Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 22 of 89

Page 41 & 42

Asmah jin qarar qofa alamar ya bar dakin, ta tashi da sauri ta rarumi hijabin mummy data gani, ta zura akan tawul din jikinta ta fice daga dakin itama duk ilahirin jikinta rawa yakeyi,

Saida ta tsaya a qofar dakinsu ta saisaita kanta sannan ta shiga, samunsu tayi suma duk sunyi wanka suna shiryawa, wucesu tayi ta fada kan gado rigingine,

Kallon kallo su zahra suka shigayi a tsakanin su, Amira ce tayi qarfin halin qarasawa bakin bed d'in, ta dago kan Asman ta daura kan cinyarata, sannan tace, "lafiya sister meya sameki" alama Asmah ta mata da hannu kanta ke sara mata,

Batool ce ta qaraso da sauri ta zauna kusa da ita tace " ayya sannu Asmah, sannu kinji, kwanta ki huta qila aikin hada breakfast d'in da mami ta saka mu dazu ne, yasa mata ciwon kai kunga ita ta zage taketa aiki sosai , kunsanta da rashin ganda,"
Zahra tace barinje na dauko miki maganin ciwon kai a d'akin mummy, girgiza mata kai tayi alamar ta barshi bazata sha ba,

Kwantar da ita Amira tayi suka ci gaba da shirin su, sunyi suna mata sannu,rintse idanuwa tayi kamar mai bacci, take abubuwan da suka faru few minutes da suka wuce,suka shiga dawo mata fresh a kwakwalwarta, innalillahi wainnailahi rajiun ta shiga maimai tawa acikin zuciyarta, gaba d'aya ranta a jagule yake, gsky Aslam ya cuceta , kuma Allah ya isa ganin jikinta da yayi, bata yafe ba,

A hankali ta fara samun relief a cikin zuciyarta , saida ta kwashe kusan fourty minutes a haka kafin ta yunqura ta miqe, ganin tunanin ba abinda zai haifar mata sai qarin takaici da damuwa, tunda abinda zai faru ya riga ya faru , sai a kiyaye gaba,

Zuwa lokacin su Amira sun gama shiryawansu tsab da su sunsha makeup kowacce ta kashe daurin zamani kamar sune amaren,

Ganin ta miqe yasa suka shiga jera mata sannu, tare da tambayar ta ya kan, da sauqi tace musu ta shiga toilet ta wanko fuskarta, tazo ta zauna itama batool ta tsantsara mata makeup, tayi kyau kuwa sosai kamar wata balarabiya, Amira ta miqo mata nata kayan tasanya,

Wow masha Allah Asmah kam tana da kyau sosai tun daga kyawun fuska, kyawun diri, uwa uba kyauwun hali da kyawun zuciya,

Kashe dauri tayi itama suka fantama cikin gida akaci gaba da yinin biki dasu,

Asmah kam jikinta a sanyaye yake, tun abinda ya faru dazu amma haka ta daure taci gaba da harkokin gabanta, har zuwa dare inda nan suka kuma caba wani adon cikin ankon su na dinner.

Aslam kam yana barin part din mummy, parky lot ya wuce ya bude motarshi ya shiga back sit ya zauna , tunanin abinda ya gani few minutes ago ne ya shima mai yawo filla filla a cikin brain dinshi, yana kisima kyau da tsaruwar halittan yarinyar, tunanin daya dinga yi kenan har baisan tsawon lokacin daya dauka yana zaune cikin mota yana tunanin ba , baccin dai da bai samu yayi ba kenan,

Can kuma kamar daga sama yaji wani bangare na zuciyarshi na kwa'banshi da cewa, meye haka kakeyi Aslam, ka zauna kana bata lokacin ka a banza kana tunanin wannan mayyar yarinyar, me take dashi da har zaka tsaya kana tunanin ta, kaida kake da amarya kamar zee babban yarinya meye na jikin wata mace zai rudeka, har ka zauna kana 'bata time d'inka a banza a hofi, tsaki yaja a fili tare da fitowa daga motar ya nufi sashen su, yana isowa kuwa ya taradda wasu friend d'insa nata neman shi sumai sallama, zasu wuce, yayinda wasu da dama sun riga sun wuce saida a had'u wurin dinner anjima.

