo takeyi take, tana cewa da tasani da bata zoba, a galabaice suka isa.
Gida ne fankacece mai dauke da dakuna hudu ƙananan, daya uwar gidan daya na mai bi mata daya na miji sai daya na yara wanda nan aka gyara wa beebaloo,abinda yaba yan rakiyar beebaloo matukar mamaki, yadda suka ga da murna da farin ciki sauran matan mallam kamsusi suka amshe su, tuni suka gabatar musu da tuwan dawa da miyar gari harda ruwan randa mai sanyi, gaba dayan su ba wacce ta iya hadiye lomar farko na tuwon, saboda rashin dadin sa mayar salam sai uban yaji, karshe da yunwa ta ciwo su dole dama tuwan sukayi suka sha shi kamar koko, Allah Allah suke gari ya waye su baro kauyen.
Da safe uwar gidan mallam kamsusi ta kawo musu kunun garin dawa da dumame, cikin fara'a ta gaishe su babu alamar kishi ko kaÉ—an a fuskarta, kasa hakuri kanwar beebaloo tayi tace"baiwar Allah naji ance mana kece uwar gidan shi, kuma banga alama ba nace koba ke bace." Cikin washe baki tace "wlh nice uwar gidan shi." Da mamaki ta kara ce mata"shine babu ko alamar kishi a fuskar ki." Kallonta matar tayi da mamaki tace"kishi fa kikace baiwar Allah,kishin wa?kishin mallam wai, aini idan yau mallam zai karo wata matar ya cike ta hudu sai nafi kowa farin ciki, ko ba komai raba kwana zamuyi, aini nafi kowa farin cikin da auren nan na mallam badan kar nayi karya ba da sai nace har shi nafishi farin ciki da auren, kardai na cika ku da surutu bari na barku ku kimtsa." Ta faÉ—a tana mikewa ta fice, kallon juna yan rakiyar beebaloo sukeyi, cike da mamakin wanga lamari, to duk yadda akayi a kwai lauje cikin nadi.........
Oum Ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
FisabilillahðŸ™
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
109
~MALAYSIA~
Bayan wata uku
Dad ɗin zee na hango zaune a cikin wani ƙaton falo mai dauke da kujeru sama da guda hamsin, a cikin falon akwai wani ɗaki mai wawakeken kofar glass, zaune yake ya zuba tagumi da hannu bibbiyu yayinda gabanshi kaɗan mum ne sai safa da marwa takeyi ta kasa zaune ta kasa tsaye, basu kaɗai bane a falon a kwai wasu mutanen amma kowa da abinda ya dameshi babu mai shiga harkar kowa,
Daga kaina nayi na kallin sunan da ke rubuce a saman dakin ~labour room~ abunda idanuna suka hango min kenan.
Suna a wannan yanayin bini bini dad kan amsa call a waya yayinda mum kam gaba daya bata cikin hayyacinta, sai yi take tana aza hannu a kai tana saukewa, can bayan kamar 30 minutes sukaga an budo kofar glass din an fito, wani mutumi ne fari sol kamar zabiya sanye da kayan likitoci ya fito daga dakin, da sauri Dad ya zabura ya mike,shida mum har suna rige rigen isa gareshi, a ruÉ—e. Dad ya fara cewa "Dr ina daughter ta haihun,ko har yanzu?" Mum ma cewa take "pls Dr ina daughter na, wani hali take ciki, Dr idan abin bazai yuwu ba kawai ayi mata theater" Dr kam rasa ma wani amsa zai basu yayi, ganin yadda suka tare shi, gashi shi kuma sauri yakeyi yasa yace musu"excuse me pls" tare da dojewa ya wuce su da sauri, hannu mum ta daura akai tana hawaye tare da ambaton "innalillahi wainnailaihi rajiun" Dad kam bin bayan Dr yayi da sauri saidai kafin ya cin masa ya shige wani office, Wanda babu mai ikon shiga sai likitocin asibitin, dawowa yayi jiki a sanyaye ya nemi gurin shi Nada ya kuma zama.
