Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 84 of 89

Page 127

Shi ne ya fara yin karfin halin buɗe murfin motar ya fito, ya zagayo ta gefen da take ya buɗe mata ita ma, cikin matuƙar sanyi jiki ta fito, mayar da ƙofar motar yayi ya rufe, tare da kama hannun ta suka nufi nata part ɗin.
A hankali ta saki labulen windon data dan ɗage kaɗan tana kallon su, da baya da baya ta ringa ja har ta isa bakin bed ta zauna dabass, tagumi ta rafka da hannu bibbiyu tayi shiru tana jin zuciyar ta na mata wani irin zafi ga wani ƙululun abu daya tokare mata kirji shi bai sauka ba shi bai hau ba,ba sai ta ba kwakwalwar ta wahala gurin gano ko menene wannan ba, ko bata tambaya ba tasan menene, kishi ne, kishin shi take yi matuƙa gaya, kishi kuwa bana wasa ba, amma ta ɗaukar ma kanta alkawari zata jure zata danne, kodan ta dawo da martabar kanta a idanun shi, domin a yanzu tasan da ita da kashi duk daya suke a wajen shi, take hawaye suka balle mata kamar an buɗe fomfo, little na ganin tana kuka yazo ya rungume ta kamar yadda yaga tana yi mishi idan yana kuka ya shiga rarrashin ta yana cewa "Mummah kiyi shiru ki dena kuka zan siya miki sweet mai tsinke da ice cream." Samun kanta tayi da sakin murmushi jin abin da yake cewa, yaron yana da matukar wayo ga uwa uba surutu duk da ba ko wsni lokaci yake magana ba, idan yayi wani maganar takan yi matuƙar mamaki, sau da yawa takan ce, my boy a ina ka kwaso surutu haka, me sunan ka dai shiru shiru ne. Share wahayen ta tayi tace "OK my boy nayi shiru kaji, oya zo ka kwanta haka dare yayi." Kai ya gyada kawai ɗaukar shi tayi suka haye kan bed ɗin suka kwanta, addu'ar bacci ta shiga karanta mishi yana amsawa kamar yadda take mishi kullum, bayan sun gama ya shiga rero mata surutu, shiru tayi ta rufe idanun ta kamar ta yi barci ganin haka yasa shima yayi shiru take kuwa barci ya kwashe shi. Jin alamar yayi barci yasa ta mike a hankali ta zare jikin ta cikin nashi, bata jin bacci kwata kwata, dan ji tayi idanun ta sun bushe ƙamass Ta dawo gidan Aslam burin ta ya cika kamar yadda take so, sai dai Kuma hankalin ta ya kasa kwanciya kamar yadda ta zata, ta dauka idan yau ta ganta a cikin gidan Aslam a matsayin matar sa a karo na biyu shike nan duk wani damuwar ta ya yaye a she abin ba daga nan take ba, a lokacin da ta ta babbatar Aslam ya auri Asmah bayan bata, bata damu ba domin a wannan lokacin bata wannan take yi ba burin ta kawai Aslam ya amshe ta a karo na biyu, amma yanzu bayan ta samu wannan daman sai wani irin masifaffen kishin Asmah ya turnike ta, sai dai ta daukar wa kanta alkawarin zata yi yaki da zuciyar ta baza ta bari ta saka ta ta aikata aikin dana sani kamar yadda ta sakata ta aika ta a baya, toilet ta nufa dauro alwala tayi tazo ta gabatar da sallan nafila raka'a hudu, bayan ta gama ta dauki kur'ani ta shiga karatu, sosai tayi karatun ta, bayan ta idar kuma ɗaga hannu tayi sama ta shiga kwararo addu'a, duk dai akan Allah yasa Aslam ya yafe mata, Allah kuma ya bata karfin halin jure duk wani abu da zai mata, ya kuma rage mata kishin Asmah a ranta. Ba ita ta tashi ba sai kusan karfe ɗayan dare, koda ta hau gado ta kwanta gaban ta ne ya yanke ya faɗi tuno shin a wani hali iyayen ta ke ciki a yanzu, ta sani dole zasu shiga matsanancin tashin hankali musamman Dad, daga kwancen da take ta shiga yi musu addu'a akan Allah ya basu hakuri da juriyar daukar wannan lamari. Ba ita ta samu barci ba sai kusan karfe ukun dare.

