Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 21 of 89

Page 39 & 40

A haka wunin ranar ya qare jikin Aslam a sanyaye minti kadan tunanin kamal da Asmah ya fadomai a rai, minti kadan hoton su lokacin da suka sakar ma juna murmushi ya fado mai a rai, da'ker ya samu ya yaqi zuciyarshi yayi fatali da wannan tunanin, yaci gaba da harkokin gaban shi, har zuwa dare,

Dare nayi anan ne ya raina kanshi don kasa bacci yayi. Sai tunane tunane yake, yana saqa yadda zai ruguza wannan soyyaya na cin a mana, yasan ko yakai maganar wurin manya babu mai goyan bayan shi, zasuce meye hujjan shi na hana kamal Auren ta tunda shi ya qita, zasu zata ko sonta yake, shi kuma yanzu a zuciyarshi babu burbushin sonta ko kad'an a ciki zee dinshi ita kadai ce a ranshi ita yake so itace za'binshi, itace irin macen da yakeso wayayya yar boko, shi mai zaiyi da wata Asmah baya sonta baya kaunarta, hasalima shi ya tsaneta, kuma tsanan da ya mata ne yasa baya son ta auri wani makusancin shi,

(kai dai kasani Mallam Aslam muna nan muna jiranka ka gama kewaye kewayenka zaka dawo kan hanya ne😬)

Da ire iren wadannan tunaninkan yaketa juyi akan makeken bed dinsa, baiyi aune ba sai ji yayi ladan na kwada kiran assalatu, zabura yayi ya miqe tsaye ya kunna wutan d'akin ,kallon shi ya kai kan agogon bangon dake d'akin biyar saura kwata ya gani, mamaki ne ya kamashi na tsowan lokacin daya dauka yana tunani, da haka ya shige toilet ya dauro alwala raka'atanil fajir ya gabatar kafin ya wuce masallaci.

A can ya taradda mazan gidan duka,manya da yara , baqi da yan gida, ana idar da sallah miqewa yayi yaje ya gaisar da iyayen shi , da kuma alhaji baba , su amir da kamal ma hannu ya basu sukayi musabaha,sannan ya fice daga masallacin bai jira kowa ba , don bacci yake son yayi kafin lokacin tafiya daurin aure yayi, Amir ne ya biyo bayanshi da sassarfa yana cemai "haba ango kasha kanshi , na zainabu Abu mai tagyayen suna bako jira" share shi yayi bai tanka ba , a haka suka iso part dinsu na samari, Amir nata tsokanan shi yaqi tankawa ,

Kowannen su daki ya shige , Aslam bacci yake ji sosai don haka yana shiga dakinshi ya haye kan bed dinshi ya duqunqune cikin bargo sai bacci, ko azkar da karatun alkur'anin daya sabayi kullum bayan asuba bai samu yayi ba, bacci ne ya kwashe shi mai nauyi, kasancewar bai samu bacci da daddare ba,

Daurin auren qarfe Tara na safe za'ayi don haka , su Abba da daddy da abokansa , da duka wani mai niyyar zuwa wajen daurin auren qarfe takwas kowa ya shirya,

Amir ne ya sakko downstairs cikin manyan kaya harda babban riga light blue, ya murza hula dark blue da ratsin light , sai zuba kamshi yake, a nan falon ya tarad da kamal shima cikin nashi shigar ta manta kaya iri daya dana Amir din, wasu daga cikin friend dinsu ne suka fara shigowa cikin , suma dai shadda light blue dinnne a jikinsu, da alama shadda light blue shine ankon da abokan ango suka fitar don zuwa wajen daurin a auren, zama sukayi , wadannda zasuyi breakfast suka fara yi, don tun saven thirty mami da sukaba kwangilar had'a breakfast din abokan ango ta aiko musu da shi,

Anas ne yace"ya kamata mu hanzarta kundan dai san anguwar da d'an nisa ". Dr bash yace"wai nikam ina angon ne " ya fad'a yana kallon Amir, Amir yace"may be yana shiryawa kasan shirin angwaye daban yake, amma dai barin shiga na fito mana dashi ". Miqewa amir yayi ya nufi upstairs don dubo Aslam,

