Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 53 of 89

Page 95

~BABYN ADAM~

Har Barr ya gama kwanaki bakwai daya kamata miji mai mata yayi a dakin amaryarsa budurwa,babu abinda ya shiga tsakanin su, na auratayya, saidai a yan kwanakin nan ba karamin sabo sukayi da juna ba, ta riga ta gama sakin jiki da shi duk dari darin da takeyi dashi da yanzu ta dena,yakan dan taba wasa da ita amma iyakanshi kenan bai taba nuna yana son wuce hakan ba, wannan yasa hankalinta ya kwanta, ta saki jiki da shi tunda abinda take ma tsoron, taga baida alamar yi, da amala dai ita nata miji ba dan air bane.😛

Har yayi kwana bakwai a dakinta bata fara girki da kanta ba daga gidan su ake aikowa, dan maryama cewa tayi baza tayi ba,

Duk motsinsu akan idon maryama, ta sanya musu ido sosai sometimes har labe take musu, ta fahimmci babu abinda ya shiga tsakanin su har yanzu, hakan kuwa ba karamin daÉ—i ya mata ba.

Tsakanin ta da Barr kuwa babu zaman lafiya kwata kwata, kullum cikin tayar mai da hankali take, gaba daya lamarin ta ya isheshi, kawai daurewa yakeyi yana kai zuciya nesa.

Yau ta kama zai koma ɗakin uwar gida ya gama kwanakin shi bakwai a dakin amarya, zahra harda kukanta shaɓe shaɓe haka yasa ta a jikin shi yana lallashi kamar wata jinjira, da'ker ya samu tayi shiru, tashi yayi ya shiga toilet ya haɗa mata ruwan wanke, yace tayi wanka ta same shi a dakin shi zai hada ta da maryama ya musu nasiha daga nan kuma yaji ra'ayin su,yanayin kwanakin da zasu raba.

Bayan fitar sa ta tashi ta shiga toilet d'in ta sheka wankanta da sabulanta masu kamshi na gyaran jiki, ta wanke dogon gashinta ta fito, zama tayi kan kujeran gaban mirror tayi shafe shafen ta, na mayukanta da turarukanta haɗaɗɗun gaske, tsantsararren makeup ta ɓata lokaci tayi a fuskarta, lokaci ɗaya ta dauki wani irin mugun kyau kamar wata balarabiya, dama ko batayi kwalliya ba mai kyauce balle kuma, lace ta ciro tsantsararre maroon color sai ratsin peach, ɗinki riga da skirt, dinki ya dan kamata haka yasa ya fito mata da shape sosai, dass ta fito kamar wata yar tsana, dauri ta kashe mai kyau na yayi, mayafinta karamin ta dauka peach ta ratayeshi a kafaɗa, turare ta dauka ta kara fesawa a kayanta, ta zura takalmanta mai tsini mahadin mayafinta ta dauki handset dinta ta nufi sashen Barr.

Bayan shigan shi daki wayar shi ya dauka ya danna ma Maryama kira, ringing wayar keyi tana kallo taki dagawa, har ya katse kara kira yayi saida ya kusa yankewa ta daga, ta kara a kunne batace ƙala ba, jin haka yasan baza tayi magana bane,don wani bin ji take da izza kamar wata jinin sarauta, da kausasheshen murya yace"na baki nan da 10 ki kimtsa ki sameni a part ɗina" kit ya kashe wayar sa, yanayin yadda taji muryarsa tasan ba wasa a maganar shi yasa ta tashi ba wani kimtswan da tayi kayan bacci ne a jikinta riga da wando da hulla haka ta taho abinta, Maryama ba kazama bace, amma tunda akayi mata kishiya ta dauki wahalallan kishi ta daura ma kanta shikenan komai nata yaja baya, har a gurin miji kimarta ya ragu, saboda wannan haukan da tajeyi da sunan kishi, saiyaji duk ta fice mai a rai, duk ta sukurkuta kanta a banza a wofi, tunda gashi dai duk tsiyar ta bai hana shi aure ba kuma bai hanashi kawo amaryar cikin gidanta ba,

( pls mata a kiyaye asan irin kishin da za'a dingayi ba kishin da zaki zubar ma kanki mutunci a gurin miji ba, duk sonki da miji idan ya tashi aure, kiyi hakuri ki danne kishinki, ba'ace karkiyi kishin mijinki ba amma kisan irin Wanda zakiyi, idan kika kama girmanki sai kiga duk wani abinda zai gudanar a lamarin aurenshi saida yardan ki, kece zaki zama bai bashi shawara komai zaiyi saiya gaya miki saiya nimi shawaran ki, tunda yaga kin bashi goyan baya, anan saiki yagi abinda kika yaga,amma in kika yi hauka zaki tashi a tutar babu ne, wasu ne can zasuci moriyar lamarin, idan kikayi kishin hauka kika tayar mai da hankali, kimar ki zaki zubar a idanun shi da idanun dangin shi,idan akwai wacce Baku shiri cikin yan uwanshi, ta samu hanyar da zata kuntata miki,saidai kiga ana abubuwa baki da labari, amma kin kama kanki, sai ki kange komai, komai sai anbi ta hannun ki, ya sakar miki ragamar komai, dan Allah a kiyaye kuma duk tsiyar da zakiyi bazai hanashi auren da yayi niyya ba, kijama kanki raini a gurin kishiya may be ma kin girmeta kin fita komai, Allah yasa mu dace).

