Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 31 of 89
Page 57 & 58
Da mahaukacin gudu ya bar gidan bayan zee ta shiga motar , saura kadan yabi takan me gadi,
Allah ne kadai ya kaisu gida lpy don Aslam gaba d'aya baya cikin haiyacin sa,
Yana yin parking ya fice a fusace ko qala baice ma zee ba,
Direct d'akin sa ya nufa ya kulle kofar ta ciki ya bar key a jiki,
Kan bed dinshi ya fad'a rigingine , ya shiga sauke wasu irin ajiyar zuciya, kai da kaji kasan bana lfy bane
Zee kam ganin ya fice baice mata kala ba , ko ajikin ta, hakan ko kadan bai dameta, ita yau jinta takeyi wasai , saima wani nishadi na musamma daya risketa , a yau Wanda ta dad'e batayi irin shi ba,
Cikin yan waqe waqenta tana rausaya ta shiga falon, ganin baya nan , ta ta'be, ta haura sama abinta, dakin ta ta shiga tayi wanka tayi sallan azahar da la'asar, sai lokacin ma ta tuna da yunwan da takeji dazu,
Kitchen taje ta dafa indomie ta zauna taci , har lokacin bataji motsin Aslam ba, nan tabà r plate d'in ta wuce dakinta ta kwanta ta kama sana'ar tata (charting),
Har dare ba motsin Aslam ba labari, fitowa zee tayi dan ta samawa cikinta abin tabawa, har ta wuce qofar d'akin Aslam , ko me ta tuna kuma ta dawo , tura qofar tayi ta jishi a kulle da key, knocking ta shiga yi shiru ba amsa, daqe kafada tayi alamar , kai ka sani dinnan ,
Kitchen taje still indomie ta qara dafawa, don shi kadai ta iya , zama tayi ta cuccusa abinta tasha lemo da ruwa , ta qara gaba abinta , kamar d'azu,
Da safe sai gurin qarfe goma zee ta farka tayi matuqar mamakin ganin gari ya waye,kenan yau Aslam bai tasheta sallan asuba bane kome,
A bangaren Aslam kam tun jiya da ya shiga d'aki ya kulle , ba abinda yakeyi sai aikin tunani, takura zuciyarshi yayida kwakwalwarshi , da tunani da damuwa,
ga baci ba sha , don da safe bai karya ya tafi office, kuma a office d'in coffee kawai ya sha, hakan yayi sanadin da zazzafan zazzabi ya rife shi ruf,
Kan gari ya waye tuni ya fice a hayyacinsa , sai wuraren goman safe ya samu dan sauqi ya watsa ruwan sanyi, yayi sallah ,first aid box din dake d'akin ya duba ya dauki , maganin zazzabi dana ulcer yasha bayan yad'an sha ruwan tea da cake,
Komawa yayi ya kwanta yaci gaba daga inda ya tsaya jiya, a tunani,
Zee bayan tayi wanka , ta fito falo ganin ba Aslam, yasa tayi tunanin ko ya wuce office ne abinshi, komai bata ji aranta ba , saima cewa da tayi a fili, "kai ka Sani,nidai tunda , baba tsoho ya hanaka, auren wannan yar iskar yarinyar, mai kama da 'kwara, ya gama min komai duniya,".
Ji tayi baza ta iya cin indomie da safe ba don haka , ta koma d'aki ta dauko makullin mota , saida ta isa parking lot d'in taga motar Aslam alamar, yana cikin gidan bai fita ba,
Ficewa tayi abinta daga gidan ko ajikinta, Aslam yana d'akin shi kwance yaji tashin motar zee alamar tabar gidan,
Tsaki ya ja a fili ya gyara kwanciya, yaci gaba da tunanin mafita da yadda zaiyi ya cire soyayyar Asmah a zuciyarshi , kozai samu salama daga irin azalzalan da take mishi ba dare ba rana,
Yau wasai kamal ya farka daga barci duk wani fargaban shi , ya kau ji yake kamar ma andaura auren shi da Asmah an gama, shiya kaisu school , kuma shiya daukosu,
Su zahra sai tsiya sukema Asmah wai dama soyayya takeyi da ya kamal shine ta 'boye musu,
Da misalin qarfe hudu na la'asar uncle nura mijin ya rabi'ah ya faka dalleliyar motar shi a parking lot d'in gidan surukan nasa, fitowa sukayi shida abokin tafiyar nashi, ba kowa bane kuwa face barrister Adam ,
Suna fitowa abban hanifa ya wurgawa brr Adam harara yace" hankalinka ya kwanta yanzu, kasaka ni kawo ziyara gidan surukai ba shi" murmushi brr Adam yayi " sorry bestie na tallafi ruhin abokin ka wlh in bankai kaina ga iyayenta ba yau bazan iya rintsawa ba, ka wala ni da yawa , kaji tausayin mijin maryama, angon fatima zahra to be, insha Allah"
Bello ne ya musu iso zuwa part din daddy , da fara'a daddy ya tarbesu, gaida shi sukayi cikin mutuntawa kamar yadda suka saba,
Bayan sundan taba hira kad'an , abban hanifa ya gabatar da buqatar su , na neman izinin shi game da neman auren zahra,
Daddy yaji dadin wannan lamari, saboda ya dad'e da sanin brr Adam a gurin abban hanifa , yasan mutumin kirkine kamar yadda abban hanifa ya kasance mutumin kirki, don hausawa kance , in kana son sanin halin mutum ka dubi abokin sa,
Take ya tabbatar musu ba'ayi mata miji ba , kuma ya basu izini su naimi soyayyar ta da yardarta.
