Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 88 of 89
Page 131
Mutuwar Dad ya girgiza zukatan mutane da dama, duk wanda ya tuna abin da ya faru kafin awa ashirin da hudu da suka shude, sai ya kara tsarkake lamarin ubangiji ya kuma kara tabbatar wa lallai rai ba'a bakin komai yake ba, lokacin da labarin rasuwar Dad ya riski zee kusan zaucewa tayi, take ta fisge daga rikon da Aslam ya mata ta nufi ɗakin da gawar Dad kwance da mahaukacin gudu, tana yin arba da gawar Dad take ta yanke jiki ta faɗi sumammiya. kwanan keso Dad yayi saboda da daddare ya cika. Washe gari Karfe tara Mom ta iso a birkice , bata yarda cewa Dad ya rasu ba saida tayi arba da shi kwance baya motsi lulluɓe da farin alawayyo, take ta ƙara birkicewa ta shiga zunduma ihu tana kururuwa da birgima kamar wata arniya maimakon ta mishi addu'a, rarrashin duniya an mata taƙi ta haƙura har aka gaji aka yi kyale ta, masu zagi da alawadai nayi masu tausayi nayi. Karfe goma daidai aka kai Dad makwancin shi na gaskiya, Aslam da duk wani makusancin shi sun halarci jana'izan Dad, tare dashi aka cigaba da karɓan gaisuwa a gidan alhaji Abdur-rahman. Har aka kai Dad aka watse zee bata cikin hayyacin ta, dan tunda ta sume aka kwashe ta aka sake bata gado a asibitin, likitoci suka duƙufa a kanta har aka samu ta farfaɗo, koda ta farfaɗo zabure zabure ta shiga yi tana ihu ce ihu ce lamarin kamar da bugun aljanu ganin haka yasa likita ya zunduma mata alluran barci mai karfin gaske, sai da Dad ya kwana ya wuni a kushewa sannan ta farko,cikin hukuncin ubangiji ta farka cikin hayyacinta sai dai kuma ruwan hawaye ya kasa ƙafewa a idanun ta, a ranar Dr ya bata sallama direct Aslam ya wuce da ita gidan Alhaji Abdur-rahman aka cigaba da zaman makoki tare da ita, duk yan gidan su Aslam sunje sunyi gaisuwa tun daga kan su mummy har su batool da mazajen su, Aslam da Asmah kam kullum nan suke wuni shi yana falon Alhaji Abdur-rahman ana karbar gaisuwa dashi ita kuma tana tare da zee tana kwantar mata da hankali, har zuwa ranar da akayi addu'an fidda'u na kwana uku. Sai da zee tayi kwana bakwai sannan Aslam ya dauko ta, har zuwa lokacin mutuwar Dad nanan daram a ranta, sai dai tayi amfani da shawarar da Asmah ke bata a kulkum ta daina yi mai kuka sai dai in abin ya ciyo ta tayi ta hawaye tana mai addu'a domin tasan shine abin da yafi buƙata a halin yanzu, part guda aka ware wa Mom a gidan Alhaji Abdur-rahman a nan take zaman takaban ta, Allah sarki Dad tasa ta ƙare wasu har sun manta dashi sai wa'inda ya zame wa dole kamar dai zee da Mom da Alhaji Abdur-rahman.
