Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 4 of 89

Page 6

A toilet din dake dakin gaba d'ayansu sukayi alwala banda batool dake kwance kan gado tana fashin sallah, hijjab da pray mat suka dauka a cikin sif kasance war an mata jerenta komai akwai a gidan hatta kayan sawanta suna cikin sit, zahra CE ta shiga wani app a wayarta ya nuna musu alqibla suka fara sallah,
Batool dake kwance taji kamar ana kwala sallama a kofar parlour saurarawa tayi still taji an sake yin sallamar, tashi tayi ta sauko parlour tana amsa sallamar,
Wani mutum ta gani me kimanin shekara arba'in , gaisawa sukayi cikin mutunta juna. Ya Dora da cewa"hajiya dama wani ne yazo yana waje wai mai gidan ne ya bashi saqo ya kawowa madam"
Sai lokacin batool ta fahimci waye wannan mutumin wato mai gadin ne,

"Kace yace yaya aslam ne ya aiko shi gurin asmah?"batool ta tambayeshi, "eh haka yace hajiya, yacema daga can babban gida yake"
"OK muje na ganshi" batool ta fada tana
nufar hanyar waje, bin bayanta mai gadi yayi suka fito compound din gidan,
Karasowa bello yayi ganin mai gadi da batool sun fito, batool tace"mallam bello dama kaine"
"Eh batool nine ya kike ya gujiba gujiban biki"
Batool tace "lpy qlau ya naka gujiba gujiban don nasan kaima kasha gujiba gujiban"Dan dariya yayi tare da cewa"wlh kuwa balool kaman kin Sani, Allah dai ya basu zaman lpy da zuri'a dayyibah "
"Amin thumma amin "batool ta amsa,
saka hannu bello yayi a aljihu ya d'auko farin takardar da aslam ya bashi ya miqawa batool"gashi kiba madam inji yallabai yace a kawo mata"amsa batool tayi tana jujjuya paper sannan tace"to shikenan mallam bello insha Allah yanzu inna shiga zan bata"
"Yawwa batool Na gode sai anjima"bello ya fad'a tare da juyawa ya wuce ,itama batool juyawa tayi ta shige parlon a ranta tana mamakin meye a cikin takar Dan nan da yaya aslam ya aiko dashi da bazai iya kira a waya ba

Koda ta dawo dakin kusan dukansu sun idar da sallah saidai suna zazzaune a gurin suna azkar d'insu, komawa tayi bakin gadon ta zauna tana jiran su idar ta miqa ma asmah saqon, zamanta kamar da minti biyar zahra ta miqe tana linke hijab,kallon batool tayi tace"wlh batool kedai anyi mara hankali"tana balla mata harara , itama batool hararan ta balla mata tare da cewa mai Na miki kuma uwar kankanba , tsaki zahra taja tare da cewa "kinzo kinhau gadon amarya ko kunya babu bayan kinsan sarai mummy ta hanamu hawa gadon mutane, kumama don tsabar rashin kunya gadon yaya aslam din kika hau, to wlh saina gayawa mummy" ,

Harara batool ta balla mata tace" to gulmammiya ba mummy zaki gayawa ba inkinga dama kije ki gayawa yaya aslam din da kanshi ya kasheni ko kuma kije ki gayawa alhaji baba qarewa"
Amira ce da itama idarwanta kenan tana like hijjab tayi gyaran murya uhummmmm duk juyowa sukayi suna kallon ta, itama su take kallo tace"
kudai kunji kunya wlh ko ina akaje sai kun sai kun raba hali sai kace wasu qananan yara"
Khadija ce ta kyalkyale da dariya tana cewa "
wlh twins din mummy kuna ban dariya"

kukan da sukaji asmah ta fashe da shine ya maida hankalinsu kanta, zaune take a inda ta yi sallah ta daga hannu sama tana kai kukanta gurin mahaliccinta, sosai take addu'a akan aurenta da Neman mafita mafi alkhairi, dukkan su da amin suke amsawa har ta gama ta shafa suma suka shafa tare da ita,
batool ce ta matsa kusa da ita tare da miqa mata paper da bello ya kawo tana fadin "amaryan yayanmu wai gashi inji angon naki ya aiko mallam bello direba dazu kina sallah wai ya kawowa shibarsa" ta fada cikin sigar zaulaya,
Dago kanta tayi ta Dan qurawa pepan dake hannnun batool ido kafin ta mika hannu ta karba, bud'e pepan tayi ta qurawa rubutun da baifi layi uku ba ido,
Karantawa takeyi tana qara maimaita karanta abinda ke cikin pepan a zuciyarta. ganin dai tabbas abinda ta gani arubuce a cikin paper tabbas haka yake ba gizo idanunta ke mata ba,ya sata sakin wani qayataccen murmushin Wanda yasa yan biyu mummy da amira da khadija kallon kallo a tsakanin su,
Zahra ce datafi kusa da ita ta miqa hannu ta karbi papern a hannunta warwarewa tayi ta fara karan tawa da qarfi yanda sauran zasu jita kamar haka

Share
And
Comment
Fisabilillah🙏🏻
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Na sadaukar da wannnan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya,
Allah ka jiqan iyayen mu}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.