A mooris event za a gudanar da dinner Wanda za,a fara 9 a gama 1am,

Misalin 9:30 na dare yammatan mummy na hango zaune a falon mummy sun sha makeup, sai zuba kamshi sukeyi,kamar wadanda zasuje gasar zabar sarauniyar kyau, su biyar ne yau harda Khadijah da suka zo d'azu da mamanta, mamanta bazata kwana anan ba gidan alhaji Mallam zata kwana, ita kuma Khadijah tace anan zata kwana don tana son zuwa dinner, da'ker mama ta barta saida mummy ta saka baki,

Itama Khadijah taci kwalliyarta cikin lece dinta milk colour kasancewar ita batada ankon su Asmah

Kamal ne yayi sallama yace su taso suje, dama shi suke zaman jira, don yace in sun shirya su jirashi ya zo ya daukesu.

Miqewa sukayi suka bishi, suna shiga harabar gurin taron Kamal yayi parking suka fito suka shiga cikin hall d'in, wuri saka nema suka zauna , had'ad'd'un samarin dake wajen kuwa sai binsu da kallo sukeyi sunga kyakkyawan yammata, wuri ya tsaru sosai amarya da ango sun zuba kyau, kamar wasu wata da zahra a cikin sararin samaniya, anfara gudanar da komai cikin tsari da wayewa,an kira amarya da qawayenta sun taka, haka ma ango saidai shi angon baiyi rawa ba sabanin amarya da ta tiki rawar ta, kamar ba itace amarya ba, liqi kam anyishi kamar ba gobe su zahra ma sunje summa yayansu liqi amma basuma zee don duk haushinta sukeji,

(tab zee bata samu shiga ba wajen qannen miji😅)

Kamal kam kasawa yayi ya tsare Asmah ganin irin kallon da mazan gurin ke binta da shi, guri ya samu kusa da ita ya zauna yana gadin kayarsa, suna dan fira jefi jefi,

Amir dake zaune a high table kusa da ango a matsayin babban abokin ango,tun shigowar su Asmah hara zuwa sanda sukaje sukayi liqi hankalinshi na Kansu, ganin yawanci mazan wurin hankalin su na Kansu yasa yaji gaba daya hankalinshi bai kwanta. Shawarar da zuciyarshi ta bashi yabi, sakkowa yayi daga kan high table din, ya nufo inda suke, suna ganin shi suka shiga gaishe shi amsa musu ya shiga yi cikin sakin fuska yana dan tsokanansu irinta abokan wasa, kallon Amira yayi yace"am Amira pls zoki tayani shigo da wasu kaya daga mota ," to Amira tace tare da miqewa tabi bayan shi suka fita daga hall din, suna Zuwa gurin motar shi mai makon taga ya bude mota ya dauko mata kayan daya ce,sai gani tayi ya jingina da jikin motar ya tsaya yana kallonta,itama kallon nashi tayi taga meya tsaya yi bai dokko mata kayan ba, suna had'a ido ya sakar mata wani kyakkyawan murmushi mai dauke da manufofi kala kala, gabanta ne yayi wani irin faduwa,ya salam ta furta a zuciyarta, batun yau ba ya Amir ke burgeta musamman in yana wannan murmushin nashi mai masifar kyau,

Ya Amir kyakkyawan gaske ne gashi da masifar sauqin kai ba kamar ya Aslam mai shegen girman kai da rashin fara'a ba,

Amir ne ya katse mata tunani da cewa "Amiran mami an girma yanzuma shekaran ki nawa " d'ago kai tayi tana kallonshi jin tambayar da ya mata, aiko gani tayi ya qara mata ido sai murmushin shi mai kyau yake saki, kunyarshi taji ya kamata ganin irin kallon da yake mata, fuskarta ta rufe da tafukan hannayenta tana murmushi tace" sha takwas fah'. Amir yace"masha Allah ashe dai yarinyar ta zama ammata, to yaushe zaki turo mana sirikin mu yazo ya gaishemu mu big big brother's". Aiko da sauri ta bude fuskarta tace "laaa ya Amir nifa bani da saurayi" wani boyayyan ajiyar zuciya Amir ya sauke tare da ce mata "da gaske" tace ". Eh " yace "aiko ya kamata kiyi saurayi kin zama ammata yanzu eighteen years fa"

Haka Amir yaci gaba da jan Amira da fira yana bugan cikin ta yana mata wasu tambayoyi da wayau, hakan yafi mai kwanciyar hankali akan ya barta cen wasu qattin banza su dinga kalle mai tanadin shi na shekara da shekaru har a samu wani mai tsaurin ido yazo yamai shigar sauri, wanda yake ganin bazai taba lamuntar hakan ba,