Nan suka shiga zuba godiya kamar bakinsu zai tsinke, sai da daddy yace ya isa , sallama sukayi da daddy suka fito, da niyar zasu dawo gobe,
Suna fitowa brr ya dubi abban hanifa , yace "yanzu sai mu shiga ko " abban hanifa yace "ina?" Yace
"Ciki mana, muje na ganta , na gaya mata kasan ance da zafi zafi akan daki karfe" harara abban hanifa ya watsa mai yace" to ai sai ka shiga ka sameni a gida " ya fada yana bud'e motar shi ya shiga, shima bar Adam din shiga yayi , suka fice , a hanya yake cewa" to wlh kuwa yau a minna zan kwana, ni da komawa bidda har sai na samu yardar ta da soyyayar ta," abban hanifa tace" in kuma baka samu bafa " baisan sanda yakai hannu ya bame mai baki ba yace" annabin rahama yace fadi alkhairi ko kayi shiru, insha Allah zan samu amincewarta , bakin ka ya sari dutsen faida" abban hanifa yace" to nidai ba ruwana, ka tattara ka koma bidda gobe ka dawo , don kar ka had'a ni da maryama taga kamar da ni aka had'a baki aka mata kishiya , duk da dai nasan komai zan fad'a ba yarda zatayi dani ba , tunda kanwar matata ce, qilama tace ni na had'a ku" dariya brr Adam yayi yace " ohoo dai kai ka sani, ai kunfi kusa, inagama kai zan dauka ma kakai mata kayan fad'an kishiya" abban hanifa yace "rufamin asiri ni bana zuwa irin wad'anan abubuwan , bazan manta ba wani abokina , da ya raka abokin shi kai kayan fad'an kishi ,waishi irin zai mata wa'azi , da makaranta suka tashi ta shaqo shi, saida yayi kwana uku a asibiti ana qara mai ruwa" brr Adam kam mai zaiyi ba dariya ba, cikin dariya yace"kaidai wlh matsora cine abokina",abban hanifa yace"eh naji komai zakace kace, ai mata akan kiyashi zasu iyayin komai , saidai kuma wasu nasu kishin da sauqi akan na wasu," da haka suka qaraso , gida, nan suka qarqare wuni sai dare abban hanifa ya kaishi masauki dan firr qin kwana gidan yayi,
Aslam yauma haka ya kwana cikin mugun ciwo Wanda har yaso yafi na jiya,gaba daya ya fad'a cikin kanqanin lokaci, ya qara haske yayi fiyat dashi, yau abincin ma qin zama yayi a cikin sa , da yasha shayi amai yata kwara wa harda jini jini a cikin aman, gaba d'aya ya gama galabaita, gashi ya saka wayar shi a airplane mood, ba Wanda zai iya kiransa balle asan halin da yake ciki,
Kalaman alhaji baba duk bayan minute amsa kuwwa sukeyi a kunnen shi(ni Muhammad , a mastayina na Wanda aka wakilta ya aurad da Asma'u , na baka aurenta kuma na sanya lokaci nan da wata uku masu zuwa) yanzu shike nan ya rasa husnah kenan , yanzu haka zai zuba ido yana ji yana gani husnah ta auri wani d'a namiji ba shi ba, kai ina hakan bazai taba yuwuwa ba ya zama dole yayi wani Abu akan lamarin nan,
Tunawa yayi da waye alhaji baba , tsayyaye ne kaifi daya, baya magana biyu, take sabon zazzabi ya lullubeshi, wayar shi ya zaro ya kunna hotunan Asmah na rannan yana kallo , da haka ya d'an samu relief,
Zee bata dawo gidan ba sai bayan isha'i don yau garin yawonta ta hadu da wata qawa, wai ita bebalo,bazawara ce, auren ta biyar taqi zama, sai shegen yawo kwararo kwararo lungu lungu, bata nan bata cen, haka suka kulla kà wance, sukayi musayar numbar waya
( dama ance sai hali yazo d'aya ake abota)
Me gadi ne bayan sun gaisa yake tambayar ta Aslam , ganin tun shekaran jiya da ya shigo bai qara ganin fitar shi ba, sai lokacin ta tuna rabonta dashi tun shekaran jiya, tace"kana nufin tunda na fita yana cikin gidan nan bai fita ba?" megadi yace "eh hajiya ,nima naga shirun yayi yawa shiyasa na tambaya ko lfy"
"Ba komai" ta amsa mai , sannan ta nufi cikin gidan zuciyata babu dad'i, duk da tasan akan wannan shegiyar yarinyar ya saka kanshi cikin wannan halin,
D'akin shi ta fara biyawa tayi knocking yafi sau goma , yana jinta amma ya shareta , dan itama yanzu haushinta yakeji gaba d'aya, kowa na duniya haushin su yake ji Asmah kadai yake ji da gani,
Ganin yaqi tankata yasa ta wuce abinta , duk da zuwa yanzu lamarin ya fara bata tsoro,
Washe gari ma haka aka maimaita yaqi bude qofa , ita kuma ganin haka ta shirya ta fita yawanta da sabuwar qawarta beebalo,
Misalin qarfe goma na safe Dr bash yayi parking motar shi a harabar gidan su Aslam , kwana uku kenan
yana neman Aslam ba amo ba lbr har office dinsa yaje amma ance rabonshi da office yau kwana uku daga can ne ya nufa gida dan ya tambaya ko lafiya,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.