A bangaren Aslam da Asmah kam yau suma haka suka kwana, kadaran kadahan, duk da Aslam yayi iya yin shi dan ganin ta saki ranta amma abin ya gagara, ya mata uziri yana ta binta yadda taso, har zuwa safiya bata cikin walwala, ganin yadda duk yabi ya damu sai wani lallaɓa ta yake yi, yasa taji ya bata tausayi dole ta aro walwalan karya ta yafa wa kanta, idan yayi wani abin dan ya saka ta dariya tayi murmushin yaƙe, hakan kuwa ya mai daɗi ganini haka ya samu karfin halin fita office duk da bai daɗe ba sha biyu ya dawo.

A haka suka kwashe kwana uku, zuwa lokacin Asmah ta sake sosai ganin ko kaɗan Aslam bai canza mata ba sai ma wani ƙarin kulawa da tattali na musamman da yake nuna mata, tuni ta ajiye batun wani kishi da wata zee suka bude sabon shafin soyayya, kuma har tsawon wannan kwanakin daga ita har Aslam din babu wanda ya saka zee da little a idanun shi, Asmah tana sane da hakan don lokaci lokaci sukan faɗo mata a rai, sai dai tana tsoron ta saka musu baki dan tana gani wannan tsakanin su ne matsalar su ce su ta shafa, kullum Aslam na part ɗinta bai taba cewa zaije wajen su ba, yadda ma yake yi kamar ya manta da wasu halitta a gidan, itama bata ce yaje ba, sai dai fa a can ƙasan zuciyoyin su tunani da kewar little ya hana su sakat, so ɗaya ta taɓa saka yaron a idanun ta amma ya kama zuciyar ta fiyye da yadda bata yi zato ba, shima Aslam ɗin haka kullum da tunanin yaron yake kwana yake wuni sai dai yaki zuwa gareshi saboda wani dalili da shi kadai ya bar wa kan shi sani, amma fa daure wa kawai yake yi. A bangaren zee kam duk fitar shi da shigar shi akan idanun ta, takan kwana kuka kamar hawayen ta zasu kare, little yayi ta rarrashin ta idan taki yin shiru shima sai ya fashe da kuka, daga karshe ta yanke shawaran da take ganin shine zai ɓullar da ita kan hanya, zatayi amfani da nata kalar hikimar ta karkato da hankalin mijin ta gare ta, bada tsiya koda tashin hankali ba, domin idan wannan tace zata yi a halin yanzu ita ce baza taci riba ba, dan ta riga ta sadakar Asmah ta sha gaban ta, ta ko wanne fanni.

