Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 77 of 89
Ci gaba mom tayi da kwantar mata da hankali da kuma tabbar mata da cewa ta kwantar da hankalinta zata koma gidan mijin ta ko yanzu ko anjima, da'ker da siÉ—in goshi mom ta samu zee tayi shiru.
Sauke ajiyar zuciya take yi a kai a kai tana sauraren maganganun mom dake ƙara kwantar mata da hankali, a haka barci ya fara fusgarta, ganin haka yasa mom kwantar da ita a gadon ta, tare da daukar little Aslam ta fice daga dakin, hankalin ta kuma gaba daya sai ya koma kan Dad wani yanayi yake ciki a halin yanzu? tasan duk inda yake a halin yanzu yana cikin tsananin bacin rai ta sani itace shaida akan irin tsanar da yama Aslam, fatan ta dai Allah yasa bai bar cikin gidan ba, ya zame mata dole tayi wani Abu akan wannan lamarin matsayin ta na mace kuma uwa, ta sani sauya ra'ayin Dad musamman akan Aslam abune mai matuƙar wahala amma ta dauki damarar ko ana ha maza ha mata, zata kafe kai da fata, sai inda karfin ta ya kare tunda har yayi hakuri ya bar zee da cikin Aslam ta haifa a gaban shi, to kuwa zai yi hakuri ya barta ta rayu da mijin ta, saidai tasan abin ne da kamar wuya.
Inda take kyautata zaton samun shi ta nufa wato É—akin shi, kamar yadda ta zatan kuwa a nan ta same shi,ran shi a bace kamar wanda aka aikowa sakon zagi, sai safa da marwa yakeyi from wall to wall na É—akin, ya kasa tsayuwa waje daya ya kai gwauro yakai mari.
Jin motsin shigowar ta yasa ya juyo ya kalle ta, tare da cewa a kausashe "Kin sani na sani wannan bukata ta daughter bazai taba yuwuwa ba idan da Wanda na tsana a duniya to Bayan wannan yaron yake, na tsane shi ina jin haushin shi na kullace shi sosai a zuciya ta , shine mutum na farko daya fara warware mini tsari na, ban taba tsara zan aurad da daughter a daidai wannan lokacin ba, amma yaron nan ya karya mini tsari ta hanyar cusa mata soyayya har ta nemi tayi fito na fito Dani akan shi, ban taba samun banbancin ra'ayi da ita ba, duk abin da na zabar mata shi take bi, duk abinda nace tayi shi take yi, duk abin da na hanata bari take yi. amma akan wannan yaron ta tirje ta dage ta kafe ta rufe idanunta ta manta da matsayina a gare ta har sai da ta saka na aika ta abinda banyi niya ba, Bayan haka wanan yaron shine mutum na farko daya fara daga hannu ya marar mini fuskar ɗiya Wanda ni mahaifinta tunda na haifeta har takai shekara ashirin da shida a gabanta ban taba koda dun gurin kanta bane, har ila yau shine mutum na farko daya fara dukan mini ɗiya, Bayan Marin da ya mata." Mom da tunda ta shigo bai bata damar cewa komai ba tayi sauri ta tari nunfashin shi da cewa "Kuma shine mutum na farko da zaka fara baiwa hakuri domin ya taimake ka ya karbi ƴarka a karo na biyu." Take idanunta Dad suka wani ƙankance jin maganar bazan da mom keyi, to maganar banza mana a ganin shi, shi take nufin zai bawa wannan yaron hakuri,nuna kanshi yayi yace "ni, kina nufin ni zan bashi hakuri, to saboda me akan me zan bashi hakuri sh.. " bata bari yakai karshe ba ta sake taran numfashin shi da cewa "saboda farin cikin tillon ƴarka, idan har da gaske kana mata irin son da kake faɗa kana mata to ka sasanta da mijinta ka kuma barta ta koma ɗakin ta taje su raini ɗansu a gaban su kamar yadda muka Raine ta a gaban mu." Ranshi yaji yana kara ɓaci, ji yake yi kamar zagin shi mom akeyi idan tace ya bari zee ta koma gidan wannan yaron, cikin masifa da hargagi yace "kinga karima fitar min daga ɗaki kafin na buɗe idanuna na rufe." Ya karkare maganar yana nuna mata hanyar fita, ganin haka yasa mom ficewa daga ɗakin salin alin, ya rakata da harara tare da cewa"maganar banza maganar wofi,Idan naki bari ta koma fa, me zaki iyi yi."
Koda mom ta fito bata koma ɗakin zee ba ɗakin ta ta koma ta lalubi bakin bed ta zauna, tasan dama hakan zai kasance amma duk da haka baza ta sare ba, zata ci gaba da lallaba har, ta samu haƙan ta ya cimma ruwa.