Bayan wata daya da rasuwan Dad, zaman lafiya tsakanin Asmah da zee sai abin da ya ƙaru, zuwa lokacin zee ta koma asalin zee ɗin ta, tayi laushi ta kara miƙa wuya ga lamarin ubangiji, ta dau hakuri da dangana akan rashin mahaifin ta, idan ta tuna shi sai dai kawai ta mishi addu'a, Aslam ma ya dena yi mata wasu abubuwan da yake mata zuwa yanzu dan ba karamin tausayi take bashi ba , musamman idan ya tuna da wasiyyan da mahaifin ta ya bashi da kuma amanar ta daya damƙa a hannnun shi a lakacin yana kan gargarar barin duniya. A bangaren Asmah yau ta wayi gari cikin wani irin yanayi mara daɗi tun cikin dare ta ke jin cikin ta na wani motsi kamar akwai abu mai rai a ciki,dama takanji haka lokaci lokaci cikin kwanakin nan tana sharewa amma na yau sai yayi yawa gashi Aslam ba'a dakin ta yake ba, tun cikin daren tayi ta kiran wayar shi amma yaki shiga, haka ta zauna ta dafe cikin ta tana ta kuka, idan taji motsin yayi yawa sai ta shiga karanta ayatulkursiyu ta tofa, ta firgita ainun da lamarin kafin safiya duk ta fice daga hayyacin ta, kwanaki da cikin ta keta kumbura taje asibiti taga likita, Dr Aysha ta mata duk wani tambayoyi akan alamomin ciki tace bata jin ko daya, kuma duk watan duniya al'ada takeyi, duk wani test daya kamata tayi, tayi harda su scanning babu komai, kwantar mata da hankali Dr tayi tace ba komai kawai tumbi bi ne, ta kiyaye cin abubuwa masu maiko da kitse kuma ta ringa motsa jiki zai baje insha Allah, koda taji haka sai ta tattara lamarin ta watsar kawai tunda dai ita ba ciwo yake mata ba, kuma ma ba wani shegen girma yayi ba itace kawai take ganin abinta sai ko Aslam shi da yake mijin ta , amma idan ba mutum kallon kurulla ya mata ba bazai ga komai ba, shine kuma cikin wannan week ɗin ta farajin motsi motsi a cikin nata, tana dai daurewa tana basarwa don ko Aslam bata fadawa ba, sai dai tayi ta addu'a tana rokon Allah koma menene ya yaye mata, har aka kira sallan assalatu idanun ta biyu bata rintsa ba, da'ker ta lallaɓa tayi sallah, tana idarwa ta farajin kamar ana yaki a cikin har in ta taba tanajin motsin a hannun ta, wayar ta ta dauka ta sake gwada kiran Aslam still bai shiga ganin haka yasa ta juya akalar kiran ta zuwa numbar mummy dama abin da ya hana kiran ta tun jiya dare ne dan karta ɗaga mata hankali, mummy nakan dardumu da asuba tana lazumi taji wayar ta na ringing kamar ta share haka kawai taji zuciyar ta na azalzalan ta akan ko baza ta dauka ba ta duba, ganin sunan Asmah na yawo a saman screen din wayar yasa taji gaban ta ya fadi, a fili ta furta "Asma'u da wannan farar safiyar Allah dai yasa lafiya." Ɗaga kiran tayi ta kara a kunne tare da yin sallama, cikin shehsheka taji muryar Asmah na amsa mata sallama, cikin dan tashin hankali jin Asmah kamar kuka taje tace "subhanallahi! Asma'u mekefaruwa, meya sameki waya taɓa ki?" Dan ita duk a tunanin ta cikin Aslam da zee ne wani ya saka ta kuka a Cikin kuka take ba Mummy labarin abin da ta kwana ji a cikin ta yau, mummy karan kanta abin yadan tsorata ta, wani tunanin ya faɗo mata a rai da sauri ta kauda shi tare da yin istigfari a zuciya, cikin sanyin jiki tace "Ina Aslam ɗin yake to?" Tace "yana ɗakin anty zee yau a can yake kuma tun cikin dare nake ta ta kiran shi wayar shi yaki shiga." Katse kiran mummy tayi tare da cewa "Ina zuwa." Lambar Aslam ta shiga kira itama cikin rashin sa'a yaki shiga, ganin zai bata mata lokaci yasa ta shiga shirya wa dan tafiya gidan Aslam taje taga halin da marainiyar Allah take