Yau da ta kama kwana biyar da dawowar ta gidan komai na ɗan kayan abincin da ta aiki megadi ya siyo mata sun kare hakan ya saka bayan tayi wanka sun karya ita da little ta laɓe a abakin window kamar yadda ta saba, tana kallo har Aslam ya bar gidan, yana fita kuwa ta zaro galenta ta riko hannun ɗanta suka fito so take ta sake aikar megadi ya kara siyo mata kayan abinci. Daidai sunzo kofar part din Asmah, ita kuma ta buɗe kafar ta fito hannun ta dauke da kwandon shara da alama shiya fito da ita dan ta juye a babban drum dake waje, turuss suka ja birki dukan su suna bin juna da kallo, zee ce tace ta kawar da kallon ta hanyar sakar mata wani irin kyakkyawan murmushi, tana ƙarasowa wajen ta tace "manya idanun ku kenan, kun shige ciki shiru ba ajin ko motsin ku, to yau dai gashi mun haɗu ina kwana ya gajiya ya zaman shiru." Sororo ta tsaya can kuma ita ma
ta sakar mata murmushin yaƙe tace "ina kwana." Kama basken ɗin sharan zee tayi tace bari na taya ki zubar wa, saboda tsabar mamaki bata San ta sakar mata kwandon ba. Zee na tafiya ta mai da idon ta kan little da ke tsaye yana kallon ta, wani irin sanyi taji a zuciyar ta ta wahalu da kewar yaron, tsugunawa tayi ta maida tsawan ta dai dai nashi tace " zo my boy." Ta faɗa tana mika mishi hannu, sai da ya kare mata kallo sannan a hankali ya isa gare ta samun kanta tayi da saka shi a jikin ta ta rungume tsam, tana sauke ajiyar zuciya, zee data gama juye sharan kamar ance ta juyo, idanunta ya sauka akan abin da ke faruwa, da sauri ta dauke kanta tana sakin murmushi, abin ya burge ta lallai yarinyar bata da damuwa da alama. Gurin megadi ta ƙarasa ta bashi saƙon daya fito da ita koda ta juyo samun su tayi a gurin suna fira little sai dariya yake yi ko me take ce mishi oho. Tana isowa tace "iyyee mummy and son anata fira to me ake cewa nima a gaya min." Dagowa tayi wannan karon da murmushi gaske bana yaƙe ba ta kalle ta, taji daɗin yadda zee ta kira ta da sunan mummyn yaron, tace "sannu anty zee nagode." Zee tace."Ba komai anty Asmah." Sai kawai suka kwashe da dariya kamar sun saba da juna, zee tace "bari mu karasa ciki." Ta faɗa tana kamo hannun little maƙe kàfada yayi tare da lafewa a jikin Asmah duk dariya suka suka mai zee tace"iyee lallai yaro yaga mummyn shi na asali, to bari na barka a gurin ta zuwa anjima." Ta fada tana kallon Asmah, cikin jin dadi Asmah tace "ai kuwa nagode na samu dan taya hira." Cikin dariya zee tace "kin samu dan saka surutu dai." Kallon shi tayi tace "wai haka my son." Make kafaɗa yayi, zee tace "ai dama bazai ce eh ba sai kunje zaki gane nufi na, nidai nayi nan." Ta fada tana wucewa part din ta, Asmah ma daukar shi tayi suka shige nata part din.

Ranar tayi wunin farin ciki sai wasa take mai ta dafa mai indomie ta bashi a baki ta bashi wannan ta bashi wancen karshe har ya gaji yayi barci ta kaishi dakin ta ta kwantar, har yamma yana gurin ta, gashi ranar Aslam bai dawo da wuri ba, dan tun 2 take ta zuba ido shiru, wanka ta mishi itama tayi da yamma taci kwalliyar ta bata da kayan yara don haka tace bari taje ta amso gurin zee, koda ta fito falo ta samu ana knocking da sauri ta karasa ta bude duk a tunanin ta Aslam ne duk da bata ji diran motar shi ba, sai dai ga mamakin ta zee ta gani a bakin kofar murmushi suka sakar wa juna, Asmah tace "laa anty zee dama gurin ki nake shirin zuwa yanzu na amsar wa my son kaya sai kuma gaki shigo daga ciki mana kin tsaya a waje." Ta fada tana kauce wa ta bata hanya, zee tace "A'a anty Asmah ba sai na shigo ba naga yamma yayi nace bari na zo na dauke shi, Allah yasa dai bai miki rigima ba." "Ba wani rigiman da yayi min wasan shi ya dinga yi, yaron yana da saurin sabo ai." "Hmmm make dai kawai yayi ma haka, nima nayi mamaki sosai yadda ya aminta da ke lokaci daya yaron dake da shegen kyuyan tsiya." Murmushi tayi tace"Ki shigo mana anty zee." Zee tace "kin dai dage kar mai gidan yazo ya same ni." Dariya ta kwashe dashi tace "kaji anty zee dai to sai me idan ya ganki a nan É—in ai abin da yayi kara shi yayi ciyawa."