Tsakanin shida mum an rasa mai jarumtar rarrashin wani, kimanin awa goma kenan da suka kawota asibitin, tun cikin dare naƙuda ya tasar mata gadan gadan, ba shiri kuwa aka shige da ita labour room, saidai har zuwa yanzu karfe goman safe bata haihu ba kuma ba Wanda yace musu wani Abu game da ita, saidai kawai gani sukeyi likitoci da nurses nata zirga zirga a ɗakin.
Hankulansu gaba ɗaya yakai matukar ƙololuwar tashi, tsoron su gaba ɗaya kar su rasa
ta, itace farin ciki su, ita kaÉ—ai suka mallaka suna matukar tsoran rasata.
A wannan yanayin maimakon su tayata da addu'a, amma ina abinka da jahilai, Dad sai zufa yake hadawa idanunshi sun rine jajur,in yayi ya lailayo ashar ya É—ura wa Aslam, yayinda mum ta kasa tsaye ta kasa zaune sai fareti takeyi tana risgan kuka.
Bayan mintunan da basu gaza goma ba wata nurses ta fito daga É—akin, nan itama suka mata caa aka, kallon mutanen falon tayi fuskarta dauke da murmushi tace,"su wanene iyayen zainab Abdussalam" bakin na rawa Dad yace "yes mune mune" mum ma tace "eh nice mahaifiyar ta, wani hali take ciki" nurse tace "alhmdllh ta sauka lafiya yanzu an samu baby boy," tsabar farin ciki mum batasan sanda ta rungume nurse ba, Dad kuma kallonta yayi yace "nurse wani hali take ciki" cikin murmushi tace," tana lafiya yanzu haka ana gyarasu ita da babyn nan da yan mintoci za'a fito da ita zuwa É—akin Hutu, sai ku samu ku ganta" dad" ajiyar zuciya Dad ya sauke tare da shiga jero ma nurse É—in godiya, nan kuma ya É—auki waya ya shiga kiraye kiraye.
Nurse kam da'ker ta samu ta kwace kanta a hannun mum ta koma É—akin da ta fito.
Ba'afi 20 ba kuwa aka gunguro zee daga labour room zuwa É—akin Hutu, sai lokacin su mum suka samu ganinta, tayi fiyaut da ita, ta kara haske, basu DaÉ—e a É—akin ba akace su fita su barta ta samu barci sosai an mata alluran barcine, kasancewar ba karamin wuya tasha ba, tayi nakuda mai tsayi kamin ta samu ta haihu da taimakon kwararrun likitocin asibitin.
Babyn dake nannade cikin farin shawel an mishi wanka an shiryashi cikin tsadaddun kayan sanyi aka mikoma mum, hannu na rawa ta karɓa, tsurawa yaron idanu tayi tana kallo, Dad dake tsaye ganin haka yasa shima ya matso don yaga mai take kallo haka, abinda ya faru da mum ne shima ya faru dashi, kallon yaron sukeyi babu ko keftawa.
Bacci yake yi idanunshi a kulle fari sol ƙato da shi mai kama da Aslam sak, babu abinda ya banbantasu,kwata kwata bai dakko komai na zee ba, duk da mum da Dad basa kaunar Aslam hakan bai hana ɗanshi samun kyakkyawan matsuguni a zuciyoyin su ba, farat daya yaron ya shiga ransu, a kallo na farko.
Gaba ɗaya sun shagala da kallon yaron saida sukaji, muryar nurse tana musu magana sannan suka dawo hayyacinsu,saƙon Dr ta sanar musu na cewa da yayi su same shi a office, Dad ne yabi bayan nurse din zuwa office ɗuin Dr yayinda mum ta rungume yaron tsam a kirginta tanajin wani irin son shi da kaunar shi na huda kofofin zuciyarta.