ciki. A waya ta sanar ma daddy abin dake faruwa shi kanshi lamarin ya daure mishi kai, baiyi kasa a gwuiwa ba yace ta shirya ya kaita, minti 30 ya dauke su zuwa gidan Aslam, har zuwa lokacin Aslam na part ɗin zee dan koda ya dawo masallaci can ya koma da nufin yayi shiri ya sallame ta gaba ɗaya sai ya koma part ɗin Asmah, horn din motar su mummy da kuma ƙaran bude get da mai gadi yayi shiya janyo hankalin shi, yana tsaye gaban mirror yana shirwaya zee na gefen shi tana taimaka mai, kallon juna suka yi da mamaki fal fuskokin su, waye da wannan sanyin safiyar a gidan su, kasa hakuri yayi ya karasa bakin windo ya daga labule ya leka zaro idanu yayi lakacin da yayi arba da motar Daddy kafin ya gama mamaki yaga Mummy ta fito ta nufi part din Asmah, da sauri ya saki labuleb ya juyo ya kalli zee data ke nan tsaye tana jiran taji su waye, yace cikin dan tashin hankali "Daddy da Mummy ne fa." Cikin kaɗuwa tace " A gidan nan da sassafe? To duk yadda akayi ba lafiya." Bai tsaya jin me zata ce ba ya zira jallabiya ya fice da sauri ganin haka yasa ta rufa mishi baya. A can kuryan ɗaki Mummy ta same ta durkushe tana hawaye da sauri ta karasa ta dago ta, ganin mummy yasa ta fashe da kuka, rarrashinta Mummy ta shiga yi "yi shiru Asma'u ya isa haka, yanzu zamuje asibiti insha Allah koma mai ke ciki zasuyi scanning mu gani, asibitin Dr nasidi zamuje babban likitan mata me kuma yana da wankin ido imma jinnu ne ko sihiri zai gane." Kasancewar sanye take da hijabin da tayi sallah yasa mummy kamo hannun ta kawai suka nufi kofar fita, daidai nan Aslam ya iso da sauri zee na biye da shi, ɗaga ido mummy tayi ta musu kallo daya sai taji wani haushin su ya tirnike ta suna can suna soyayya sun bar mata yarinya ita kadai zata mutu a banza ita fa shi yasa auren mai mata bai taba birgeta ba, sama sama ta amsa gaisuwar su, ta wuce su rike da hannun Asmah dole suka matsa mata a hanya, ganin yadda ran ta ke a bace, daddy na hango su ya fito ya bude musu gidan baya, zaunar da ita tayi tare da rufe mata kofar ta zagaya ta shiga mazaunin ta nada suka dauki hanyar asibitin Dr nasidi dake kwangila, suna fita Aslam na fitowa, hankalin shi gaba daya ya tashi dafe kai yayi ya shiga karanto innalillahi wainnailaihi rajiun, ganin haka yasa zee nufar dakin ta da gudu ta dauko makullin mota bata tsaya mai bayani ba ta shiga ta tayar ganin haka yasa shima yayi sauri ya fada ta bi bayan su mummy cikin sa'a ta cim musu saboda traffic light daya tsayar da su, koda suka iso asibitin sun taradda da layi duk da likita bai karaso ba sai Karfe takwas, duk wani zirga zirgan da za'ayi na bude file da sauran su Aslam ne yayi, so yake ya tambayi meke damun Asmah amma yana Shakkar mummy ganin yadda fuskar ta ke daure, kasa jurewa yayi ya nufi ta inda yasan zai iya sanin sauki, wurin daddy, a nan yake jin mekefaruwa, aiko dai hankalin shi ba karamin ta shiga yi ba haryaso yafi Asma'un shiga rudu, takwas daidai Dr nasidi ya iso, mutane da yawa ke gabansu amma kasancewar akwai sanayya a tsananin su, ɗan wani tsohon abokin daddy ne yasa aka musu wuru wuru wanda ba'a rabuwa dashi a Nigeria suka shiga, yana gama jin bayanin ta daga bakin Mummy kallo daya ya mata yasan lamarin ta akwai saka hannun mutanen ta a ciki, amma bai gaya musu haka ba, scanning ya fara mata take ciki ya bayyana yaya uku rerass da ransu da lafiyan su yan wata shida har an gama halittan su, bai basu bayanin komai ba saida ya gama daidai ta komai, duk wani abin da ya kamata ya