Zama tayi tana ƙarewa falon Asmah kallo, masha Allah komai yaji dan babu abin da nata zai nuna ma wannan ɗin ita sai take ga kamar wannan ɗin ma yafi nata tsaruwa, ruwa da darinks ta gabatar mata, sannan ta zo ta zauna, kan kace kobo fira ya barke a tsakanin su, kamar wasu wadan da suka daɗe da sanin juna, duk rabin firan dai a kan little ne, hankalin su ya tafi har basu ji Duran motar Aslam ba sai karan doorbell suka ji, gaban zee ne ya yanke ya fadi, take ta zazzaro ido waje kamar wata mara gaskiya, yayin da Asmah ta saki wani kayataccen murmushi, mikewa tayi da sauri ta nufi kofar fuskar ta dauke da madaukakin farin ciki. Tana bude kofar ya shigo baiko lura da su zee ba ya jawota ya rungume, lumshe idanu yayi yana sauke ajiyar zuciya kicin kicin kwacewar data shiga yi ne yasa shi saurin bude ido jin wani sabon abu yau, kasancewar shike facing cikin falon hakan yasa idanun shi suka sauka akan little kafin ya gama tunanin wani abu kuma ya hango zee zaune tayi kasa da kanta, sake ta yayi tare da hade rai yayi kicin kicin kamar bai taba dariya ba, duk walwala da anashuwar daya shigo dashi kan fuskarta shi take ta bace fat, ita kanta Asmah sai da ta firgita gani yadda ya juye lokaci guda, raɓa ta yayi ya haye sama abin shi ya bar ta anan sake da baki.

Tunda ta ji dirar mota hankalin ta ya bata shine ya dawo, cike da dauki na san ganin kyakkyawar fuskar shi ta dago kai tana kallon kofar sai dai abin da ta gani ya matukar dukar zuciyar ta, har sai da taji kamar zuciyar ta zai zillo kasa ya faɗo, da sauri ta dukar da kanta ta shiga kokarin komawa da zuciyar ta, tana maimai ta innalillahi wainnailaihi rajiun, kallon ta Asmah tayi, gaskiya taji babu dadi don ko ita ne baza taji dadi ba duk da dai baisan suna falon ba, kuma ji yadda ya wuce kamar bai ganta ba, kawai sai taji zee ta bata tausayi, nufar ta tayi tana kirkiran murmushi tana magana ta shiga ta mata amma bata san tana yi ba da alama tayi nisa sosai cikin tunani sai da ta ce "Anty zee!" Da karfi sannan tayi firgigit ta dago ganin ta yasa ta saki murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo amma fa na ciki na ciki. Tace " kin gani ba kin tsai dani gashi oga ya zo ya tarad dani gaskiya naji kunya kuma duk laifin kine." Ta fada tana mike wa da nufin daukar little su tafi sai dai ga mamakin su wayam ba yaro ba dalilin shi, zaro idon da tayi ne yasa Asmah saurin juyawa, itama abin ya daure mata kai to ina little din yake, abu kamar almara babu shi a falon babu alamar shi, Asmah tace ina zuwa ko yabi "honey sama ne." Da sauri ta haura tabar zee nan gaban ta na faduwa.

Samun shi tayi zaune a bakin bed ya rage kayan jikin shi ya bar dogon wandon suit da singlet little na kamkame a kirgin shi ya rungume yaron kamar zai mai da shi jikin shi, sauke ajiyar zuciya tayi ganin yaron a nan, fitowa tayi da sauri dan ta gaya wa zee ga ya cen gurin Aslam sai dai ga mamakin ta wayam taga falon, ko shakka babu ta wuce, wannan abu bai mata dadi ba gaskiya, zama tayi na kusan mintin goma tana tunane tanane lamarin Aslam ya mugun daure mata kai, yana son danta amma yace ita baya son ta to ko shakka babu wagga batu karya ce , jiki a sanyaye ta mike ta nufi upstairs tun kafin ta tura kofar dakin ta ringa jiyo dariyar shi shida yaron kamar zasu tada dakin, da sauri ta karasa ciki a kan gado ta hango su Aslam na kwance ya daura little akan kafarshi ya daga shi sama yana mishi lilo shi kuma yana ta kwasan dariya, ikon Allah tace a ranta, wannan lamarin da daure kai yake. Karasa wa ciki tayi ya dago yana kallon ta, rasa abin cewa yasa tace "sannu da dawowa." Sauke little yayi ya mike zaune yace mata "me ya kawo ta part din nan." Tace "kamar yaya." Hararan wasa ya watsa mata tare da cewa "kamar yayo." Dariya ta kwashe da shi tace "hira tazo muyi ko haramun ne kishiyoyi suyi hira a tare." Yace "bazan hana ki ba amma wlh kibi a hankali dan da kike ganin ta haka shalau shalau ba kanwar lasa bace." Dariya ya bata wai shalau shalau ta kuwa dara sosai tare da cewa " kai dai ka sani, koma ya take ai dai zabin ka ce, kuma sai na gaya mata." "Kin daÉ—e." Ya fada yana mikewa "muje ni da Allah ki bani abinci naci na kwaso yunwa da gajiyar aiki."

