Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 44 of 89
Page 79 & 80
Wani uban tsalle zee ta daka, nan take sai gata a bakin kofar toilet, kamar ba ita bace kwance shame shame ba lafiya, da kallon mamaki duk suka bita, Dad yace"meye haka daughter ki tsaya ya miki allura mana, ki rabu da wanna cikin da ke wahalar min dake" girgiza kai tayi tace"no Dad bana so kar a zubar inason abuna, zan haifeshi inason cikina" sanƙare wa Dad yayi yama kasa furta ko kalma ɗaya tsabagen mamakin, yace "daughter pls kar muyi haka dake, ki taimakeni a cire cikin nan kinfi kowa sanin yadda na tsani mahaifin cikin nan , bazan iya jurar haɗa zuri'a dashi ba," maƙe kafaɗa tayi kamar wata karamar yarinya yar two years, mom Ce ta kara da cewa"haba daughter kizo mana kinga munbar Dr a tsaye fa " still kin zuwa tayi haka suka shiga rarrashinta da tsoratar da ita akan maganar haihuwa da irin azabar da zata sha, amma ta.musu ƙememe, ta gwammace ta sha ko wacce irin azaba Ce indai baza ta mutu ba akan ta sha azabar rabuwa da Aslam, tasan idan Allah ya taimaketa ko ta dalilin wannan cikin na jikinta dole wata rana zata sake haɗuwa da Aslam ɗinta.
Dr kam ganin sunata lallshinta ta ki yarda , ya ajiye sirinjin ya zare safar dake hannun shi, ya shiga haÉ—a kayan shi don yana da gurin zuwa da yawa.
~9ja~
Yau Aslam ya cika kwana uku da farkawa, jiki alhamdulillahi yana samun sauki sosai, dan zuwa yanzu yakan mike tsaye da kanshi ya shiga toilet, yana samun kulawa sosai gurin likitoci da kuma yan uwanshi,.
A gida kuwa shirye shiryen biki ake tayi ba kama hannun yaro , tuni baƙi sun fara sauka daga garuruwa mabanbanta, ranar asabar da karfe goma ne za'ayi daurin aure a babban masallacin juma'a dake minna.
Gayyata kam ko ta ina yinsa ake gaba É—aya gari ya dauka da maganar wannan daurin aure na amare biyar ya gama baibaye garin minna da kewaye , hatta gidajen radio maganar da suke yi kenan a yan kwanakin na, haka gidan TV. NTA minna, duk wata kafar sada zumunta , saida maganar bikin nan ya leka,.
Ba wani program za'ayi sosai ba, saboda matsalar rashin lafiyan Aslam badan haka kam , program din da suka shirya yi yakai bakwai, yanzu kam ummi ta shirya mother's day , sai walima, sai kumbo, sai kuma kidan kwarya da za'ayi ranar yinin biki.
Amir kam baiji dadi ba da alhaji bana yace baza ayi dinner ba , sai cizon yasta yakeyi, dan dinner nan ba karamin shiri ya mishi ba, rashin kunyar daya tanada buhu buhu zaiyi a wurin dinner nan yawa ne dasu, dan duk cikin angwayen Amir ya fisu rawan kafa, hatta pre wedding pictures ba Wanda sukayi, sai shi baban rawan kai, har asibiti yaje kamar abin arziki, ya samu Aslam ya wanke tass, wai ciwon son shi bai tashi tashi ba saida ya bari bikin shi ya zo ya gama tsara bikin shi da irin rawar da zai sha a wurin dinner, gashi yanzu ya rusa mai shiri.
Dariya Aslam ya shiga yi mai dan yafi kowa sanin yanda Amir yaci burin yin abubuwa sosai a bikin shi, suna haka Dr bash ya shigo ɗakin, haduwa sukayi suna tama Aslam tsiya, harda tuna mai lokacin da yake cewa su daina neman ƙana nan yara zasu jamai raini a wajen ƙannen shi, sai gashi shi saboda soyyayar ƙaramar yarinya ya kwanta ciwo harda cewa shiya sadaukar da rayuwa husnah Ce ajalin shi, nan Amir ya tashi yana kwada ma Dr bash abinda ya faruwa ranar da su Alhaji baba sukazo yana kwaikwayan muryan Aslam, dayake bash din baya wurin, aiko dai bashir yasha dariya harda rike ciki,.
Amare sai shan gyara sukeyi ta ko'ina, idan kaga daya daga cikin su idan ba kamata farin Sani ba bazaka ganeta ba , sun daina fita ko compound din gida saida kwakkwaran dalili, batool kam har yanzu bata saduda ba kullum akazo yi musu wani abin da kuka take amincewa, wani ma saidai a kyale ta idan ta tubure.
