Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 25 of 89

Page 47 & 48

Aslam na shigowa falon ya hangi mutane cike da falon , butum biyu kawai ya waya a cikin su mom da dad d'in zee,sai sauran da bai
taba ganin su bama, hango zee yayi kanannade jikin wani qaton mutum fari Sol da gani kasan bature ne, sai wani kukan shagwaba take mishi, tana cewa zatayi missing dinshi sosai, shi kuma sai shafa bayanta yakeyi yana bata hakuri, sauran mutanen falon kuwa sai dariya suke including mom and dad,

Jiki a sanyaye Aslam ya qara so cikin falon zee na ganin ta miqe daga jikin best friend d'in nata, tazo da sauri ta rungume shi, ci gaba tayi da mai kukan shagwaban tana cemai wai mom da dad da friends d'inta da suka zo mata biki daga Malaysia zasu wuce su barta,

Badan yaso ba yayi hugging nata back, qarasawa yayi ya gaida mom da dad, a yatsine mom ya amsa da lfy, dan ita har yanzu haushin shi takeji gani take shi ya hure ma zee kunne har ta nace sai ta aure shi,

Dad d'in ma dai a dake ya amsa kamar an masa dole, iya su kadai ya gaisar a falon ,don duk sauran , yan matane qawayen zee sai wannan namamajon best friend d'in zee d'in, zame ta yayi daga jikin shi ya tashi zai haura sama , har zai fara taka step ya tsinci muryar dad na cewa " uhmm Ashmal kake kowa," zee tace "Aslam fa". Yace"koma wanene zo nan inada magana da kai" a gadarence Dad kemai magana, datajar sukurtaka Aslam ya duba ya dawo , zama yayi a kujeran dake facing Dad , a wulaqance Dad ya kalle shi yace"kayi nasara a kaina ka rusamin tsarina kasa na aikata abinda baya cikin tsarin rayuwata a yanzu, wato rabuwa da my one and only daughter ta , well done kayi qoqari , bazan ce ka riqeta da kyau ko amana ko whatever ba , amma ka sani duk abinda ya samu y'ata na cutuwa saina daureka , koda kuwa ciwon Kaine , ka kiyaye, duk abin da ake mata a gidansu shi zaka mata duk abinda tace tana so shi zaka mata dole kaji na gaya maka,"

Kallon matar shi yayi yace "ku tashi muje kunsan jirgin qarfe goma zamuje bi gashi har nine thirty yayi" cikin kuka zee taje ta rungume dad da mom tana kuka , mom saida ta share hawaye itama saboda kewar yarta, fita sukayi suka shiga motocin su suka bar gidan , zee daqar ta rabu da jikin iyayeta,

Aslam kam kasa musu rakiya yayi, yana zaune a falon jikin shi a sanyaye, zee ta shigo ta same shi,
Zama tayi kusa da shi tace "honey yunwa nake ji" kallonta yayi yace"ki dauki kazar dana shigo dashi jiya ki mana warming dinsa sai ki had'a tea ki karya dashi" yatsina fuska tayi tace"honey gsky ni bazan iya wani warming d'in kaza yanzu ba a san dai yacce za'ayi, kokuma mu fita kawai muyi breakfast a waje,"

kamar zai musa mata kawai yace taje ta shirya suje to, miqewa tayi ta haura sama danta shirya,

Yana zauneta sakko cikin riga da wando d'amammu, ta yana wani dan siririn gyale a kanta ta saka wani uban hill,

Binta yayi da kallo kafin yace"ina zakije a haka " kallon jikinta tayi , ita bata ga wani abun da saya yake mata wannan tambayar ba, tace "na shirya muje ko" yace "kije ki sanya hijabi kinsan yanzu fa ke matar aurece bazaki dinga shiga any how ba" ranta bai so ba haka ta juya , a zuciyarta tana mita Aslam ya fara kaita bango fa, komai tayi sai yace baiyi daidai ba ita fa batason takura , tana daga mai qafa nefa,

Zuwa tayi ta dauki after dress ta daura akan kayan don ita Allah ya gani baza ta iya fita da hijabi ba , sai kace wata tsohuwa,

Shima bai ce mata komai ba ganin ta rufe qananan kayan , suka fice,

Wani babban restaurant sukaje , suka yi order abinda sukeso, Aslam tsakara ya dinga yi, danshi baya son girkin waje , ko girkin qannen shi ba kullum yake ci ba, balle wannan da baisan wasu qazamai suka girka ba, musulmai ne ko arna, ita ko zee hankali kwance take cin abincinta,