Saida zee ta kwashe awa shidda kwarara tana barci kafin ta farka, wuraren la'asar, zuwa lokacin kam asibiti ya cika makil da yan'uwa da abokan arziki yan gayu masu abin hannu,yawancin su ma turawa ne wadan da su mum ke hulÉ—a dasu, kowa ya dauki yaron nan kallon daya zakaji ya shiga ranka, da alama dai baiwarsa ce hakan.
Zee ta farka da sauƙi sosai don bayan Dr ya duba ta, ya tabbatar musu nan da gobe ma za'a iya sallamarta taje gida abinta, bayan mum ta bata shayi mai zafi tasha ta kuma sha magunguna, sannan aka bada daman mutane su shiga su dubata, kowa barka yake mata, bata iya amsawa sai smiling kawai take musu, lokacin da aka bata babyn kuwa tsura mishi idanu tayi tana binshi da wani irin kallo, babu abinda take gani a fuska da jikin yaron sai Aslam dinta, take wani irin kewa da kaunar mijinta ya turniketa, rungume yaron tayi sosai a jikinta tana jin wani irin kaunar shi na huda zuciyar ta, bata San sanda ruwan hawaye ya wanke mata fuska ba, ta shiga risgan kuka harda sheshsheka, ganin haka yasa mum ta miƙa mata hannu alamar ta bata yaron girgiza mata kai tayi alamar A'a dole mum tayi hakuri ta bar mata abinta.
Zuwa dare babyn ya fara kuka, Dr yace ya kamata a bashi abinci yunwa yakeji, Dad yace Dr ya rubuta musu madaran da za'a dinga bashi yaje ya siyo, da mamakin su ji sukayi zee tace , A'a kar a siyo madaran ita zata shayar da É—anta, Dr yace well dama haka ake bukata, nan wata nurse ta gyara mata shi sosai ta koya mata yadda zata rikeshi a yayinda da zata shayar da shi, nonon aka sa mai a baki ba shiri kuwa yaro ya kama yana tsotsa, duk da matsanancin zafin da takeji hakan baisa ta fasa shayar dashi ba, nurse din data fahimci tanajin zafi ta shiga kwantar mata da hankali da cewa karta damu zai daina, idan ya kwana biyu yana sha, shikenan baza ta kara jin zafi ba kuma.
A asibitin suka kwana zuwa washe gari ta ƙara samun sauki sosai don haka Dr ya rubuta musu sallama suka dawo gida, kulawa sosai zee ke samu daga gurin iyayenta ita da little Aslam dinta, wata babban nurse mai zaman kanta, wayayya mai wadataccen ilmi Dad ya daukar musu ita ke kula da komai nasu ita da babyn bangaren wanka tsaftar su da abincinsu, kai komai ma daya shafe su.
Zee taji dadin yadda iyayenta suka karbi yaron da yadda suke nuna mai kauna da kulawa, bata taɓa zaton haka ba, ganin yadda suka dauki karan tsana suka dorawa uban ɗan.
Kafin sati ya zagayo tayi bulbul ita da babynta gwanin sha'awa, jego takeyi na yayan gata, baza ayi taron suna ba, raÉ—in suna kawai za'ayi dad ne ya siya duk wani abinda ake bukata na radin suna kamar rago da sauransu,tambayarta sukayi sunan da take so a saka ma É—anta babu kunya ko kara tace Muhammad Aslam, haka ko akayi, duk da Dad yaso ace sunanshi ta zabar wa yaron.
(kuji min Dad da ƙoƙari wai da sunanshi ta zaba😒 babu kunya ba tsoron allah cikin da yayi niayyar hallakawa)
Hankali kwance take jegonta bata da matsalar komai babu abida ke damunta sai kewar mijinta, bayan haihuwartan nan , abin ma saiya daɗa nunkuwà , kullum dashi take kwana take tashi a zuciyarta ji take kamar tayi tsunstuwa ta ganta a agabanshi, ta mika mishi ɗanshi, cikin farin ciki,ta kusa kai matakin da baza ta iya jurewa ba, jira takeyi yaronta yayi kwari, ta lashi takobin zata koma gidan mijinta koda son ransu ko babu, koda tsiya koda tsiya tsiya.