A bangaren Alhaji baba kuwa ya Riga ya gama magana da iyayen yarinyar da ya zabar ma Aslam a mastayin zabin shi ta biyu a gare shi, kuma alhamdulillahi sun bayar, da hannun bibbiyu, lokaci kawai ake jira,.
Yau ta kama laraba kuma yaune mother's 's day da za'a gudanar a nan fillin gidan karfe hudu ne zuwa magrib, tunda sassafe yayata ta kaina anti bebi mai design da ummi tayi booking dinta tun ana saura sati uku biki ta sauka a gidan, ita da mukarraban ta , wato yaran aikinta, nan ta shiga zanawa amaren design ma gani na fada, lokacin da tazo yiwa batool, batool nata botsare botsare, ita bata so ganin haka anti bebi ta shiga hada kayanta , to dayake kunsan halin mutuniyar tawa badai saurin fushi ba , saida ummi ta jata gefe ta gaya mata matsalar batool d'in, sannan ta yadda ta lallabata suka gama, suna gamawa saiga Khadijah, wai itama anti bebi zata mata batason na yaran aikinta, aiko dai sisina tace batayi, ita amare kadai akace zata ma design, dayake itama yayan nawa kaifi daya ce inda kukasan Alhaji baba ya yayeta, saida aka dinga saka baki sannan ta dan zizara mata kadan baikai na amaren yawa ba, amma shima ya tsaru ba laifi, wata hajiya ce cikin kawayen mummy tace itama na anti bebi take so, tattara kayan ta tayi ko amsa bata ba hajiyar ba, ummi ne tace "anti bebi ki mata mana ko kadan ne" ta dago rannan a hade kamar zatayi kuka tace "gsky ummi baza ta samu ba, baban mami karfe uku yace na dawo idan na wuce lokacin yace bazai kara barina zuwa design gidan mutane ba, ga Rukayya nan ta iya sosai itama, ta mata,.
Yaran aikinta Rukayya da yaya sukuma suka shiga yiwa sauran mutanen gidan , da bakin da kenan da duk Wanda ke bukata, kasancewar suna da sauri karfe uku sun gama ma kowa, nan aka shiga wanka domin shirin zuwa wajen mother's day, haka dai anti bebi ta bar gidan nan ba tare da tama hajiyan nan design ba saidai sunyi canjin lambar waya saboda wata rana.😅
Tun azahar masu decoration suka fara aikinsu kafin la'asar guri yayi shar ba mai cewa compound din gidan Alhaji baba ne,.
Karfe uku da rabi masu makeup har mutum biyu suka diro gidan suka shiga shirya amare,
Karfe biyar gida ya cika ya timbatsa da manyan hajiyoyi kawayen su ummi Dana mummy da mami, da yake ranar ta uwayen amare ne, aiko sun amsa gayyata ba karya.
Ummi da mummy da mami anko suka sha cikin wani uban sun lace fari kar, mai tsadar gaske Wanda a kalla kudin shi yakai rabin million, banda awarware da yankunnaye da abun wuyan gold da kowaccen su ta zuba wuya da hannu, masha Allah su ummi sun sha kyau iya kyau , kana zuwa gurin ba sai ka tambaya ba zaka gane asalin uwayen amare,.