mata yayi, ya bata duk wani taimako da ya dace sai da ya tabbatar yanzu komai normal, sannan ya nemi ganin mijin ta a office din shi, jiki a sanyaye Aslam ya tafi don tunda daddy ya gaya mai mekefaruwa jikin shi yayi sanyi, musabaha sukayi da Dr nasidi shima matashi ne dan akalla zasuzo tsara da Aslam din, dan da alama ma sunsan juna, bayan Dr ya nuna mai wurin zama ya zauna, farin takarda ya mika mishi tare da cewa " Da farko dai zan fara da cewa Congratulation Mr Aslam." Ya fada yana sakin kayataccen murmushi, kamar wani gaula haka ya tsaya yana kallon shi, zaka rantse baijin yaren da Dr nasidi keyi ne,ganin bai amsa faifan ba yasa Dr sake cewa "karbi mana dan uwa." Kamar mara jini a jiki haka ya miƙa jhannu shi nya karɓa,koda ya karba bai iya budewa ba sai rike wa yayi gam kamar wanda aka ba tikikin shiga Aljannah, Dr ganin bai bude ba yasa yace ka "Bude mana." Ba musu kuwa ya warware faifan ya fara binshi da idanu, wani irin yam yam yam haka ya ringa ji yana ratsa tsakanin kanshi da zuciyar shi, tabbas ba barci yake yi ba idanun shi biyu amma kuma abinda yake gani a rubuce jikin faifan ne yasa yake gani kamar mafarki yake, bayani ne akan cikin Asmah watannin Cikin da matsalar Cikin da kuma saka hannun Dr akan tabbatar da cewa yayi duk abin da ya dace yanzu komai nomal abu daya ne babu adadin babies din wannan kuma ya bar musu su jira ranar haihuwa, yana gama karanrawa dago kai yayi yace "Dr a mafarki muke ko a ido biyu?" Dariya Dr ya kwashe dashi, indai irin wadan nan bankauran ne ya saba gamo da su iri iri amma nayau na Aslam ya bashi dariya sosai, cikin zolaya yace "ko nadan mare ka ne sai ka tabbatar" ga mamakin shi saiji yayi Aslam yace "eh Dr pls ka mareni kozan dawo cikin duniya ta." Sai kuma hawayen farin ciki shaaa wanda shi karan kanshi Aslam din baisan wanda suka zubo ba, can kuma ya mike ya kaima Dr nasidi runguma,yana zuba mishi godiya, shikam dai Dr dariya yake yi, yana kara yimai congrat, lokacin daya fito daga wurin Dr zee da mummy suna dakin da aka ba Asmah bed rest na awa uku, daddy ne kawai a wajen daga yadda ya hango Aslam yana tafe da kuzarin shi fuskar shi a washe dauke da madaukakin farin ciki ba kamar yadda ya tafi ba yasa tun kan ta karaso ya mike ya tare shi, shima ganin haka yana zuwa kawai ya fada jikin Daddy ya rungume shi gagam cikin farin ciki ya shiga cewa "Alhmdllh daddy husnah tana dauke da ciki na, Ashe ciki ne da ita daddy har na tsawon wata shida bamu sani ba." Cike da mamaki daddy yace "Ciki fa kace Aslam, wane irin ciki, kodai baka ji da kyau bane." Yace "wlh daddy naji da kyau haka Dr ya fada kuma ya bani bayanin komai a rubuce." Da sauri ya sake shi tare da mika mishi faifan da Dr ya bashi, daddy na gama karanrawa ya fuskanci gabass ya daga hannu ya shiga jerowa ubangiji kirari, mutane sai kallon su suke yi, abinka da Nigeria, suko ko a jikin su basu san ma suna yi ba, zaro waya Aslam yayi tare da cewa "daddy bari na kira umminmu na sanar mata." Hana shi daddy yayi ta hanyar kama hannunshi suka nufi dakin da su mummy ke ciki. Asmah na kwance tana maida barcin da bata samuyi jiya ba,zee na zaune a kujeran dake gabanta ta zuba tagumi yayinda mummy keta safa da marwa ta kasa zaune ta kasa tsaye jira kawai take Aslam ya dawo daga wurin Dr taji menene ke damun Asma'un ta, suna shiga ta dakata tare da juyowa da sauri ta kalli Aslam cikin yanayin damuwa tace "me Dr yace?" Bai iya amsata ba sai wani irin kyakkyawan murmushi daya ke binta dashi, daga