Suna gamawa suka dawo gida, wanka suka qarayi tare, suka shirya cikin kayan shan iska, dawowa falo sukayi suka zauna, Aslam na zaune kan dogon kujera ita kuma tana kwance, kanta akan cinyarshi, charting takeyi da friend dinta , shi kuma lulawa yayi duniyar tunanin kalaman amir na dazu, ga yunwa dake sakadar cikin sa , dole miqewa yayi ya nufi kitchen da kanshi yayi warming gasasshiyar kazar jiya ya hada tea ya sha , yana ci zee ba kunya tazo ta saka hannu sukaci tare , suka gama ta wanke hannunta ta tashi ko plate d'in shiya dauke ,

Da rana haka suka qara fita cin abinci, haka da daddare, Aslam haka ya wuni da yunwa, don ba abincin kowa yake iya Ciba, a kwaishi da kenkyami, saidai ya sha drinks da cake,

Da daddare ba yanda baiyi ba da zee ta bashi had'in kai taqi, saida ta biye mai suka sha romance kala kala, ta zame jikinta , dole ya hakura ya kwanta, nan kuma tunanin Asmah da kamal ya mai sallama da'ker ya samu bacci ya daukeshi,

Washe gari da asuba bayan ya tada ta da'ker ya tafi masallaci kafin ya dawo har ta idar ta koma ta kwanta , tashinta yayi yace tazo zai fara koya mata karatun addini, qin tashi tayi , saida ya mata Jan ido ta taso tana gungumi,

Karatun suratul fatiha yace tamai, tiryan tiryan tayi , sai dan kuskure kad'an kad'an daya gyara mata, surori ma ta iya falaqi da nas da iklas, ganin ta iya na sallah , yasa yaci gaba da koya mata alwala da farillansa da sunnonin sa, da yake taga ranshi a had'e yasa ta maida hankalinta sosai har tadan fahimta, iya nan suka tsaya , yace gobe zasu tashi a sallah da farillanata, jibi kuma suyi wanka,

A haka suka kwashe sati daya da aure kullum sai sun fita safe rana dare yawan cin abinci, ga tunanin Asmah da kullum yake addabar zuciyarshi, ba abin da yake sonyi kullum sai ganinta, zuwan shi gidan uku baya ganinta taje school,

Yau dai Aslam ya gaji da yawan zuwa cin abinci a restaurant , ya qudiri aniyar yau zee zata fara girki,

Bayan sun idar da karatun su na asuba daya zamema zee matuqar takura, nan ya sanar mata batun girki yi tayi kamar bata jishi ba , dama duk haqurinta ya gama karewa akan shi kiris take jira,

Komawa tayi ta kwanta bayan sun gama karatun ba ita ta farka ba sai sha biyu, lokacin tuni Aslam ya fita ya siyo bread ya had'a tea ya qarya, don ba irin tashin da bai mata ba tana ji ta share,

Warwatsi tayi da kayan data cire a nan tsakar d'akin ta, ta shiga toilet tayi wanka , ta shirya cikin kayanta na gado , qananan kaya,

Falo ta sakko nan ta samu Aslam zaune yana danna system dinsa, baiyi fushi da ita ba, bud'e mata hannayenshi yayi fuskarshi dauke da murmushi zuwa tayi ta shige jikin shi, yace"gimbiyata kin tashi " murmushi tamai , ki tashi kije kiyi breakfast, OK tace

Miqewa tayi taje dining nan ta tarad da kayan tea da sinkin biredi sai kofina duddubawa tayi taga iya su kenan akan dining d'in, dawowa tayi gun Aslam wai bataga abincin akan dining ba , ko suna kitchen ne,

Dagowa yayi yace"baki ga biredi da kayan tea akan dining ba " tace "nagani dama sune abincin" yace "eh, tunda baki girka mana ba ai dole tea zamusha" tace"gsky honey ni bazan ci biredi ba , kasan dai yadda zakayi dani don yunwa nakeji, kokuma kaje ka siyo min abinci, " yace "wlh ba inda zani yau inkin matsu ki shiga kitchen a kwai komai ki girka abinda kike buqata "

Tana zumbura baki ta nufi kitchen d'in , kwai ta fasa zata soya , ta kusa kwashe awa daya ta fito tana hada uban zufa,da kwan ba'ki kirin da shi duk ya qone gashi ya ji uban gishiri, hada tea tayi ta zauna , loma daya tayi ta furzar dashi, dole dai boredin taci tabar kwan a gurin ta wuce ta kwanta abinta ba shara ba wanke wanke,