Lokacin da amare suka fito tsit wurin yayi , wasu kuwa miƙewa tsaye sukayi , zabar kiɗima , sunga haduwa iya haduwa,
Can rumfar dake kusa da na amare na hango yan dama ta biyu fan's , kowaccen su ta kure wanka , ta sako na kasan akwati, an hakince akan kujera ana daddana waya,wasun su kuma na fira kasakasa, suwaibaaliyu Ce ta kalli anty naimcy dake gefenta hakimce tace "yaudai karya zai kare zamuyi ido hudu da Asman data rikirkita mana tunanin Aslam din mu" bata kai aya ba, amare suka fito, kakus Hadiza jafar dake zaune gaba gaba, Sai kallon su mummy takeyi tana jero masha a zuciya, ta fara ganin su zabura yayi ta mike dafe da girji, tana zare ido, ta gidan dan darmay kuwa suman zaune tayi, nikam ina zaune kusa da kawata Fulani gal, muna sirri kasa kasa, dan bamuson kowa yaji mu, Kiy kura dake zaune kusa dani ganin ban ma San wainar da ake toyawa ba yasa ta kai min tsunguli a gefen fuska, zafin tsungulin ya ratsani na dago da niyyar kai mata dundu, dan nidai gaskiya ban bari ta kwana, ganin inda take nuna min yasa tuni zafin tsungulin ya gudu, kawata ma ganin na sake baki da hanci ina kallo yasa itama ta daga kai ta kai idonta inda nake kallo, Oum habeeba wayar dake hannunta tana dannawa ne ya subuce ya fadi ba tare da ta Sani ba, Allah ya somu bai fashe ba, daba na karantawa dama ta biyu yau, Fateema kam wutan kanta ne ya dauke dif, zainab kam da yake ta maka bakin glass irin no respect din nan yasa ban gane halin da take ciki ba, daughter Mr salis kam baki da hanci da kunne duka ta bude tana kallon su dashi, fatima bala gazara , salima abdullahi maman lubna, duk suna zaune, suna ba ido abinci,kai wlh dama ta biyu fan's muna da yawa in nace zanta lissafo sunan ku da daydaya sai mu cinye page dinnan bamu gama ba , masu comment wacce bata ji sunan ta ba ma hade a next page,
Sanye suke cikin wani dankareren lace babban nasu mummy, saidai su nasu black color ne kasancewar su farare sol ga kuma gyaran da fatar su ta dauka, karkuso kuga yanda ya musu kyau , an nada musu goggoro ash colour, takalman kafar su masu tsini suma ash hannayen suna rike da wani dan gudul din pos shima ash ,wuya da hannayensu kuwa gold ne kirar dubai, fuskar su kuwa tasha heavy makeup ko wacce na zuba kamshi, kyau kam kowacce ka kalla, sai kayi tunanin tafi su kyau duka idan kuma ka kalli wata itama haka,.
Wurin da aka tanada dan zaman amare , suka zauna cake dankarere mai hawa biyar na daga gefe, haka aka shiga gudanar da program, cikin wayewar kai , mummy ummi da mami kowacce ta fito ta yi godiya ga Allah ta kum nuna irin farin cikin da take ciki ayau haka wasu daga cikin dangi, dakuma wasu kawayen su mummy,.
Anci mai kyau ansha mai kyau, yan dama ta biyu fan's ranar kakansu ta yanke saka, sai cin kaji ake ana kari, kakus kam tunda ta danki dangwalelen kaza, ta tasa a gaba bata karama kowa magana ba, har aka tashi, garin da tace zata bari ma tuni ta manta da batun,.
Gab da magriba aka tashi a wajen taron,.
Washe garin ma haka akasha kumbo shima a gida akayi, gida ya cika ya tumbaza har fiye da jiya , dan yan dama ta biyu fan's, harda wadanda basu zo jiya ba yau sunzo dan sunce ba'za a barsu a baya ba, kwanda suje su kashe kwarkwatan idanu,.
Ranar juma'a kuma akayi walima, a labour kutigi, karfe hudu zuwa shidda, manyan malamai ne mata, masu ji da ilimin addini Dana zamanj suka bada lecture a wurin waliman nan, gaba daya jikin amaren nan yayi sanyi kalau karma batool taji labari, Asmah da zahra kam harda kukan su shabe shabe da majina,.
Karfe shidda daidai aka tashi, can na hango yan dama ta biyu fan's ana shararowa da kafa zuwa bakin titi, dan dai labour kutigi opposite government hause yake ba kowani lokaci ake samun keke napep ba gashi daga gurin zuwa titi da dan nisa ko rabi basuyi ba aka kira magariba , tuni kafa ya dauke a hanyan, su kakus ido ya raina fata, gashi kowacce tayi lodin sabeniyasa kaya guda dan wasu ma irinsu ta gidan dan darmay so bibbiyu suka karba, ana cikin haka Allah ya turo wani mai hilux,nan muka shiga dagamai hannu , yana tsayawa mukaga Ashe bello ne, haka dai ya taimake mu ya lodo mu a bayan hilux din nan zuwa babban titi, daga nan wasun su masauki suka nufa dan kafa yai tsami,nidai da yake inason na dauko mana rahotan , sa kalle da za'ayi bayan magrib , dole na tari napep zuwa gidan alhaji baba nida Kiy kura da Fateema da Oum habeeba,.
Ana idar da sallah aka shiga sa lalle, hajiya mama da kanta ta saka amare a lallai, zo kuga kuka gun yan matan mummy, inda kukasan an riga an daura aure ne, abin tausayi suna tunanin rabuwa da juna , to ai dole tun yarinta tare ake kwana ake tashi, mummy kam kasa tsayawa tayi a wurin a hankali ta silale É—akin ta , taje ta sha kukanta na kewan rabuwa da yan matan ta, ummi kan dariya ta dinga musu tana tsokanar su kamar yadda ta saba karshe ma wayarta ta dauka ta shiga ri musu video,.