ita har zee sororo suka tsaya suna kallon shi, daddy ne da har yanzu faifan nan ke hannu shi ya miƙa mata tare da cewa, "Dr yace nan da wata hudu amaryar ki zata iso sai ki fara shiri." Bata bi takan zancen daddy ba dan a halin yanzu bata shi take ba, tun kafin ta gama karanta bayanin dake rubuce ta zube a gurin ta shiga gabatar da shujudul-shukur, tana dagowa kuma ta rungume Aslam tana hawayen farin ciki ta shiga ce, "Alhmdllh! Alhmdllh! Alhmdllh ala kulli halin Allah kun gode maka." Aslam kam murna kan murna wai yau shine Mummy ta rungume kai da alama dai idanunta sun rufe ne bata san shita rungume ba, shi yanzu ko bindiga za'a saka mai aka, yaushe zai iya tuna when last ya kiji a jikin mahaifiyar tashi, zee ma tayi farin ciki sosai dan koda ta samu cikin ta na biyu bata yi irin farin cikin da tayi a yanzu da bayyanar cikin Asmah ba. Tun a asibitin suka shiga buge bugen waya suna gaya wa yan uwa da abokan arziki, baga Aslam ba baga mummy ba kai har daddy ba'a barshi a baya ba wannan karon, tunda Aslam da daddy suka shigo dakin ta farka, sai dai bata bude idanun ta ba,duka abin da ke faruwa a kunnen ta, hawaye ne kawai ke ziraro wa daga idanunta ba tare da kowa ya kula ba, suna can suna ta murna da buge bugen waya, kan kace kwabo kuwa tuni asibiti ya fara cika da yan uwa kwace ce musu akayi asman ta haihu, daddy tafiya yayi bayan komai ya lafa ya bar mummy idan anyi sallama Aslam ya maido ta, Dr ganin sunyi yawa adakin yasa yace su fita zuwa waje a bata dama ta huta nan da awa biyu ma zai basu sallama su tafi gida gaba daya, duk fita sukayi a dakin aka barta ta huta kamar yadda Dr ya bukata, Aslam ne bayan Dr ya tafi ya lallabo ya koma dakin ba tare da kowa ya kula da shi ba, tun dazu yake ta neman wannan daman na samu ya kebe da ita ya zama shine mutum na farko da zai fara yi mata wannan albishir din, a kujeran sake facing dinta ya zauna tare da kama hannayenta ya rike, ya tsirawa fuskar ta idanu yana kallonta, haweye da yaga yana zirarowa a hankali ta gefen fuskar ta ne ta tabbatar mai da idanun ta biyu, murmushi ya saki a hankali cikin rada yace "Bazan hanaki zubar da hawaye ba husnah ta, ki zubar da abinki nasan na farin ciki ne dan nima na zubar da nawa." A hankali ta ware idanuwan ta akan fuskar shi, tace "Ya Aslam da gaske ne, abin da nake ji kuna fada cewa wai ina dauke da juna biyu har na tsawon wata shidda, kenan nima zan haihu kamar kowacce mace." Girgiza mata kai ya shiga yi cike da karfafa gwuiwa yace "kwarai husnah kina dauke da ciki Dr ya tabbatar mana da haka, insha Allahu very soon zaki haihu ki zama uwa kamar ko wacce mace." Mikewa tayi zaune ta fada jikin shi ta rungume shi ta fashe da kuka tare da cewa "Ahmdllh alakulli halin Allah mun gode maka, wlh zuciya har yanzu ta Gaza daukar lamarin da sauki ji nake kamar zata fashe tsabar farin ciki." Murmushi yayi yace "Haka Allah yake lamarin sa, mahakurci dama ance shine nawadaci wata rana." Kamar yadda Dr yayi alkawari awa biyu kawai suka kara ya basu sallama tare da bata magungunan da zata ta amfani dashi na nasara dana musulunci, suka dunguma zuwa gida,ranar Asmah ta kara tabbatar lallai ita yar gata ce, sai tururuwan zuwa gaishe ta akeyi ana taya ta murna, tare da al'ajabin yadda lamarin ubangiji ya kasancewa, wadan da ke nisa kuwa sai kiran waya akeyi har daga dangin mahaifanta itama. Kamar jira cikin yake yi a gano shi, ko sati ba'a rufe ba ta kama wani irin laulayi mai zafin gaske, duk abinda ya kamata