~9ja~
Yau kimanin wata biyar kanen da auren yan matan mummy,kuma har zuwa wannan lokacin cikinsu babu wacce ta taba zuwa gida da sunan ganin gida, kowacce tana gidanta hankali kwance, duk da kuwa cikinsu ba wacce batayi nacin son zuwa gida ba amma mazajen suka hana wannan kuwa umarnin alhaji baba ne.
Soyayya kamal da khadija ba'a magana, tattalin da kulawa suke ba juna na musamman, idan kaga yadda suke gudanà r da rayuwarsu zaka dauka sunyi shekara goma suna soyayya kafin suyi aure, a halin yanzu Khadijah Nada cikin ta dan wata huɗu.
Haka ma Amir da Amira sukam bama a magana, kalar nasu salon soyayya ta dabance, basa jin kunyar uban kowa a gaban kowa nuna ma juna soyayya sukeyi, ƙiri ƙiri mutane suka guji zuwa gidansu, saboda idan kaje indai kana da kunya, ta baza ka iya awa ɗaya a gidan ba,suma dai a kwai cikin ɗan luv, saidai fatan Allah ya raba lafiya.
Su batool ma yanzu komai nomal,babu abinda suke sai shan soyayya da cokali mai yatsu, bangaren yadda sukeji da cikin su kuwa ba'a cewa komai,tunkan a haife shi, shikaran kanshi cikin yasan shi dan gata ne, abinka da masu abin duk sati ake scanning, ta bangaren maah ma ba'a barta a baya ba, duk abinda ta gani indai na jariri ne siya takeyi ta ajiye, abin kwalama kuwa na masu cikin kullum cikin yi takeyi tana aikama batool dashi, bama ci takeyi ba wani bin saidai Dr yaci idan Wanda zai iya cine, ita dai barta da cabbage dinta, yanzu kam an samu ci gaba ta daina cinshi gaya, saidai ta kwada da kulikuli taci, rigima kam yayi sauƙi a gurin batool saidai kunsan ance mai hali baya fasa halinsa, duk da haka duk randa ya tabota haka zata kwana tana masifa, musamman yanzu da wata Dr a gurin aikinsu ta nace tana sonsa, tunda batool ta samu labari ya shiga uku ko minti talatin ya kara akan lokacin da yake dawowa haka zai sameta ta cika tayi fam, komai zai ce mata baza ta yarda ba kawai gurin Dr basira ya tsaya, kishin sa take sosai da sosai ji take da tana da hali da nikab zata saka shi ya dinga sakawa, saukin shi ma yanzu yana da loggonta data fara zai lalubeta ya fara sakar mata zafafan romance daga nan zancen zai mutun sai kuma na gobe.
A bangaren zahra kam, yanzu babu abida zamu ce sai alhmdllh, tsakaninta da miji babu komai sai tsantsar soyayya da kaunar juna, da gasken fa baby take a gurin Barr Adam ji yake da ita kamar Yar jinjira, musamman yanzu data samu ciki, kula yake bata na musamman kamar ya hadiyeta, tsakanin da maryama yanzu kuwa babu komai sai girmama juna da mutunta juna, dama zahra kwata kwata bata da matsala, matsalar daga maryama ne, kuma a halin yanzu gaba daya tayi laushi, bayan dawowarta Barr a gaba ya sakata ya mata nasiha tare da sanar da ita wlh ta gode ma Allah daya haÉ—a ta da kishiya irin Zahra bata samu mai irin halinta, nan ya sanar da ita cewa zahra ce ta tirsasa shi ya dawo da ita badan haka ba da har yanzu tana cen, take taji wani nadama ya shige ta lallai ta gode ma Allah dabai haÉ—a ta da mai irin mugun halinta ba don ta Tabbatar inda itace a matsayin zahra,da wlh zahra tabar gidan kenan har a bada asaidai a bita da takardan ta, tayi nadama, ta tuba taubatan nasuha, washe gari kuwa har part É—in zahra taje ta same ta nemi gafarar abinda ta mata, Allah sarki zahra dama bata riketa a raiba, nan dai tace ta yafe mata, tashi tayi ta rungume ta tana mata godiya, a haka Barr ya samesu, ba karamin dadi yaji a ranshi ba, take ya haÉ—a su ya nusu nasiha, tare da nuna musu irin tsantsar farin cikin da yake ciki a ranar saboda hada Kansu da sukayi, tun daga ranar kuwa suke zaune lafiya abin su, yara yanzu sun zama yan gata masu uwaye biyu, maryama suna kiranta da mummy zahra kuma suna kiranta da mum, dakinsu nanan a part din zahra data ware musu, lafiyayye Dan yama fi dakinsu na part din maryama haÉ—uwa, in sunga dama su kwana a gurin mummy insun ga dama su kwana gurin mum, maryama ce ta fara gane zahra nada ciki, aiko dai tayi farin ciki har zuciyar ta, take ta shiga tsokanarta tana kiranta da maman yan biyu, tun zahra na daukar abin da wasa har dai lamarin ya tabbata, saidai muyi fatan Allah ya raba lafiya.
