Complete Hausa Novels

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Da_Izzata_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 3 of 89

Page 5

Wayarsace dake gefensa ta fara ringing ko bai kalla ba yasan bazai wuce amir ba, miqa hannu yayi ya dauki wayar ya duba, kamar yadda yayi tsammani kuwa amir d'inne,

Kamar ko wani lokaci mayar da wayar yayi ya ajiye baiyi receiving ba, jota da biron da ke ajiye gefensa ya dauka,
sai da ya tsaya yayi Dan Jim kafin daga bisani yayi rubutun da bai wuce layi uku ba ya falle page din ya linke ya ajiye ,
Kallon agogo dake manne a dakin hotel din yayi ganin 6:40pm yasa ya mike ya shiga toilet domin ya dauro alwala,
Yana fitowa jallabiya ya dauka ya daura akan 'kananan kayan dake jikinsa. Paper da yayi rubutu da key ya dauka ya saka a aljihu ya fito d'akin d'auke da wayoyin shi a hannu ,
Kulle kofar dakin yayi ya fito a cikin hotel din ya nufi masallacin kusa da hotel din,
Daf da zai shiga masallacin wayarshi ta fara qarar alamar saqo ya shigo, Dan dakatawa yayi ya duba message din ganin saqon da aka turo ya saka shi dialing number da aka turo message din, picking akayi cike da girmamawa Wanda ya kira din ke fading
"yallabai gani nan Na karaso hotel din "
A daqile yace
"kasame ni a masallaci"
Ya kashe wayar ya shige cikin masallacin, saida aka idar da sallan magriba suka samu ganin juna, bayan sun gaisa hannu yasa a aljihu ya Ciro paper dayayi Dan note dazu ya miqa mishi tare da fadin. "ka kai ma waccen yarinyar"
Amsa yayi da hannu biyu amma ga dukkan alamu bai game wacce yarinya yake nufi ba , Dan sada kansa qasa kadan yayi alamar girmamawa sannan yace "yallabai wacce yarinya kake nufi"
Kallon shi aslam yayi ya dauke kai yace" yarinyar da suka kai gida Na dazu"
Murmushi ne ya kufce a fuskar bello yana Dan Sosa qeya yace
"yallabai amarya kake nufi"
Wani mugun kallo ya watsawa bello dayasa lokaci daya murmushin fuskarshi gimtsewa, Juyawa yayi zai wuce aiken da aka mai yana cewa "a huta lpy yallabai"
Saida yayi taku kamar biyar aslam ya kira sunan sa "bello" juyowa bello yayi ya dawo yadan risina yace "yallabai gani". Saida ya bushi iska yace "kada kowa yasan ina nan ciki harda daddy da amir, babu wani mahalukin dayasan inda nake sai kai kad'ai don haka take care" yana gama fadin haka ya duya ya shige cikin hotel din abinshi..

*********************
Bayan yan kai amarya sun wuce amira da zahra ne suka sakata a tsakiya akan tayi shiru ta daina kuka haka Allah ya qaddaro mata amma ina ko sauraronsu batayi sai kukanta takeyi bil hakki .
Khadijah CE itama ta matso gabanta ta tsuguna miqa hannu ta kama hannayenta ta riqe cikin muryan lallashi tace " yaya asmah ya kamata kibar kukan nan haka kada wani ciwo ya kamaki, idan fa wani Abu ya sameki Wanda kike kukan nan dalilin shi fa bashi da asara, muda muke sonki mukeda asara,mune zamu shiga wani hali idan wani Abu ya sameki pls yaya asmah ya isa haka"ta karashe maganar tana langwabar da kai idanunta cike da hawaye,

Dago kai tayi ta kallesu baba daya sai taga sun bata tausayi, share hawayen fuskarta tayi tare da qaqalo wani bushasshen murmushin da iyakacinsa fatar baki tayi musu,"Na gode yan uwana yanzu Ku tashi muyi sallah magriba yayi" ta fada tana zare hannunta cikin Na Khadijah, suma murmushin sukayi mata Khadijah Na fadin "yaya kokefa, don Allah karki qarayin kuka kinji " gyada mata kai kawai tayi,

Share
And
Comment
Fisabilillah🙏
Date: Sep 27, 2022

💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Na sadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya,
Allah kajiqan iyayen mu}

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.