Aslam saida ya gama aikin da zaiyi a system dinshi ya tashi zai gifta ta kusa da kitchen yaji qauri na tasowa da sauri ya nufi kitchen d'in, frypan d'in data soya kwai ya gani akan hot plate d'in data kunna ta soya kwan,

frypan yayi jajur kamar garwashi, da sauri ya qarasa ya kashe hot plate d'in, ya sauke frypan din, Juyowan da zaiyi ya zame ya fad'i qasa tim, kallon qasan yayi fasassun kwaine kusan uku, ruwan su duk ya zube a qasa shi kuma bai kula ba ya taka ya zame, dama ga tsantsin tiles, kitchen d'in yabi da kallo yayi caca yau d'aya da madam ta fara shiga soya kwai, cikin dan fusata ya nufi dakin ta.

Ganinta yayi kwance tayi dai dai tana charting da friend d'inta tana kwasan dariya bata ma San ya shigo ba, ga d'akin baza baza da kaya ,

Qarasawa yayi yasa hannu ya fisge wayarata, dagowa tayi tana kallonshi, cikin dan fushi yace"haba zainab ki tashi ki danyi share share mana kinga kitchen yanda kika barshi ba kyan gani ga falo tunda kikazo gidan nan baki ta'ba share shi ba duk ko ina yayi qura ,kalli dakin nan pls for god sake, bama a batun toilet, haba da Allah komai sai ance kiyi , wa kike son ya gyara miki ke ko kunya bakiji, kiyi baqi,"

Miqewa tayi daga kwancen data ke, tace"dakata Aslam ban gane me kake nufi wai nice zan dinga wanke wanken kowa? Lallai ma da sake, kalleni sama da qasa banyi kama da yar wanke wanke da shara ba tun wuri inzaka nemo mai aiki ka nemo, danni a gidan mu ko tsinke bana kawar wa, aure na kayi ba baiwar ka bace kaji da kyau, OK sai yanzu na gane dama ka auroni ne dan nazo na dinga maka bauta, to wlh baka isa ba karyarka tasha karya " ran Aslam yayi qololuwar baci a tsawace yace"zainab ni kike gayawa irin wadannan banzayen maganganun," tace "na gaya maka kai waye , duk shiru shirun da kaga ina maka qyale ka kawai nayi amma tunda na fahimci baka da mutunci wlh nima bani da shi, " shammtarsa tayi ta fizge wayarta a hannunshi , ta kwanta taci gaba da dannawa.

Ba qaramin kai zuciya nesa Aslam yayi ba da bai rufeta da duka qafa da qulli ba, fita yayi a dakin yaje falo , kasa zama yayi sai safa da marwa yakeyi, daga karshe tausasa zuciyarshi yayi ya dauki tsintsiya da mopa ya share ko ina na part d'in except dakin zee, yayi mopping , ya feffesa air freshener,

shi kwata kwata baya son qazanta, kuma babu abida yafi tsana kamar yan aiki a rayuwarshi , saboda kenqaminshi ko dakinshi shi da kanshi yake sharewa a gida ya wanke toilet dinshi da kanshi , kuma haka ya tashi gidansu banda driver da mai gadi bai taba ganin wani ko wata da sunan mai aiki ba ,komai kannen shi da iyayen shi keyi a gidan su, dan haka shima baiga dalilin daukar yar aiki a gidan shiba ,

yana gamawa dakin shi ya shiga ya yayi wanka yabar gidan , har Allah Allah yakeyi hutun daya dauka a wajen aiki ya cika ya fara fita yana bar mata gidan,

Direct family hause ya nufa part mami ya fara shiga suka gaisa ta sanar mishi Mallam dinsu Asmah ya amince zai fara zuwa gida sati da lahadi yana koyama zee karatu amma da safe zai dinga zuwa sabanin su zahra da yake zuwa da yamma,

Yana fitowa ya shiga part din ga jiya mama nan suka gaisa tana tambayarshi ina kishiyarta , "wai bazai kawota mu gaisa bane, kodan tasan nafita kyau ne take tsoran zuwa mu gaisa" , dariya yayi yace "wane ke kifi amaryata kyau" tace "ba wani nan inda gaske ne ka kawota mu gwada kyau a gani'dariya ta bashi wai su gwada kyau , aiko ya dara , a nan yadan rage damuwan dake damun shi, yana son hajiya mama, itama tana sonshi sosai cikin jikokinta, daga nan falon alhaji baba yaje suka gaisa kadaran kadahan , don har yanzu ba wani shiri sukeyi ba tun abinda ya faru , na kwanaki,