A can cikin hall kam anata ci gaba da gudanar da programs hankali kwance, wayar Amira dake hannun batool yayi qara, kallon su zahra batool tayi tace "kunga Amira daga zuwa dauko kaya shiru shiru tana neman kwashe awa guda, ko lafiya" zahra tace "wlh nima tambayan da zanyi kenan kika rigani, a baki". Wayar ne ya sake ringing batool tace"gashi ma anata kiranta barin kai mata wayar daga nan na duba ko lfy "

Cikin sauri sauri ta miqe riqe da wayar Amira a hannunta, ta nufi qofar fita daga hall hall din, tana d'an gudu gudu sauri sauri dinta samu ta kai mata wayar kar call din ya katse, dai dai qofar fita suka zabga wani uban karan da saida kofin glass d'in daka hannushi cike da ruwan taceccen lemo ya fadi qasa ya tarwatse bayan ruwan lemon ya xubar mishi a jiki, baya tayi taga taga zata fad'i , Allah ya taimaka jinta tayi a jikin mutumin da suka zabga karo ya tarota jikin shi, handset din amira dake hannunta tuni ya fadi qasa, kallon fuskarta Dr bash yayi don yaga da wa yaci karo haka, idanun shi ya sauka ana batool da itama ta dago kai a fusace , fusge jikinta tayi daga nashi, cike da tsiwa da rashin kunya tace"dalla Mallam baka ganine, ko kai makaho ne ko, baka da ido ne ko idonka a tsakiyar ka yake da zakazo ka bangaje ni ka watsamin lemo mai sanyi a jikina, mutane kuna tafiya bakwa kallon gabanku sai kace wasu tumaki, " takwai karshe tare da banka mai wata uwar harara kamar idanunta zasu fad'o qasa,

Zuciya ne ya d'ebi Dr bash ya d'aga hannu zai wanka mata mari sai kuma ya dunqule hannunshi ya naushi iska ya fasa marinta, kallonta yayi cikin bacin rai tare da nunata da yatsa yace ke wacece da zaki bangaje sannan kizo kina gayamin maganar banza maimakon ki bani hakuri, kinsan ko ni wanene, muza hannunshi daya nunta dashi yayi yatsarshi ya bada wani sauti tas tas, yace kinci albarkacin Aslam da mummy da yau saina nuna miki ke qaramar Mara kunya ce tsaki yaja sanan ya ra'bata ya wuce abin shi,

Binshi tayi da harara kafin tana tsaki tare da cewa "aikin banza aikin wofi AI da ka mareni da wlh yau sai kasan ka taba. husaina fatima batool abdallah, "

(Tofah ku kuma kalan naku salon kenan hmmmm ku dai ku biyoni muje zuwa in garin ba nisa)

Daukar wayar amira dake qasa tayi ta duba ba abinda ya samu wayar, fitowa waje tayi dan kaima amira wayar,

Hango amiran tayi ta nufo ta tsayawa tayi har amiran ta isota ,miqa mata wayarta tayi, batace mata qala ba don ranta ya Riga ya gama baci da abinda mutumin da sukayi karo ya mata,

Amsar wayar amira tayi ganin miss call din mummy yasa tabi kiran da sauri, mummy ta daga tace"Amira ina kuka shiga ne inata kiran wayoyinku a kwashe , da'ker ma na samu naki oyaa maza ku kamo hanya ku dawo gida daddynku yace ku dawo haka dare yayi sha daya ta gota,".

Qarasawa sukayi ciki nan ta sanar zasu saqon mummy, aiko babbata lokaci suka miqe da niyyar komawa gida duk da ba'a tashi ba,

Ya kamal d'in da ya kawosu shiya maidasu , a hanyarsu ta komawa gidane batool ke basu labarin karon da tayi da Dr bash tanayi tana kwashe mai albarka tunda ita bawai sanin shi tayi ba, a haka suka iso gida,

A mooris event kuwa sai 1am aka tashi a daga dinner bagan nayi ciye ciye anyi shaye shayen drinks, anyi rabe raben sobeniyas kala kala mutane suka watse , ango ma ya dauki amaryarsa suka wuce gidansu dake London road, bakin dan rakiyan nan da akema amare wai su yan boko😕 sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya

Oum ummeetarh
07041130088

Share
and
Comment
Fi sabillah🙏🏻
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen nu}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.