ace tayi su tun ciki na karamin batayi ba sai yanzu, take kuma cikin ya fara wani irin girma yana fitowa fili da kadan da kadan kafin ta rufe wata daya da bayyanar shi ya fito rass ya zama wani tukeke kamar dan wata tara ba bakwai ba, ga laulayi daya sakata a gaba ba dama ta ci abinci sai amai ba dama ta shaki abin da bai mata ba sai amai , tuni ta koma abin tausayi duk wanda ya ganta sai yaji kamar ya zubar mata da hawaye,da kanta tace ta barma zee kwanan ta sai ta haihu, kafin wata na takwas girman cikin ya fara basu tsoro,kuma duk bayan sati biyu Duke zuwa asibitin Dr nasidi yace musu ba komai normal ne karsu damu, wannan suke samun relief, tana shiga watan haihuwa mummy tace ya tattarota ya dawo da ita gaban ta dan ita tsoro take ji,kar nakuda ya taso mata gida babu wani babba daga ita sai zee kuma dukansu bawai sun san kan abin sosai bane, shima bai musa ba haka nan ya kaita, aka koma aka zura sa sarautar Allah idanu kowa ya dukufa da addu'a ba dare ba rana, Aslam har masallatai da makarantun islamiyya yake bi yana bada saraka akan lamarin, Asmah kam tana jin jiki ba kadan ba ko tashi bata iyawa ita kadai cikin rinjayanta yakeyi sosai, ta dena zuwa awo sai shi Dr ya biyo ta gida ya duba ta, yana kuma kara kwantar masu da hankalin akan cewa komai na tafiya yadda ya kamata su dai kawai su dage da addu'a, har ta fita wata na tara shiru haihuwa zaizo bai zoba tun suna saka rai yau gobe jibi amma shiru kake ji wai malam yaci shirya yasha ruwa, mummy kam tuni ta rufe fita ko ina, Aslam ma kullum a gidan yake wuni kwana ne kawai bai taba yi ba haka zai saka ta a gaba yana taimaka mata suyi ta zagaye gidan suna exercise. Ranar da cikin ya shifa wata na goma sha daya ta wayi gari garau ranar dan har wani karfi takeji na musamman ba kamar kullum ba, dan ranar har mikewa da kanta takeyi kuma tayi exercise sosai da kanta ranar ba tare da ta jira Aslam ba, koda ta gama exercise din ta a falo ta samu mummy, sannu Mummy ta mata har tana tsokanar ta da cewa in ta haihu sai ta Zane babyn dan ya wahalar mata da ƴarta ya shige cike ya nemi guri ya kwanta to dai a kwai ranar ƙin dillanci, tana murmushi tace "mummy bari na watsa ruwa na dawo." Koda ta shiga dakin da aka ware mata a ƙasa tube dogon rigar ta na robaroba tayi ta daura zanin mummy babba ta shiga toilet, ita karan kanta tana mamakin karfin da lafiyar da take ji yau a jikin ta wanda rabon da taji irin shi tun kafin baiyanar cikin ta, tsugunawa tayi da niyyar yin fitsari, ji tayi marar ta yadan daure kasa mikewa tayi daga tsugunan da tayi, cikin abin da baifi minti biyu ba taji wani irin nishi mai mugun karfi ya taso mata daga tsakiyar bayan ta, kafin tayi wani yinkuro sai ji tayi wani abu na kokarin rasto kasan ta ya fito duk da bata san ko menene ba ta tsorata ainun kwala kiran sunan mummy tayi da mugun karfi, mummy dake falo bata kai ga tashi ba a gigice ta mike ta nufin dakin da Asmah ta shiga dan yin wanka ko kafin ta karasa toilet din har baby daya ya fado, da sauri mummy ta ta karasa ta tallabo ta tana fadin "subhanallahi." Ina! Asmah bata san inda kanta yake ba kafin ta kai ga kara cewa a wani abu wani babyn ya kuma fadowa, bata gama mamaki dayan ma ya fito fit tare da mabiya a lokaci guda.....
ba editing ayi hakuri
Oum Ummeetarh
07041130088
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasaukar da wannan book ɗin ga duk wacce ta rasa hahaifiya Allah kajiƙan iyayen nu.}
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.