Koda zee ta tashi mom bata gaya mata yadda sukeyi da Dad ba itama bata tambaya ba, ta dai gama yanke shawara ta tsaida matsaya ɗaya, zata basu haƙƙin su na iyayen ta da haihuwar ta da sukayi ta bisu sauda ƙafa, idan har suka tirje to lallai zasu neme ta su rasa, ko mai tsira da amince yace kada kuyi biyayya ga abin halitta wurin sabon Allah, ita zata bi mijin ta domin shine aljannar ta.
(Allah sarki zee duk wannan abin bata San Aslam yayi nasaran auren Asmah ba fa😟)
~9JA~
Bayan wata biyar
Jiki a sanyaye Aslam ya miƙa hannu ya karbi farin fefan da Dr ke mika mishi, kallon su Dr Aysha tayi cikin tsananin tausayawa tace " Amm Mr and mrs Aslam wannan shine result din scanning ɗin da aka mata, bamu ga komai ba, kuma still babu ciki, amma dan Allah kar ku damu karku cire rai, in-sha Allah zaku samu ciki, yanzu dai zan daura ku akan magunguna kuje kuyi ta sha na wata daya ne muga yadda hali zaiyi." Tuni hawaye suka fara zarya akan dakalin fuskarta, yayinda shi kuma gaba daya fuskar shi ta dagule ta koma kalar tausayi, kwantar da kanta tayi akan ƙirjin shi ta side ɗin da take zaune, shi kuma ya rungume ta yana ɗan tapping Bayan ta a hankali, Dr Aysha ta kalle su, tayi murmushin ta mai kayatarwa, zancen gaskiya Mr and mrs Aslam suna matukar burgeta, ta Daɗe bata ga ma'aurata masu nuna ma juna tsantsar so da kauna kamar su ba, basa shakka kowa basa shayin kowa a gaban kowa suna nuna ma junan su kulawa, wani bin ma basu sanin sunyi wani abin, tana kuma matukar tausaya musu sosai akan rashin samun cikin da basu yi ba wannan ne karo na biyar da suka zo gare ta, ta lura daga matar har mijin sun kwallafa ransu akan samun haihuwa.
Ya duƙu fa gurin lallshin ta da alama ma ya manta a office din Dr suke, dan dago face dinta yayi da nufin ya lashe hawayen dake kwarara a idanunta, ganin haka yasa Dr Aysha saurin yin gyaran murya, da sauri duka suka kalle ta, Asmah ta dan dukar dakai alamar kunya yayin da shi kuma da ba ruwan shi da kunya idanunshi ker akan Dr murmushi tayi tace"kuyi hakuri masoya na katse muku hanzari ko, to nece wannan shine magungunan da zaku siya kusha na 1mnth idan Allah ya yarda sai kuga an dace" ta kare maganar tana miƙa wa Aslam farin fefan da tayi rubutun, amsa yayi yana mata godiya sannan suka fito daga office din tana tallabe a jikin shi suka fito suka nufi parking lot, mutane sai kallon su akeyi suko ko a jikin su.
Saida ya buɗe mata ta shiga ta zauna sannan shima ya dawo ya bude gefen driver ya shiga suka dauki hanya, suna tafe yana ƙara kwantar mata da hankali, duk da shima karfin hali yakeyi, idan da zai samu dama shima kukan zaiyi sai dai kasancewar shi namiji yasa ya dake yana lallashin ta, ita ko sai ruwan hawaye take zubar wa tana shehseka, sun zo dai dai kofar gida har mai gadi ya wangale get, wayar shi dake hannunta yayi ringing, ko dubawa batayi ta mika mishi, ganin Amir ne me kiran yasa ya daga, daga can bangaren Amir cikin yanayin tsantsar farin ciki yace"broh matata ta haihu, yanzun nan yanzu haka muna standard hospital ko sallaman mu ba'ayi ba." Aslam a ruɗe yace "iyeee kace ta haihu." Ai jin maganar haihuwa yasa ta tsaya da kukan shagwaban da take yi, tare da zazzaro manyan idanunta ta waje gabanta na faduwa tace"honey waye ya haihu" cikin washe baki yace"Amira ce" wani irin zabura tayi ta rungume shi tana faɗin "alhmdllh alhmdllh Allah mun gode maka." Tana cikin murnar kuma yaga tayi tsit, can kuma sai kuka.........
Kwana biyu kun juna shiru wlh nadan samu uziri ne kuyi tamin hakuri dai.
Oum Ummeetarh
07041130088💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.