Daga karshe ya yada zango a part din mummy don yau duk yadda za'ayi ko dare zai kai a gidan sai ya tsaya yaga Asmah , don akwai abinda yake son gaya mata,

A main falo ya samu mummy , nan ya zauna suka gaisa , ta tambayeshi zee yace tana lpy,ta sake tambayar suna dai zaune lpy ba wani matsala ko , nan ma yace lpy qalau, mummy tace masha Allah, taja bakinta tayi shiru, tunda dama bawai sun saba fira bane ,iyakarsu gaisuwa,

Katse shirun yayi da cewa"mummy yaran nan fa su zahra" mummy tace"sunje school,amma inaga suna hanya don sunce yau da wuri zasu dawo, lpy dai ko kake neman su".
"Lafiya qalau"ya amsa ma mummy, can kuma ya tambayi abinci, mummy tace bai qarasa yace to ,ganin zaman shirun yayi yawa, wayar shi ya Ciro ya bud'e data ya hau WhatsApp dan ya debe ma kanshi kewa , message ne suka fara rige rgen shigowa, dan yafi sati rabonshi da hawa WhatsApp, saida suka gama shigowa , kaf ya fara bi daya bayan daya yana dubawa Wanda zaiyi reply yayi, daya gama duba message ya shiga status,

Da status din kamal ya fara cin karo, wani short video ne na hotunan Asmah kala kala, wani tana murmushi wani ta bata rai wani tana dariya , ga sunan dai barkatai , wani kuma ita dasu batool, wani wakar soyayya na hamisu bireka yasa akan video ,a kasa kuma gurin caption yasa emojin luv da arrow a jiki guda uku💘💘💘,

Aslam ji yayi kanshi na juyawa ganin wannan status din na kamal, zuciyarshi yaji ya dauki zafi ,
Girgiza kai ya fara yana kwafah can kuma yayi tsaki,

mummy dai na zaune tana kallonshi, bata ce kala ba amma tana mamakin , meya canza mai mood yanzu yanzu haka

Bata gama tunani ba taji yana cewa "lallai kamal watan cin ubanka ya kusa kamawa wlh " mummy dake gefe tace "subhanallahi Aslam kana da hankali" firgigit ya juyo ya kalli mummy , Ashe zancen zucin da yakeyi ya fito fili,

ta sake cewa"me kamal d'in ya maka kake cewa, watan cin ubansa ya kama, " miqo ma mummy wayar yayi ya kunna mata video yace " mummy kalla , kalla fa abin ya saka a status dinshi , duk qattan duniya fa sai sun gama ganinta ," mummy na gama kallo ta d'ago tana kallon Aslam duk mamakinshi ya gama cikata tace" ikon Allah to kai ina ruwanka don yasa hotan Asmah a status dinshi, meye naka a ciki meye damuwarka a ciki, ka sanima ko soyayya sukeyi, tunda kai ka qita, sai Allah ya musanya mata da kamal yaron kirki , kai kuma ya musanya maka da zainabu ba shike nan , ai wannan ba abinda ya shafeka bane"

Duk da Aslam ya Riga yasan kamal da Asmah , soyayya sukeyi saida kalaman mummy ya dake shi , a fili ya dinga furta "soyayya! soyayya!! Kai ina bazai yuwu ba , yanzu mummy inma soyayyan sukeyi sai ku barsu , bakwa ganin kaman cin amanata akayi kenan yana matsayin qani a gareni ya auri ex wife d'ina"

Mummy da mamakin Aslam ya gama kasheta cikin tsawa tace "kaiii Aslam wani irin maganar banza kake yi haka, to a hir dinka inma Asmah da kamal soyayya sukeyi nice wacce zanfi kowa farin ciki da hakan , kai Allah yasa hakan kaje anci amanar taka kayi abinda zakayi, " kamar zaiyi kuka ya dinga maimaita " haba mummy haba mummy haba mummy" mummy tace"don't call me" ya bud'e zai CE wani Abu Asmah tayi sallama a falon, dukan su juyowa sukayi suna kallonta, ita karan kanta saida tasha jinin jikinta da ganin irin wannan kallon...........

Pls fan's kuyi haquri kwana biyu muna biki ne ,amma mungama jiya, posting will be continue, insha Allah, no stop

Oum ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fi sabilillah🙏

💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar sa wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.