Yana isa kofar d'akin knocking yayi shiru ba amsa, sake kwankwasawa yayi shiru again ,don haka ya kutsa kai tare da sallama , ba kowa a falon don haka ya nufi bed room tare da sallama ,

Wani irin zaro ido Amir yayi tare da furta"kutumelesi! Dalilin hango Aslam da yayi qudundune cikin bargo yana kwasan baccinsa hankali kwance, kunnna wuta mai haske amir yayi don dama ta cikin dim light yake hangoshi, tsayawa Amir yayi a kanshi ya riqe qugu yama rasa ta ina zai fara tashin shi, takaici duk ya gama cika shi ji yake kamar yata sharara mai mari a fuska,

Da zaimai mugunta da wlh Alhaji bab zaije ya dakko mai, saidai kawai yaji ruwan carbi a kanshi, amma yasan inya tsaya wannan duk bata lokaci ne,
Wata yar qaramar waya Amir ya zaro daga aljihunshi, itel ne wayan irin mai shegen qarannan, danno wani ringing turn mai uban tsiwa da kaudi hadi da vibration yayi, saida ya manna wayar a kunnen Aslam sannan ya danna play,

Aslam da yayi Nisan bacci sai jin wani irin kuwwa hade da vibration yayi a cikin kwkwalwan kanshi, a zabure yayi wurgi da duvet din da ya lilliba ya miqe tsaye, kanshi na wani irin sarawa,bude idon shi da sukayi nauyi yayi akan Amir dake ta kwasan uban dariya,

Aslam bai ce mishi komai ba don gaba daya kanshi ciwo yake mai bazai iya magana mai tsawo ba,

Saida Amir yayi dariyarshi mai isansa sannan ya bata rai ya koma serious face ya kalli Aslam dake lumlumshe ido alamar baccin bai ishe shi ba yace"dalla Mallam ware kaje kayi wanka ka shirya, kowa ya shirya ana jiran ka don tsabar iskanci Ashe kai kana nan qudundune cikin bargo kana barci". Sai lokacin Aslam ya tuna da daurin auren dake gaban shi"subhanallahi " ya furta yana mai d'an ware idanun shi dake lumshewa, daddafa bango yayi ya shiga toilet, wanka yayi shap shap ya fito, daure da tawul, nan ya tarad Amir ya ciro mai kayan da ya tanada don zuwa daurin auren,

Gaban mirror ya tsaya ya shafa mayukanshi da turarukan shi masu kamshi na jiki, wasu fararen sababbi fil din singlet da boxer ya ciro daga cikin wardrobe, turare ya fesa musu sannan ya koma toilet ya sanyo, saboda amir daya qureshi da ido,

Yana fitowa ya fara shiryawa cikin shaddan shi milk color mai mugun kyau da tsada, sai maiqo takeyi,

Riga ne da wando da babban riga dinkin zamani, an mishi aiki da zare coffee color, hulla milk da ratsin coffee ya saka, sai takalma cover shoes suma coffee, ba qaramin kyau Aslam yayi ba abinka da kyakkyawa cikin kyawawan kaya, abin ba'a cewa komai sai masha Allah.

Amir ne yace"wow wow angon zainab kaganka kuwa, gaskiya kayu kyau,kayi maza ka gama muje kaga su bash nata kirana, nasan kuma sunga na dad'e ne, shiyasa"ya fad'a yana ficewa daga d'akin zuwa main falo inda su bash suke,

Aslam saida ya daura agogon shi rolex mai kyau sannan ya biyo bayan Amir d'in, yana shigowa falon abokanshi suka dauki sowa da tafi ana tsokanan shi ango kasha kamshi, kasa amsa musu yayi don kanshi ba qaramin ciwo yake mashi ba, saboda baccin da baiyi jiya ba,gashi kuma Amir yazo ya tashe shi da dan iskan itel dinshi mai shegen qara , ya qara mai ciwon kan,

Kasancewar time yaja yasa basu tsaya wani bata lokaci ba suka dunguma suka fito coumpond din gidan,koda suka fito su Daddy da sauran jama'a tuni sun wuce, suma motocin su suka hau suka kama hanya kusan dukkansu suna da mota sai d'ad'd'ya wadan da ba aka rasa ba.

