Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 6 of 89
Page 9&10
Motar kamal ne ya shigo kwanar gidan a guje sai gudu yakeyi hakan yasa bai lura da asmah ba ya wuceta.......Amira ce ta fara hango motar don haka ta gaya wa sauran ga yaya kamal nan, hannu suka daga mai don ya ganesu ,
Gabansu yayi parking ya fito a rude yana tambayansu lpy meya samesu ina ita asmah? Duk hankalinshi a tashe yake.
Khadijah ce tayi karfin halin amsa masa da "yaya asmah tà na gaba..... yaya kamal muje gida sai amaka bayani wlh akwai matsala"
Shima bai qarayin magana ba ganinsu lafiyar su lay ba wani ciwo ko wani mugun abu a tare dasu, bude motar suka yi suka shiga baya dukkansu yayinda kamal ya zauna a mazaunin shi na direba,,, Rivas yayi suka kama hanyar gida,, hango asmah sukayi daidai ta isa bakin babban titi, parking kamal yayi a gabanta ya bude mata kusa dashi baice mata komai ba, itama ba musu ta shiga ganin kamal ne gashi kuma dare na qarayi.........
Zaune yake a room na hotel daya kama hankalin shi kwance kamar bai aikata komai ba...babu alamar damuwa ko wata nadama at are dashi, baidamu da neman shi da akeyi a gida ba. sarai yasan irin neman shi da amir dasu Abba sukeyi acikin garin minna... Amma ya bace musu bat ba amo ba labarinsa duk inda akasan zai iya zuwa ya anje ba a sameshi ba duk hotel din da akasan zai iya zuwa amir yaje ya bincika baije nan ba... Kasancewan amir yasan halinshi nasan Babar harka yasa iya manyan hotel din dake garin ya duba bai duba qananan ba. Hotel din daya kama ba Wanda zaiyi tunanin zai iya zuwa nan...amir kan ba qaramin kunya yasha ba Na irin gayyatar da yayi na abokansu tun da secondary, Dana aboard inda sukayi karatunsu da abokanan kasuwancinsu, amma aslam ya watsa masa kasa a ido, ko zuwa su gaisa baiyi ba kuma bai halarci wajen daurin auren ba balle ayi maganar zuwa dinner da amir din ya shirya , duk tarin yawan aboka nansu da sukazo haka amir yara jigila dasu shi kadai tun daga abincinsu abin shansu wurin kwana su dadai sauran su sai kamal dake dan taimaka masa haka dai had yasamu aka gama daurin auren ya sallame su , kiran ways kuwa amir ya kira aslam a waya yafi sau Dari bai dagawa massages kuwazed'a magana, amma aslam yayi mursisi dashi ya share shi,
System dinshi ya bude ya shiga gabatar da aikatotin shi Na yau da kullum da yake gudawarwa da suka shafi harkokin business dinsa saida ya gama tsab ya kulle system, wayarsa be ta fara ringing gyara zama yayi da kyau ya dauki wayar yana duba me kiran nashi...
(zee my 💖) ya gani yana yawo akan screen din wayar saida kiran ya kusa katsewa yayi picking tare da sallama... cikin kashe murya da tsabar iyaya zee ta amsa sallamar tare da cewa" da fatan masoyina ya wuni lafiya "
Wani kayataccen murmushi ne Wanda ba kasafai ake ganin irin shi a fuskarshi ba ya subucemai , amma kuma bai amsataba yadai amsa sallamarta a zuciyarshi....
Jin shirun yayi yawa yasa zee cire wayar a kunnenta tana dubawa ko yana kan layi , still dai call din nanan bai katseba, ganin haka yasa tasan yau yan miskilan na kusa, don haka tace "haba my husband to be yau kuma wani laifin na maka kake neman horani da shirunka" dan dakatawa tayi don tasan sarai bai cika son magana da yawaba,
Shiru kamar bazaiyi magana ba can kuma sai yace" lafiya qalau na wuni kuma ina fatan kema hakan take a gareki " murmushi tayi tace"nima qalau na wuni saidai kewarka data hanani sukuni " "dagaske kina kewata"ya tambayeta " sosaima, inkaji kewa daya kenan "
yace "ok to yayi kyau yasu mom"
"Tana lafiya tacema na gaisheka ". "OK" kawai yace mata, Dan shiru sukayi gaba dayansu kowa naji da kanshi har garama zee saboda son da take mishi wani lokacin takan ajiye Jan ajinta ta mishi magana , yanzuma ita ta katse shirun da cewa,"wani labari Mara dadi nake taji abakin mutane wai kayi aure dis week " amsata yayi da cewa "waya gaya miki " tace"friends dina da suke 9ja mana, kusan mutun biyar suka kirani awaya suka gayamin sannan kuma na gani a Media......amma saboda baka gayamin ba ban wani yarda ba, saboda nasan duk duniya inba niba baka kala wata mace ni kadai ce zabinka "lumshe kyawawan idanunshi yayi ya bude a hankali sannan ya ce mata" da gaske ne nayi aure" ya fada mata haka ne kawai don ya gwada ta, domin kuwa dagasken ne kamar yadda ta fada itace zabinshin duk duniya, itace first luv dinshi kuma har yanzu ita yakeso, bashi da wani burin daya wuce ya mallaketa domin ta hada duk abinda yake buqata awurin diya mace musamman matar da zai aura Wanda yake ganin asmah ko RabinRabin shi bada shi
Share and comment
Fisabillillah.
💖DAMA TA BIYU💖
BY
AYSHA NALADO
FREE BOOK
{Nasadaukara da wanna book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.