Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 72 of 89
Page 117
"Dr bala!" Ta faɗa cikin tsananin mamakin ganin shi a gabanta, murmushi yayi sannan ya ƙaraso gabanta, tare da cewa "na'am zaynab" tace " da gaske Kaine a gabana, me kazoyi nan ya mutanen 9ja ina ƙawata beebaloo, nasan tunda na ganka tabbas zan samu koda number ta da na Daɗe ina nema ne" fuskar shi dauke da murmushi yace"duk wadannan tambayoyi haka a Jere zaynab wanne zan fara amsawa." Ita ma murmushin ta mayar mai tare da cewa "kowanne Dr, wlh nayi matukar farin cikin ganin ka, na daɗe ina fatan haɗuwa da mutumin da na sani ɗan Nigeria." Yace nima nayin farin cikin ganin ki "zaynab kodan na nemi tafiyar ki akan abin da na aikata miki nida ƙawarki beebaloo."
Kallon shi take yi cikin rashin fahimtar inda maganganun shi suka dosa, ganin yadda take binshi da kallon ban fahimce ka ba yasa yace "nasan baza ki fahimce ni ba zaynab saidai idan ni da kaina na warware mini komai, zanso ace kinada isasshen lokacin da zaki iya aramin koda minti talatin ne muyi magana." Tace "OK babu komai domin nima inason na nemi wani taimako a wajen ka."
Waiwaigawa yayi yana Neman musu inda ya dace su zauna, can ya hango kujeru guda biyu a bakin wani umbrella tree, cikin inuwa daga gefen su, nuna mata wajen yayi tare da cewa "idan babu damuwa zamu iya zama a cen."
Kallon gurin tayi inuwa ne kuma bugu da kari ba hanya bane babban da mutane zasu dinga wucewa barkatai, "is ok." Kawai tace tare da rufe motar ta, ta zagaya ta buÉ—e gefen da little boy dinta yake ta dauke shi.
Bayan sun zauna, zee ta ce "Dr na tambayeka ina ƙawata baka ce komai ba nayi missing dinta sosai kullum fata neke Ina addu'a Allah ya haɗa ni da wani dan Nigeria wanda na sani,na aikeshi gareta,ban samu ba sai yau da Allah ya haɗani da kai." Mai makon Dr bala yaba zee amsa sai ya shiga binta da wani irin kallon tausayi, a zuciyar shi ya ayyana lallai mutum abin tsoro yanzu dama haka zaynab ke kaunar beebaloo amma taci amanar ta, ganin yayi shiru yana binta da wani irin kallo yasa da dan karfi tace "Dr bala " firgigit yayi kafin ya sakar mata murmushi, yace "sorry zaynab kinga na tafi wani tunani daban ko,ina mamakin yadda mutanen duniya suka dauki cin amanar masoyin gaskiya Abu mai sauki" kallonta yayi ya fesar da zazzafan huci daga bakinshi sannan ya fuskance ta sosai yace"zaynab na haɗa ki da girman Allah, da darajar da Allah yayi wa ma'aiki ki yafe min." Cike da mamaki tace "Dr bala yafiyar me kake nema a gareni ni baka min laifin komai ba." Yace "na miki zaynab, nine fa nayi sanadin zubewar cikin jikinki, Wanda sanadiyar hakan na fuskanci tarin ɗalu bale yanzu haka maganar da nake miki, an sallameni daga aiki, sannan an kulle min asibiti na mai zaman kanshi, bugu da kari mahaifina jin labarin abin da nake aika tawa na zubar ma da mata ciki a asibiti na , ya kamu da ciwon zuciya take ya yanke jikin ya faɗi, tun daga ranar har yanzu baisan inda kanshi yake ba, da yaɗan bude ido sunana kawai yake kira yana cewa na cuce shi, shi ba irin wannan tarbiyar ya bani ba, yanzu haka likitoci sun hanani zuwa kusa dashi saboda samun lafiya shi, duk wannan abin ya faru ne ta dalilin alluran dana miki.
Nufasawa yayi kafin ya daura da, cewa, "na zubar ma da mata sama da É—ari ciki a duniya amma akan naki naga aya, ban sani ba amma ina kyautata zaton mijin kine yayi binkice ya gane nine na miki allura, shine ya kai sunana ministry of health, aka shiga binkice a kaina har allura ta tono galma, yanzu haka case lin bawai ya mutu bane kotu zamu shiga nan da wata É—aya, nan kuma da kika ganni mahaifina ne jikin yaki daÉ—i shine aka turo mu nan, shiyasa dana ganki naji daÉ—i domin na nemi yafiyar ki,ko Allah zai tausaya min ya rangwanta min."
Tun kan ya gama bata labarin idanunta ya cika da hawayen tausayin shi, girgiza kai tayi cikin tusayawa tace "ash'sha! Gaskiya Abu baiyi daɗi ba, na tausaya maka mà tuƙà , kuma ni dai baka min komai ba Dr saboda nina kawo kaina gare ka, Allah kayi wa laifi Dr shi ya kamata ka roƙa ya yafe maka, nima a lokacin jahilci ne yakai ni ga aikata hakan,amma yanzu alhmdllh Allah ya raba ni da wannan mugu ciwo na jahilci duk adalilin abinda ya faru, wannan lamarin daya faru ya zama silar shiryuwa ta,ta farkin Allah madaukakin sarki ya zama sillar tonuwar asirinka a duniya domin ka tuba ga ubangiji kafin ka riskeshi a matabbata, sannan Allah kadai yasan mutane nawa wannan lamarin yayi sanadin fitarsu daga halaka, kamar yadda ya zama silar fitar mu nida kai."
Tunda ta fara magana yake bin ta da kallo, lallai wannan zaynab din tasha bambam da wacce ya sani a watanni baya da suka shude, zaynab É—in da ke gaban shi wayayya ce mai hankali da nutsuwa mai hangen nesa, ba kamar zaynab din daya sani a baya ba shashasha mara wayau, wacce wata ballagazar mace kamar beebaloo ke Jan ragamar rayuwarta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.