Wucewarsu ba dadewa, yan matan mummy na hango sun fito daga part d'in mami, da alama dai aiki suka taya mamin don dukkansu ba wacce tayi wanka a cikin su, sashen mummy suka nufa donyin wanka su shiya cikin ankon su na yinin biki, gidan yadan fara cika da mutane don haka falon mummy na qasa dana mami ma da suka baro cike yake da mata,

Gaisar da mutanen falon kawai sukayi suka wuce dakin su don shiryawa,.

Batool ce tayi wuff ta kama qofar toilet zata shige, zahra tayi caraf ta kamota tace "wlh baki isa ba keda kike shegen dadewa a wanka, shine zakice ke zaki fara shiga,wlh bazaki shiga sai na fito,

Nan batool itama ta cakumo ta suka fara kokawa, dama sun saba kusan kullum sai sun ta'ba,

Amira na ganin haka ta lalla'ba ta shige toilet d'in tana musu dariyar mugunta, karar rufe qofar ne ya dawo dasu haiyacinsu, nan ko suka koma kan amira cacacaca batool harda cewa allah ya isa ci mata layi da amira tayi,

Amira na jinsu tayi muqus gata itama ba baya ba wajen dadewa a wanka,

Asmah dai na zaune gefe kasancewar ta mara son haya niya yasa bata saka musu baki ba,shiru dai tayi tana bin kowa da ido in sunyi abin dariaya ta dara,

Amira don mugunta saida ta kwashe sama da rabin awa sannan ta fito batool ta shiga ,itama sai gungumi take alamar sai ta dad'e itama,

Wani tunani ne ya fado ma Asmah arai, take kuwa ta miqe tace musu tana zuwa, zahra tace"ina zuwa kuma" tace"kedai ina zuwa nace" ta fice d'akin mummy ta nufa don tayi wanka a can ta huta da bin layi , tasan ba kowa a d'akin mummy yanzu, cikin sa'a kuwa tana murda handle d'in, kofar ta bude, mummy bata kulle kofa ba kenan, shiaga tayi kamar yadda tayi tsammani ba kowa a dakin,toilet ta shige donyin wanka.

Karfe tara da minti goma aka daura auren Muhammad Aslam abdallah, da Zainab Abdussalam, akan sadaki masu yawan gaske,
Masha Allah daurin aure yayi jama'a saidai muyi fatan Allah ya zaunar dasu lpy,

Aslam da abokanshi sun shiga sunyi gaisuwar surukai kamar yadda yake a al'adar mutanen minna,

Direct kuma gida suka wuto in da zasu gabatar da reception kamar yadda Amir ya shirya,

A part d'insu Aslam din suka yada zango, nan ma'aikatan da aka turo daga galaxy hotel, inda akayi order abincin reception d'in suka shiga serving dinsu,

Abinci masu rai da motsi duk abinda mutum keso shi za'a zuba mai, ga drinks kala kala duk Amir ne ya dauki nauyin komai.

Cin abinbin su sukeyi suna firansu group group , kasancewar falon babbane yasa ya dauke su baki d'ayansu.

Aslam na zaune cikin kujera one sitter ya cire babban riga ya ajiye sai binsu yake da kallo, abin duniya gaba daya yabi ya dameshi, shi d'an farin cikin da mutum keyi bayan daurin auren shi, shi neman nashi farin cikin yayi ya rasa, kanshi ne ke matsanan cin ciwo ga kuma hayaniyar da friend dinsa keyi na qara mai ciwon kai, sai tsokanan shi sukeyi irin yadda abokai keyi, yayi shiru yaqi cewa komai saidai d'an murmushin yaqe,
Suma kasancewar sunsan halinshi na rashin son magana yasa basu wani damu ba.

Bacci yakeji sosai kuma yana gani idan har ya samu yayi baccin kanshi zai rage ciwo koma ya bari gaba d'aya, miqewa yayi da nufin yaje upstairs d'akin shi ya kwanta, wani tunani ne ya fado mai a rai, yasan indai ya kwanta a d'akin shi abokanshi baza su bari ya samu bacci yanda yake so ba, don haka rivas yayi daga niyar hawa saman ya nufi hanyar waje, ganin Anas nason tsaidashi yasa ya kara waya a kunnen shi kamar yana amsa call,

Sashen mummy ya nufa, yasan d'akin tane kawai zai samu yayi bacci hankali kwance , kuma su amir baza suyi tunanin yana can ba don ko d'akin mami yaje bai tsira ba tunda sunsan ya saba zuwa, zasu iya cewa bari su duba can in suna Neman shi,

Ganin alamar akwai mata cike da falon yasa yabi ta qofar kitchen ya haye sama ba wacce ta ganshi,

Dakin mummy ya shige ya qure A,c , sannan ya haye kan makeke bed d'inta' ya qudundune cikin bargo, inba mutum ya kula sosai ba bazai san a kwai mutum kwance a wajen ba.