Samun shi tayi zaune a falo yana amsa call a waya, guri ta samu a kujeran dake facing nashi ta zauna tana cika tana batsewa, ci gaba yayi da wayar shi ko kallonta shima baiyi ba, zaman ta kamar da minti biyar zahra tayi sallama cikin zazzakar muryarta mai dadin amo, daidai lokacin kuma Barr ya gama wayar da yakeyi, kamshinta ne fara musu sallama kafin a natse ta ɗago labulen falon ta shigo, da idanu suka bita yuuuu, kowa da irin kallon da yake mata, maryama ganin zahar da irin wankan data dauka ga wani zazzafan kamshi dake tashi a jikinta, saida gabanta ya yanke ya fadi rasss, take ta raina kanta a wurin ji tayi duk ta muzanta, kishi da ƙyashi da baƙin ciki suka mata kawanya a lokaci daya, take ta shiga aunawa zahra wani irin mugun kallo mai cike da tsantsar tsana.

Shiko Barr wani irin kallon so da tsananin ƙauna yake binta dashi, ji yake kamar ya tashi ya taro ta ya saka a kirjinshi, ko zaiji saukin zillon da zuciyar shi take mai akanta, yana tsananin son uwar gidan shi sosai amma sonda yakema zahra special ne.

Murmushi ya shiga jifanta dashi, hakan yasa itama ta shiga mayar mai da martani, matsawa yayi daga tsakiyar kujeran da yake zaune 2 sitter ya koma gefe, ganin haka zahra direct kusa dashi ta zauna a daya gefe.

Har ta zauna Maryama nabinta da wannan mugun kallon, cikin sakin fuska ta kalleta tace"yaya Maryama ina kwana" wani mugun tsaki taja kamar bakin ta zai tsinke, a madadin ta amsa gaisuwar ta sai cewa tayi"wlh kaji kunya Adam yanzu ɗan wannan abun ka iya cire kudinka ka bada sadaki da sunan kana so, kazo ka ajiye kana kwanciya da ita, yarinyace fa ƙarama Wanda na tabbata da kayi auren wuri da ka haifeta, wannan abin kunyar dame yayi kama, na tabbata wannan yarinyar idan ta girmi hanan(yar su ta fari)da nisa ta bata shekara biyar, yanzu kai baka jin kunyar ka tube zindir a gaban yar cikin ka, kalli kanka ka fa har furfura kake dashi" tsaki taja kafin taci gaba da cewa "suma iyayenta ne basu da hankali wannan ai child abuse ne".

Wani gigitaccen tsawa Barr ya daka mata wanda saida hantar cikinta ya kada, amma ta dake tana huhhura hanci, zahra kam zaro ido tayi waje maganar Maryama na karshe yayi mugun dakar mata zuciya, iyayenta ne basu da hankalin, tabdijam aikam baza ta kyaleta taci bulus ba, itama fa ta iya masifar nan da rashin kunya kawai dai batayi ne saboda Allah yayi ta da sanyin hali, yoooo ita da takema yar uwar batool danja har a gwada mata masifa da fitsara da rashin kunya, buɗe baki tayi da niyar yaba mata maganar da har ta mutu baza ta manta dashi ba, fahimtar hakan yasa Barr ya damki hannunta dake kusa dashi da karfi dagowa tayi ta kalle shi ya girgiza mata kai alamar kar tace komai, zahra a kwai biyayya kamar dai Asmah😅.

Sauke kanta kasa tayi sai hawaye sharrr, kamar an bude famfo, a zuciyar ta tace maryama kinyi da meyi zan nuna miki aiki karamar yarinya a aikace, amma kafin nan saina mallakama mijina kai na mun dawo g-g dake, sai kinyi nadamar zagin iyayena da kikayi.