WASHE GARI
Akace rana bata karya, saidai uwar diya taji kunya, tunda sassafe, gida ya dauki harama baki ta gabas ta yamma ta kudu da arewa, kafin karfe tara gida ya cika makil, da jama'a na masaka tsinke,.
Karfe goma daidai babban masallacin juma'an minna ya cika makil da jama'a, idan kaga mutane zaka dauka sallar idi akeyi motoci kuwa tun daga complex har mobile parking ne , yan sanda ke faman kula da gyara fakin motoci, bosso road ranar kasheta akayi saboda cinkoson jama'a indai zakabi hanyar saidai ka zagaya ta bay pass,. Saida duk wani mai muhimmanci ya hallara sarakuna daga garuruwa mabanbanta, haka manyan malamai daga fadin duniya , ga governor da sauran kusoshin gwamnati,.
Haka aka shiga gabatar da daurin aure bi da bi, har saida aka daura na amare biyar rerasss,akan sadaki mafi karanci da albarka, masha Allah angwaye idan ka gansu bakin nan har kunne, karma amir yaji labari sai daukan selfi yakeyi da friend dinsa, Alhamdulillahi aure ya dauru saidai muyi fatan Allah ya bada zaman lafiya,.
Har zuwa wannan lokacin Aslam na kwance a gadon asibiti, amma har nan labari ya iske shi na daurin auren, shidai har zuciyar baya jin zai so wannan zabin na alhaji baba kamar yadda yake son Asman shi amma zai yi iya kokari shi ya danne son da yake ma Asmah tunda yanzu ta zama mallakin wanin shi zaiyi hakuri da koma wacece aka daura mai aure da ita, kawai don dai yama iyayen shi biyayya, zai ta rokon Allah ya saka mishi son ta a zuciyar shi ya kuma cire mishi son Asmah, tunda ba rabon shi bace, yayi imani ya dauki kaddara zaici gaba da jinyar zuciyar shi , har ta warke daga wannan mummunan ciwo da take dauke dashi na son maso wani , amma a zuciyar shi ya kudiri aniyar ana sallamar shi a asibiti zaibar Nigeria dan bazai iya tsayawa yana ji yana gani wani ya angwance da Asmah bashi ba, bazai iya jura ba, ƙasa mai tsarki zai tafi, yaje yata rokon Allah a gaban dakinshi mai tsarki har sai yaji sanyi a zuciyar shi zai dawo 9ja,.
Acan gida kam yinin biki ake yi cikin girma da arziki ko ina manyan mata ne ta ko'ina sai watayawa akeyi, karfe uku daidai jumai mai kidan kwarya ta dasa a tsakar gida, nan kuma aka shiga caskalewa , dama ta biyu fan's kam an samu abinda ake so tunda suka shiga fili kallo ya kama Kansu, nan suka shiga kwangwajewa, jama'a sai yan gulmace gulmace ake yi kasa kasa , su waye wadannan kuma da suka zake haka sunata rawa, basu suka bar tsakiyar fili ba saida jumai ta nade kayanta,.
Duk wannan shagalin da akeyi Asmah nacen kwance kudundune cikin bargo wani zazzafan zazzabi ne ya lullubeta, tun bayan da aka gama daurin aure alhaji Mallam ya kirata ya damka mata sadakin ta a hannu ya mata nasiha mai ratsa jiki, da kuka shabe shabe ta baro falon Alhaji baba tunda ta fada kan gadonta ta kwanta, zazzafan zazzabi ya lullubeta, gashi Neman duniya tama Khadijah a cikin gidan bata ba labarinta , ko mai kama da ita bata gani ba duk Wanda ta tambaya saidai ace mata bari a kira mata ita, saidai tashi shiru a haka har bayan magrib inda motocin daukar amare suka layu a kofar gidan alhaji baba,..............
DAGA YAU INSHA ALLAH DA RANA KO DA YAMMA ZAN DINGA POSTING🙠dan allah ruwan comment dan mu samu mu karkare da wuri mu shiga sabon buk
(MIJIN NOVEL, zan aura) daga jin sunan kunsan zai nishaÉ—an tar daku fiye da dama ta biyu kudai kawai ku bani haÉ—in kai comment dinku kawai nake bukata, ba sai yan dama ta biyu fans kaÉ—ai ba.
NAGODE SOSAI MASU MIN COMMENT HAR KULLUM DAKU KADAI NAKE TAFIYATAðŸ˜
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
FisabillilahðŸ™
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wanna book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.