Asmah wankanta ta sheqa sosai a toilet din mummy, bayan ta gama ta d'auki tawul d'aya daga cikin tawul d'in da ta gani a rataye a toilet d'in, ta daura, fitowa tayi kanta tsaye don tasan ba kowa a d'akin,

Aslam jin motsin an bude qofar toilet yasa ga bud'e idanun shi don ganin ko waye, Asmah ya gani ta fito daga toilet d'in daure da d'an,qaramin tawul da bai gama rufe mata cinyoyinta ba
Numfashin shi ne ya shiga seizing gabanshi ya shiga fad'uwa zuciyarshi ya shiga bugawa da sauri da sauri,

Asmah kam direct gaban mirror mummy ta nufa kasancewar tasan duk abinda take buqata na shafa akwai a kan mirror mummy, yasa taga gara ta tayi shafe shafenta anan gaba d'aya, inyaso tana komawa sai dai tasaka kayanta kawai,

Madubin na fuskantar gado ne don haka juyama Aslam baya tayi, kwata kwata bata lura da wani Aslam a d'akin ba,

Qurama bayanta ido yayi qur baya ko qaftawa, tun daga sama hara qasa yake qare mata kallo, dogon baqin gashinta dake kwance a bayanta, yabi da kallo kasancewar ta wanke kai yasa gashin kwanciya luf luf a kafad'unta ,sauko da idanun shi, yayi kan mazaunanta da suke nan masha Allah dasu,ga wani irin lafiyayyen hips da Allah ya hore mata kamar wata babban mace,

Tunda yake bai taba sanin haka qirar yarinyar nan yake ba, bai taba sanin haka take da kyawun diri ba sai yau , irinta ne maza kema laqabi da mai coca cola shape wasu kuma suce figure 8,

Yana wannan tunanin ne yaga ta sauke tawul d'in ta daurashi a qugunta taci gaba da shafa manta hankali kwance, baya ganinta ta cikin madubin kasancewar fitilar dakin bamai haske bane sosai,

Tana gama shafa mai a jiki yaga ta miqa hannu zata sauke tawul d'in qasa gaba daya donta shafa mai a qasanta ,

Wani munafikin tarine ya sarqe aslam wanda baisan daga ina ya fito ba , jinshi kawai yayi yana tarin ,

A firgice Asmah ta juyo jin tarin mutum a bayanta, idanunta ya sauka akan Aslam dake duqunqune cikin bargo, yayinda shi kuma idanun shi ya sauka akan tsayayyun madaidaitan breast dinta da suke cike tam tam a qirjinta, Wanda tsabar tsoratan da tayi jin motsin mutum a bayanta yasa ta juyo ba tare da rufesu ba, don ita duk zatonta gamo tayi,

Wani gigitaccen qara ta saki tare da tsugunawa ta qamqame jikin ta a wurin tana maqerqerta, gaba daya kwakwalwarta tsayawa yayi da aiki a lokacin, tama rasa me zatayi donta kare kanta, banda tsugunawar nan da tayi ta dunqule wuri daya kasa aiwatar da komai tayi,

Aslam kuwa lokacin daya juyo tsayayyun breast d'inta ne suka fara mai sallama,wani Yarr Yarr yaji a jikinshi kafin kuma wutan kanshi ya dauke dif ,na wucin gadi, daga bisani kuma ya miqe kamar an tsikareshi ya buga wani uban tsaki, cike da borin kunya yabar d'akin, ta qofar kitchen din daya shigo tanan ya bi ya fice daga part din jiki a sanyaye🚶‍♂️🚶‍♂️🚶‍♂️🚶‍♂️

Karku manta comment d'inku shike qaramin qaimi wajen sambad'a muku typing🥰

Oum ummetarh
07041130088

Share
And
Comment🙏🏻
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.