Barr kam fada yahau Maryama dashi karshe ya koma nasiha yana dasa aya tace "oho dai andaiji kunya wlh girma ya fadi" bai tanka ta ba yace "yanzu ki fadi kwanakin da kikeson ku dingayi ma'ana ku raba girki," budar bakinta sai cewa tayi "Allah ya kiyaye na raba girki da yar cikina" cikin fushi yace "haka kika Ce ko to shi kenan ni na raba kwana 1-1 zaku dingayi daga yau, kuma kin amshi girki yau, da rana zaki fara zuwa breakfast din gobe, abinci kuma breakfast da dinner tare zamu dinga ci" yana kaiwa nan ya tashi ya bar masu falon , itama Maryama tsaki taja ta mike ta watsa ma zahra harara, tace "wlh ki sake mai jiki ya kwakuleki a banza dan ba zama kika zoyi gidan nan ba, na miki alkawarin saina fitar dake dan bazan yi kishi da yar cikina ba, in zaki rike budurcinki ki rike kyasamu ki kaima asalin mijinki" tana kaiwa nan ta bar falon, a fusace kamar kububuwa.

Lokaci daya taji hawayen dake fita a idonta ya kafe,murmushin takaici ta sake,a zuciyarta tace wato ma saka mani idanu takeyi tana kallon ko wani motsi dake gudana a tsakanina da mijina ko,inba haka ba ya akayi tasan babu abinda ya shiga tsakanin mu, hmmmm to zan shayar dake giyar mamaki Maryama.

Tashi itama tayi ta bar part din ta koma nata, abin daya faru ya tsaya mata a rai sosai, wayar ta ta ciro tana tunanin shawaran wa zata nema, Ummi , zuciyarta ya bata amsa lallai ummi ce tafi cancanta, saboda yadda suke da ita kamar kawaye, zata bata shawara mai kyau a bayyane baza ta rufe mata komai ba, take ta lalubo numbar ummi ta danna mata kira,ummi ta daga bayan sun gaisa, nan ta sanar mata abinda ya faru, da irin maganganun da maryama ta yaɓa mata, da zagin iyayenta da tayi.

Nutsuwa ummi tayi ta bata shawarwari masu kyau wadanda zasu billar da ita, aikam shiru tayi tana recoding d'in abinda ummi ke gaya mata, sun dade kafin sukayi sallama, haka ta wuni a daki ita kadai, ba Wanda yazo gurinta itama bata fita wajen kowa ba, maryama bata kira cin avinciba itama bata nema ba, anam part dinta ta samar ma kanta abinda zataci.

tun da safen nan kuwa bata sake saka Barr a idanunta ba sai bayan isha'i ya shigo ya same ta kwance a kan gadonta, tana ganin shi ta tashi zaune ta shiga mai sannu da zuwa, zama yayi a baking bed d'in, yana kallon ta cikin muryar kwantar da hankali ya shiga lallashinta yana bata hakuri akan abinda ya faru dazu,nuna mai tayi ba komai, komai ya wuce, dadi yaji ya kara gode ma Allah daya mallakamai zahra a matsayin matar sa, yarinyar tanada hankali da hangen nesa sosai, sallama ya mata zai wuce wurin Maryama, har bakin kofa ta rako shi tana sharar kwallah kishi fall zuciyarta, shima ji yakeyi kamar kar ya tafi ya barta, ganin hawaye yaki dauke mata yasa ya jawota jikinshi ya dago fuskarta ya shiga lashe mata hawayen dake fitowa a idanunta, yana gamawa kuma ya hade bakinsu guri daya ya shiga kissing dinta, 5 minutes suka dauka a haka kafin ya saketa yana maida numfashi yace"kiyi hakuri babyn Adam kidena min asarar hawayenki, insha Allah gobe war haka muna tare shiyasa na zaɓi 1-1 days saboda ni kaina bazan iya wuce kwana daya bakya kusa dani ba" murmushi tayi jin abinda yace, tace"gud 9t my hrt bit, ka kulamin da yayata da kyau" ta juya da sauri sauri gudu gudu ta haura dakin fadawa gado tayi tana risgan kuka kishi da kewar mijinta na addabar zuciyarta, ta kudiri aniyar mallaka mishi kanta a gobe idan ya dawo dakin ta wanna kuwa daya daga cikin shawaran ummi ne.

Saida ya kulema ganin ta sannan ya fice daga part d'in da sauri, acan kuma yana zuwa ya tarad da bala'in Maryama, ganin zata hana shi bacci yasa tsakar dare ya korota waje ya bame kofar shi, haka suka cinye daren ba wani armashi ko baccin karki ba Wanda yayi cikin su ukun kowa da abinda ke damunsa.

kuyi manage yau bani da isasshen caji,🙏

Oum ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fisabillilah🙏.
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

DAMA TA BIYU💖 ƘIRƘIRARREN LABARINE MALLAKI NANE BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYAMIN LABARI TA KO WACCE SIGA BADA IZININA BA❌❌❌❌❌

(In 👂👂👂 yaji gangar jiki ya tsira👌 a kiyaye pls)

{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.