Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 7 of 89

Page 11&12

Aiko ya gwadatan Dan wani iri kwance kwance gabanta yayi ya fadi, nan da nan hankalinta ya tashi ta birkice, mom dinta dake zaune kusa da ita tanajin duk abinda suke fad'a ta jawota jikinta ta rungumeta ganin tanason ta fashe da kuka, ita kuma mom bata son tayi kuka a gabanshi akan wanna maganan,
Don acewarta idan yaga ta damu dashi haka sosai zai wulaqantata ne idan sunyi aure, bazai dinga kulawa da baccin ranta ba, don yana ganin tana bala'in sonshi komai zai mata bazata damu ba, wai ta dena nuna mai mahaicinso 'karya raina ta, hannu mom ta saka ta kashe wayar,
Aslam jin shiru yayi yawa yasa ya cire wayar a kunnen shi ya duba gani yayi tayi ending call din , murmushi yayi don ya riga yasan hakan zata faru, yamaga qoqarinta da bata yi mai wani hauka ba, d'on yasan yanda takeson shi idan taji yayi aure ba qaramin tashin hankali zata shiga ba,
Saidai abinda aslam bai saniba ranar da zee ta farajin labarin yayi aure saida tayi dan qaramin hauka, mom dinta ne ta dinga lallashinta sannan ita ta hanata nuna mishi ta damu da auren da yayi, ita ta hanata ta kirashi tun lokacin ta zuba mishi hauka, ta gaya mata ta nuna irin abin bai dameta ba, wai don idan ya gane ta na kishinsa ya samu lagonta kenan, ba a nunama namiji mugun so don ba yan goyo bane,

Zaune take tayi irin zaman nan na tahiya kanta a kasa yayida gabanta kadan wani farin kyakkyawan tsohone hannunsa goye a bayansa sai safa da marwa yakeyi fuskan nan nashi a murtike babu alamar fara'a kai da gani kasan ransa a mugun bace yake,
Sallama daddy da mummy sukayi amsa musu alhaji baba yayi neman guri sukayi daga gefen kafet din dake shimfid'e a tsakiyar parlon suka zauna,
Asmah ce ta gaishe su cikin girmamawa sai lokacin dukkan su suka kula da itace a wurin amsa mata sukayi, zuciyoyinsu cike mamakin ganinta da kuma tarin fargaba, basu taba tsammanin ganin ta a nan a dai dai wannan lokaciba, don koda su zahra suka shigo basu gayawa mummy komai ba, koda ta tambayesu lafiya suka dawo ba sunce zasu kwana bane, ce mata sukayi lafiya qlau sudai sun dawo ne sun fasa kwanan ,
Ita kuma ganin yanayin su wani iri sai ta alaqanta hakan da qila yayansu ne ya korosu,

Sallamar da aka kumayi ne ya katsewa mummy tunaninta, mamice tare da abbah sai kuma ummi dake bayansu, suma guri suka samu suka zauna suna mamakin ganin asmah ,
Dukansu hankalinsu suka mayar kan mahaifin nasu dake ta faman safa da marwa,
Shima ganin duk yayan nashi sun hallara yasa ya juwo ya fuskancesu ransa a matuqar bace ya fara magana "Aisha" ya kira sunan mummy ,
Dago kai mummy tayi tana amsa masa da "na'am baba
Yace" yace inason a matsayinki na mahaifiyar wannan yaro aslam ki kirashi ki bashi umarni nan da minti goma ko a ina yake yazo ina buqatar ganin shi a falon nan"
Nan take gaban mummy ya yake ya fad'i kar aje wani mugun abu aslam yayi fa, don ita hankalinta bai kwanta da wannan kiran gaggawan da alhaji baba ya musuba duk da batasan kiran menene ba, hankalinta bai qara tashiba saida taga asmah a wajen yanzu kuma gashi ance ta kira aslam, haka dai ta daga wayarta don kiran aslam din ,
Yayinda alhaji baba yaci gaba da magana cikin dan danne yanayin da yake ciki na bacin rai ya kira sunan ya yan nashi guda uku da ya mallaka a duniya yace" abdullahi" "na'am baba daddy ya amsa,"

Yace "dakai da qannenka Yusuf da Amina da matayenku da yayanku .....Allah ya muku albarka" har suna hada baki gurin amsa masa da amin baba.
Daidai nan kuma hjiya mama ta shigo dakin, tsohuwace mai kamala cikin shiganta na mutunci idanunta sanye da farin glass na qara karfin gani, tana dan dingisawa alamar kafa nadan matsa mata abinka da jikin tsufa, waidonma su tsufan nasu mai kyau ne angode Allah Neman guri tayi ta zauna a daya daga cikin kujerun falon ..
Magana alhaji baba yaci gaba dayi" tun kuna qanana kuka kasance masu yimin biyayya a dukkan abinda na umurceku, sannan haka kuma horas da yayanku akan bin umarnina, Baku taba saba umarninaba daku da yayan Ku....nagode nagode Allah ya saka muku da alkhairi, kuma insha allahu zaku tsinci ribar biyayya a gaba koda bayan raina ne, sannan kuma Abu na biyu da yasa na kiraku nan shine"

(Kuyi haquri dear fan's jiya banida chaji ne)

Share and comment
Fisabilillah🙏🏻
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

🇳🇬🇳🇬HAPPY INDEPENDENCE򌰼🇳🇬🇳🇬

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.