Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 35 of 89
CI gaba sukayi da hira, can Dr bash yace "subhanallahi wlh na manta akwai wani allura guda daya da za'amai cikin dare gashi bamu dashi anan sai anje pharmacy a waje an siyo" kamal yace"ayya to kawo na siyo mana"
Rubuta mishi sunan alluran yayi ya miqa mishi, amsa yayi ya miƙe har yakai bakin ƙofa ya juyo ya kalli Asmah, yace asmy ba rakiya, cikin dan jin kunya ta watsa mishi hararan wasa , tana murmushi, hannu ya haɗe mata alamar roƙo yayi fuskar tausayi, saida ta ja mai aji sannan ta miqe tabi bayanshi,
Dakin ya rage daga batool da zahra sai Dr bash, sai aslam dake bacci,
Dr bash ya dubi zahra yace "kanwata zahra ya makaranta ya karatu," cikin murmushi ta amsa da "makaranta alhamdulillahi , karatu kuma akwai wuya ya bashir" bash yayi murmushi yace "karatun ma balle irin namu sai mai ƙoƙari, kuma ke da gani zakiyi ƙoƙari, ganin yadda kike da nutsuwa da hankali , ba kamar wasu yan matan ba da zaki gansu kullun cikin guje guje kamar yan nursery,"
Dagowa batool tayi da sauri ta kalle shi jin abin da take cewa ,ko ba'a fad'a ba tasan da ita yakeyi,
Zahra ko cikin jin dadin yabon da aka mata, tace " nifa ya bashir bani da wani qoqari saidai taimakon Allah kawai, dama batool kace itace mai kokari don duk cikin mu ta fimu ƙoƙari," cikin son ya tsokani batool yace"kai zahra wannan shirmammiyar yarinyar da ganin ta baza tayi wani qoqari ba, irinsu ne fa masu yin espo a class, da ganin idonta na rashin kunya ta kware a iya espo"
Kan uba aiko dai ya taro masifa don dama tun dazu daurewa kawai takeyi amma a cike take fam dashi kamar zata fashi,
Aiko nan ta shiga zazzaga mai ruwan rashin kunya tanayi tana murguda baki, ta inda take shiga ba tanan take fitaba,
Aiko dai Dr bash mutuwar zaune yayi yana kallonta , É—an bakinta da take masifa tana mugudawa yake bi da kallo , gaba daya masifarta burge shi yakeyi, abin na mishi É—aÉ—in kallo yana sakashi nishadi,
Saida tayi mai isar ta tayi shiru, zahra kam tagumi tayi da hannu bibbiyu tana kallon ikon Allah , don tun É—azu take ce mata ya isa amma taqi kulata , ganin haka yasa ta yi tagumi tana kallonta,
Su kamal ne suka shigo dakin , ganin haka yasa kamal tambayar ba'asi ,nan ta shiga labarta mishi abinda bash yace tana yi, kamal kunshe dariyar shi yayi yace,
"Kai ammafa Dr ka samu kanwata da yawa ita kake kira da me espo a class, to kiyi hakuri wasa yake miki ai,da'ker ya lallabata ta hakura ,"
Daga nan sukayi sallama da Dr bash, a waje suka dauki Amira suka koma gida,
Kwanan Aslam uku jiki yayi sauqi sosai , nan yace shi ya gaji da zaman asibiti a sallame shi , ƙin sallaman shi bashir yayi yace sai yayi sati, tada balli yayi ba shiri Dr bash ya rubuta mai sallama,............
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fi sabilillahðŸ™Â
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan littafin ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan mahaifan mu}
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.