Ranar dai a part dinsu little ya wuni, a tsakanin su sai ji dashi suke yi suna wasa dashi, cikin kankanin lokaci yaron ya saba dasu, ko tunanin su maida mata É—anta basu yi ba har gurin karfe taran dare, Asmah ce tayi hankalin cewa "Baza mu mayar mata da shi ba, kaga dare yayi kuma ita kaidai ce a part din ta nasan tana cen tana jira." Share ta yayi, sai da ta sake maimai tawa sannan ya kalle ta yace "A nan zai kwana." Bata rai yayi ya mike tare da daukar little suka wuce sama dan ma kar ta samu daman yi mai wani magana, baya jin zai iya rabuwa da yaron koda na minti daya ne ba tare da wani kwakwarar dalili ba, zama tayi tayi shiru tana tunani, gaskiya basu kyauta wa zee ba idan suka yi haka, to amma ya ta iya, yanzu yanda ya haÉ—e ran nan tana magana cibi zai zama kari, a tsakiyar su yaron ya kwana ranan dan tsabar gata.

A bangaren zee kuwa hakan bai dame ta ba, sai ma dadi da ya mata, domin duk wanda ke kaunar danka ai masoyin ka ne, ko iya haka suka tsaya wlh sun nuna mata soyayya, a bangare daya kuma abin da ya faru dazu yana tsungulin ta a rai, sai dai tana danne wa , duk yadda sheɗan yaso yasa ta taga bakin Asmah taƙi yarda duk yadda zuciya ta hasaso mata sai ta kauce, ta daukar ma kanta alkawari tun da Asmah bata nuna mata wani mugun hali ba to kuwa ita baza ta nuna mata komai ba zata jata a jikin ta su zama kamar yan uwa hakan ma wani mata ki ne da zata samu kusanci da burin ranta.

Washe gari daker ya tafi aiki karshe ma cewa yayi zai tafi da yaron, daka tsallen albarka tayi ta hana, dan tasan idan har ta kuskura ta bashi wannan daman so daya ya dinga yi kenan kuma bazai maida hankali kan aikin shi ba. Yana tafiya ta dauke shi suka tafi part din zee dama sun riga sunyi wankan su sun karya. Da fara'a ta tare su babu alamun damuwa a fuskar ta, bayan sun gaisa Asmah tace "sai kika jimu shiru jiya ko." Murmushi tayi tace "ba komai ai yaro ya koma wajen Asalin mummy shi." Hakan data fada yama Asmah dadi take ita ma ta fara bata labarin yadda Aslam ya karbi yaron da yadda ya dinga mai harda cewa da yayi zai tafi dashi office, dariya zee ta ringa yi zuciyar ta wasai, Asmah ta bata wannan labarin ne dan ta faran ta mata rai kuma ta kwantar mata da hankali , aiko dai kwalliya ta biyu kudin sabulu, ranar a part din zee ta wuni tuni wani irin sabo da shaƙuwa ya shiga tsakanin su kamar ba kishiyoyi ba tare sukayi girki anan Asmah taga basu da kayan abinci sai wanda ta siya ta kuma kudiri aniyar yiwa Aslam magana, sai gurin karfe ukun rana ta koma shiyar ta ta daura ma Aslam girki, tuwon shinkafa tayi lafiyayye kuma gaba daya ta girka harda zee, tako ji dadi ta amsa tana ta mata godiya.