A bangaren su Asmah kam yanzu sun wuje romeo da Juliet, soyayya suke zubawa kamar zasu cinye juna, da'ker da sidin goshi Asmah ta samu Aslam ya koma wajen aiki, shima da yarjejeniyar, yana aiki suna video call, haka dai tace mishi ta yarda, ta samu ta lallabashi ya tafi ranar farko daya fara zuwa, yana isa ko office bai shiga ba ya kirata ƙin ɗagawa tayi dan burinta a halin yanzu bai wuce ya maida hankali kan aikinshi ba, cikin abinda baifi awa daya ba ya mata missed call yafi hamshi ta share, aiko dai ko Rabin a waya bai kara ba saijin horn din motar shi tayi ya dawo, washe gari kuwa kin tafiya aikin yayi, ganin dai da gaske yakeyi, yasa itama ta ɓata rai ta daina kula shi ta fita sabgarshi, ta daina kwana tare dashi, kwana biyu suka kwashe a haka gaba dayan su sunji jiki, ba shiri yace mata yaji ya yarda zai koma aiki, amma sai inzasu dinga yin waya duk bayan awa ɗaya, ba yacce ta iya haka ta amice, amma da sharidin duk kira ɗaya bazai wuce 5 minutes ba, shima haka ya amince, da haka ta samu ya koma office.
Har zuwa wannan lokacin babu abinda ya shiga tsananin su, ta bangaren auratayya saidai zuwa yanzu an samu ci gaba sosai dan sukan sha romance dinsu na fitar hankali, saidai fa iyakar ta nan, ita kanta tana mamakin yadda akayi ya kasa nemanta har yanzu tun abin bai damunta har ya fara dan damunta, har take tunanin anya ma sonda yace yana mata da gaskene kuwa, dan indai akwai soyayyan dole zaiso su zama Abu guda ai, Allah sarki Asmah bata San Aslam yama fita bukatar hakan ba, saidai yana nan akan bakanshi, na cewa saita nemi hakan da kanta tukunna.
Gaba daya Aslam ya manta da wata zee a babin rayuwarsa, Asmah ce kawai a gabanshi a halin yanzu.
Yau gaba daya familin sun tashi da tsantsar farin cike, ba komai bane kuwa face haihuwan da akayi musu gagarumi, yayansu Rabi'a ce ta haihu maman hanifa, ta samu É—a namiji wannan karon, da safiyar yau mami ta kira su dukkansu daya bayan daya tana gaya musu, duk wacce ta kira ,sai taji ta daka tsalle tana murna tare da tambayarta dama tana da ciki ne, tasan duk abinda sukema wannan tsallen murnan koba komai zasu zo gida zasu haÉ—u da juna, to ai dole, wata biyar fa ba kwana biyar ba, duk da suna waya da juna, da kuma iyayen nasu......
Oum Ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
FisabilillahðŸ™.
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.