Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 2 of 89
Page 3 & 4
Wata mataCikin yan kawo amarya ta karasa kusa da amaryan ta tsuguna a gabanta ta mi'ka hannuta ta daura akan cinyoyinta a hankali cikin kwantar da murya tace
"haba ASMA'U kukan ya isa haka mana tun jiya kike abu daya sai kace wacce aka kashewa iyaye ya kamata kibar kukan nan haka kodan lafiyarki"
Wata kyakkyawan tsohuwa ta karbe zancen da cewa " ke da allah ya dubi maraicinki ya baki miji na bugawa a jarida. mijin da duk wacce ta sameshi ta gama more miji. kinsan yan mata nawa ne ke neman wannan damar amma allah bai basu ba ke ya baki, ba kuka ya kamata kiyi ba godema Allah ya kamata kiyi daya mallaka miki Muhammad aslam a matsayin mijin auren ki.
Koda yake bazan ma ce kiyi shiru ba. yi tayi kinga idan ASLAM ya zo ya sameki da ido jajur dole ya lallabo ya dawo wurina tinda dama nice uwargida ran gida nice ta karfen "
ta qarashe maganar cikin d'an zaulaya.
Matar datayi magana dazu ne ta sake cewa tana kallon mutane dakin"jama a ya kamata muyi haramar tafiya magariba Na gabatowa motocin da suka kawomu suna waje suna jiran mu Allah ya basu zaman lapiya" da amin wasu suka amsa a fili wasu a zuciya yayinda wasu ke fadin ba amin ba a zuciyarsu.
Wucewa duka yan kawo amaryan sukayi aka barta daga ita sai kawayenta kuma yan uwanta amira , zahra , da batool sai kuma kanwarta Khadijah.
*********************
Misalin karfe shidda da Rabi Na yammacin ranar asabar zaune yake a bakin gadon dakin hotel da ya kama yau kimanin kwana uku kenan.
sanye yake da singlet fari qal da wando 3quater, matashin sauryine Wanda a kalla zaikai shekara 30 da haihuwa.
Kallo daya zaka masa kasan dolenema yan mata su haukace akan shi domin ya gama haduwa ta ko ina. fatar jikinshi kawai idan ka kalla kasan Hutu da jin dadin sun gama zama a jikin shi komai Na jikin shi me kyau ne tun daga sumar kanshi mai dauke da baqin saisayayyen gashi mai taushin gaske, fusskarshi mai dauke da kyakkyawan bakin saje a zagaye dashi. ga kuma wani Dan madaidaicin gemu daya tsayar irin na samari yan kwalisa masu ji da gayu, zuwa yanayin tsarin halilltar jikinsa irin Na cikakkun maza masu kyawun sura, Muhammad aslam kenan ,aslam mutum ne Mara, son hayaniya shiyasa da wuya ka ganshi yana magana indai ba mai mahimmanci bane, akoda yaushe fuskarshi a kame take,
bai cika kyalkyata dariyaba saidai yayi murmushi .shima ba kowani lokaciba hakan yasa yan matan dake Neman kawo mishi wargi suke matugar shakkarsa. Yanada riqo da addini baya wasa da ibadah yana matuqar girmama iyayen shi hakan kuma ya samo asaline ganin yadda iyayen nashi ke girmama nasu iyayen suma, Abu daya ke bani mamaki ga rayuwarshi shine rashin son raini kwata kwata aslam baya son raini duk abinda zaiyi a rainashi ko cikin
abokaine bayaso balle kuma a gurin qannen shi, hakan yasa qannwnshi ke kwasan gwale-gwale a hannunshi baya wasa dash ko kadan tsakanin shi dasu girmamawane
Shere
And
Comment
FisabillillahðŸ™ÂðŸÂ»ðŸ’–DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Na sadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.