Cikin abinda baifi sati daya ba sun gama fahimtar juna, duk da kowacce zuciyar ta cunkushe yake da kishi musammam ma zee dan ita Asmah har yanzu bata San dawan garin ba tunda kullum tana tare da miji, zee na matuaƙar kokarin danne wa amma fa kullum Daren duniya sai tasha kuka ta gode Allah, Aslam gaba daya bata gaban shi kasancewar yanzu tana yawan zuwa part din Asmah dan tare ma suke hada dinner kullum duk idan ranar tayi rashin sa'a suka hadu takan gaishe shi, a dake yake amsa mata kuma kallo daya yake mata babu kari wannan abin shi yafi komai kona mata rai, bata da matsala ko kaɗan da Asmah sai wanda ba'aka rasa ba, little kam zuwa yanzu ya zama mai uwaye biyu yau ya kwana a nan gobe ya kwana a nan duk dai inda yaga dama.

Yau ma kamar kullum tare suka gama haɗa dinner, sunayi suna hira, Asmah ce ta fara kawo zancen Aslam cikin firan nasu, da sauri zee ta kauda maganar ta canza wata hiran Asmah ta lura sau da yawa haka take mata da ta dauko zancen Aslam zata doje, tausayi take bata sosai na yadda Aslam ya wofintar da ita, sau da yawa takan auna kanta a matsayin zee taga idan ita ake wa haka zata iya jura kuwa, duk sanda tayi wannan tunanin takan jinjina wa zee da hannu bibbiyu. Bayan sun kammala hada mata nata a basket Asmah tayi kamar yadda take yi kullum, dauka tayi ta tashi dan lokacin dawowar Aslam yayi daf, cikin tsokana tace ma little "muje." noƙe kafada yayi alamar bazai bita ba dariya suka zaka mai tace "dama tsokanar nake yi zaman ka wurin mummyn ka." Har takai kofa yace "Mummah." Ta juyo yace "kar kiyi kuka yau kinji." Kallon juna sukayi da Asmah, Asmah tace "kuka kuma?" Murmushin yaƙe tayi tace "shirmen little ne kawai rabu dashi." Tana gama fadin haka ta sa kai tabar part. Kuka kuka haka tayi ta maimaita kalman, tabbas yaro baya karya, to meke saka ta kuka ne, da sauri ta kalli little dake ta wasan shi tace "my boy Mummah ka na kuka kace." Yace "eh mana mummy kullum sai tayi kuka da daddare, ta ringa cewa Allah ya dawo mata da hankalin mijin ta,Allah yasa ya yafe mata, zuciyar ta zata fashe." Zama tayi dabass tana maimaita innalillahi wainnailaihi rajiun, lallai suna shiaga hakkin zee, baiwar Allah a she tana cikin damuwa har haka amma ko a fuska bata taba nunawa ba, kila ma tana jin haushin ta , kila ma ta ringa ganin kamar ita ta hana Aslam dawowa gare ta, tasan ba abinda baza ta ayya na ba tun da dai ita zuciya ai bata da ƙashi lallai Aslam yau ya dawo zata same shi suyi magana ta fahimtar juna.

Bayan sunyi shirin kwanciya yana zaune bakin bed yana wasa da little, zuwa tayi ta zauna a gefen shi, ta kalli little tace "my boy." Yace "na'am." Tace mema "Mummah ka ke cewa kullum idan tana kuka." Cike da rashin wayau yaron ya shiga jero wa harda wadan da bai fada dazu ba, kallon kallo suka shiga yi a tsakanin su, tace "to kaji daga bakin da bai san karya ba." Shiru yayi baice mata komai ba shi karan kanshi yasan abin da yake yi bai kyautu ba, amma bawai dan wani manufa yayi haka ba gwada ta yake yi yaga shin da gaske tayi hankalin kamar yadda ta sanar ko a'a kuma alhmdllh ya samu gamsuwa sosai da tuban nata, ya tabbatar tayi taubatan nasuhan kamar yadda ta fala kuma shima yana shirin ya koma gare ta amma shakkar Asmah yake yi, yana so ya koma gare ta,kodan fita haƙƙin ta,duk da dai har yanzu bawai yana jinta a ranshi bane kamar yadda yake jin Asmah, sai dai ya bata wani matsayi mai girma a ranshi ko ba komai ta ciri tuta domin ta kawo mishi farin cikin ruhin shi wato little......

Oum Ummeetarh
07041130088t
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALDO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu.}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.